Mowar miji(Borar Danginsa)

7.7K 224 7
                                    


👑 *Mowar miji*👑
          { _Borar Danginsa_}

By
Zainab shukrah😍

Follow me on wattpad
Zainab Yakasai
14

Washe gari 8:00am a gidan Maamah tayi masa, yana zaune parlour yana jiran fitowarta, Amaal kam ta Dade a school, sai bayan 30mnts ta fito tana kallonsa ta zauna tace "Nayi tunanin ba zaka zoba ai" yayi saurin zamewa kasa yana shafa kansa yace "Gud morning Ma" tace "Morning" kawai , yace "Maamah ban isa ince ba zanzo ba ai, wani abu ya rikeni amma kiyi hak'uri" tace "Ah Ameer ai ba sai ka bani hak'uri ba, ai nasan bayin kanka bane an riga an asirceka ne yanzu kafi karfi na ai" kallonta kawai yake da mamaki, Maamah ta canja gaba daya, da duk duniya shi tafi so amma akan auren nan duk ta tsaneshi, da kyar ya bud'e baki yace "Wallahi Allah Maamah Simbiat bata min asiri ba, bata San yadda ake asiri ba wallahi, Dan Allah ki bawa Simbiat dama wallahi zakiji dadin zama da ita" shekeke Maamah take kallonsa tace "Kai banason gulma wani wai zan sota, bari kaji Ameer abinda fa zuciya bata so bataso, kuma bazata taba soba" ya matso a hankali ya dora kansa kan laps d'inta ya sakar mata kuka yace "Maamah bansan meyasa kika canja minba, kin tsaneni yanzu gaba daya, Maamah Ameer dinki ne fa, your only son, your source of happiness, that person who made up proud, am that Ameer who's always there for you, kin manta Ameer din da kullum baki iya bacci in baki tabbatar yaci abinci, yayi wanka sannan yayi bacci ba, Maamah please don't let auren wadda bakya so ya shiga tsakaninmu" daga nan yayi shiru yana jiran me zatace, babu lefi maganganun Ameer sunyi tasiri a zuciyarta ta dinga shafa kansa, da gaske Ameer is her only source of happiness, su duka sunsan bata yiwa Amaal rabin son da take yiwa Ameer, Sai tace "Ameer meyasa tun farko baka hak'ura da auren yarinyar nan Simbiat ba? Da ka hak'ura da duk abubuwan da suka faru basu faruba" yaji dadi sosai at last Maamah tayi masa magana me tsawo yace "Maamah kimin uzuri tun lokacin na fada miki bazan iya rayuwa idan babu itaba" Maamah ta dan fara jin tausayinsa amma batason nunawa don ita bazata shirya da shiba Sai ya rabu da Simbiat, ta dago kansa tayi rubbing hands d'inta duka biyun a face d'insa tace "Ka tafi office yanzu, you're getting late" daga nan ta sakeshi ya mik'e ya mata sallama ya fice. Har yaje office mamakin Maamah yake, Allah yasa taso Simbiat.
After 2days
A gajiye ya dawo gidan burinshi kawai ya kwanta don haka room d'in Simbiat ya wuce kai tsaye, da sallama ya shiga sai ya ganta da wasu Mata uku, ya koma baya da sauri, sukuma suka sauko daga bed suna gaida shi, ya answer da fara'a kafin ya fice, ganin ya koma yasa Simbiat bin bayan shi, kusan a tare suka shiga room d'in ya janyota jikinsa yana shafa lips d'inta yace "Babe meyasa kika kai bak'i bedroom dinki?" Ta fara kame kame tace "Ai naga ba bak'i bane, cousin sisters d'ina ne fa" ya wara idonsa yace "Amma ai bansan suba" tace "Eh daga IMO state suke ai" "Eyya Amma da kun zauna parlour dai yafi ai" yace, ta gaji da maganar gaba daya tace "A'a nidai banason fitina is better mu zauna can din" daga nan ta zame jikinta tana k'ok'arin shiga toilet ya janyota da sauri yace "what did you just say? Baki son fitina? This mean Afaf tana tonon ki da fitina idan kinyi bak'i" tayi saurin toshe bakinta tana zare ido as if Afaf tana gurin tace "A'a nidai bance ba, Dan Allah ka rufamin asiri" ya jata kan bed suka zauna yace "Simbiat zanje in tambayi Afaf da kaina, idan bazaki fadamin abinda take miki ba" idonta ya cicciko ta rik'e shi gam tace "Don't go please, bata min komai wallahi" ya dinga kallonta yana tausayinta yayi wiping tears daga flowing a idonta yace "Simbiat kin fiya sanyi da yawa, be strong please, ita mace ce and your female also,ki nuna mata bakyajin tsoronta, zaki samu saukin zaman gidan, ba koda yaushe nake zama da kuba I know for sure Afaf tana takura ki, why  can't you hurt her the way she hurts you,nasan batafi k'arfin kiba, kada ki Bari bak'in cikin wata ya sanya miki ciwon zuciya, be strong please sweetheart" maganar sa tayi mata dadi, amma ita tasan tun asali batada fitina, bata son hayaniya Sam amma gaskiya lamarin Afaf ba irin Wanda zaka tsaya kayi shiru bane, kamar yadda Ameer yace tsaf zata saka mata ciwon zuciya, tayi murmushin k'arfin hali tace "Nifa nace maka bata yimin komai" ya jingina da gadon yace "Babe kara kawai zaki min, nifa nasan halin Afaf tsaf, am kiyi hak'uri kinji, wata rana sai labari" tayi nodding kanta kawai ta mik'e tana cewa "bari na had'a ma ruwa kayi wanka, I know you most be tired" har ta shige toilet d'in be dena kallonta ba, hak'urinta da juriyarta ya kara Mata matsayi a zuciyarsa, yana shiga toilet ta fito masa da kaya ta koma gurin sisters d'inta.
Washe gari Jimoh tazo gidan, tunda Simbiat taji maganarta gabanta ke faduwa don tasan ganinta babu alhairi, duk da tana mugun jin yunwa amma kasa fitowa tayi don suna parlour, cikinta ya dinga juya mata, da dinga kuka kasa-kasa, zuwa can wani aman wahala ya taso mata,Sam batada strength d'in sauka kan gadon ma bare taje toilet haka ta dinga amai me daci ajikinta, sai bayan asr Jimoh ta wuce zuwa time din kam Simbiat ta gama jigata kukanma ta hak'ura ta Dena sai hawaye ne kawai wani ke koro wani, bayan kamar minti goma sai ga sallamar Ameer, ganinta unconscious ba k'aramin daga masa hankali yayi ba, da gudu ya d'auko ta ya sakata a mota suka wuce Aminu kano, dake yanada friend Dr. Haiydar yasa tun kafin su k'arasa ya kirasa ya fada masa inda zasu hadu, suna karasawa Haiydar da Dr.kabeer suka karbi Simbiat suka rufa a kanta, investigation ya nuna musu cewa ulcer ne ke damunta, sai kuma ciki da takeda shi na 2months ....aww fadar  irin farin icikin da Ameer yashi bata bakine, beyi tunanin haka ba Sam ya dinga hamdala , sai bayan isha suka dawo gidan, lokacin Simbiat har tayi bacci ma, Ameer kasa hak'ura yayi yayi dialing number Maamah, da sauri tayi picking, fuskarsa dauke da fara'a yace "Maamah dama kira nayi in fada miki,kin kusa samun grandson or daughter..Simbiat tanada ciki, duk da Maamah tana masifar son yara, kasancewar guda biyu Allah ya bata amma bataji dadin maganar ba Sam, taso ace Afaf keda ciki ba Simbiat ba, a hankali tace "Allah ya raba lafiya" daga nan tayi hanging, Sam Ameer beji dadi ba ,meyasa?meyasa Maamah bazata so Simbiat ba duk da tana shirin Samar musu da farin ciki a familynsu, wato Babe ba?......

Cute😍

 mowar miji (Borar Danginsa)Where stories live. Discover now