Ni dai kasa Daurewa nayi, nace,
"Mami ina Hamma ne, ko baya nan ne?"

"A'ah yana nan, shima yana cikin asibitin nan be da lafiya, amman yanzu Dady ya ce, min ya farka, ki kwantar da hankalin ki da sauki."

Hankalina ji nayi ya kara tashi da a kwance nake da sauri na mike zaune, zaman kasa yi min yayi na mike da sauri.

Ai kuwa nayi gaba zan fadi saboda rashin kwarin jiki na.

Da sauri Mami ta riko ni, ta ce,
"Ina zaki?"

"Mami gun Hamma zani."
Zaunar da ni Mami tayi, ta ce,
"Kiyi hakuri, anjima kaje kinji."

Dan dole na hakura, kwanciyya nayi amman duk hankalina baya jikina.

Karfe uku ina kwance naji an budo kofar dakin Juyowa nayi.

Hamma na gani da sauri ya shigo. Mikewa nayi zaune da sauri.

Sai da yazo gaban gadon ya durkusa, hannun sa ya kai, kan wuya na, ya taba fuskata, ya juyar da ita gefe, ya kuma juyar da ita gefe.

Wani murmushi ya saka, rumgumeni yayi a jikin sa, ya dago ni ya kuma mayar dani.

Sai da yai haka sau uku sannan ya kamo hannuna, ya kai dan yatsana bakin sa.

Cizar hannun yayi, wata kara na saki da sauri ya zare hannun yana dariya. Nima dariyar nayi.

Kan gadon ya hau ya zauna, ya janyo ni jikin sa ya rumgume ni.

Saukar danshi naji a bayana wannan yasa na dago da sauri.

Haawaye na gani a idon Hamma Najib,
"Haba Hamma mene abin kuka?"

"Najwa hankalina ya tashi sosai, kwakwalwata ta samu rudani da kin mutu da bansan ya zanyi da rai na ba. Da bansan ina zan shiga ba. Da bansan ya...."

"Haba Hamma, kamar ba musulmi ba, zaka dinga ringa wannan maganar, baka san Allah na jarabar bawa yaga ya zai yi ba.
Ka kuma san Allah me rahama da jinkai da ya baka ni, da ya dauke ni, haka Allah zai mayar maka da wacce tafi ni, hamma kana mika komai ga Allah dan zai iya jarabar ka yaga yadda zakayi."

Yatsan sa ya saka ya rufe min baki, ya ce,
"Najwa nasan da wannan kuma ina kokari, amman ki tayani da murna da godewa Allah da ya bar min ke."

Ya fada hawaye na zubowa daga idon sa.

Magana ya cigaba dayi,
"Bazan iya kwatan ta miki halin da na shiga ba da baki da lafiya, haka nan bazan iya kwatan ta miki halin da na shiga ba da aka ce min kin mutu. Cikin kan kannin lokaci na koma wani iri...."

Mami ce ta shigo dakin da sallama. Da sauri Najwa ta janye jikin ta daga na Najib.

Basket ne a hannun ta, mikawa Najib tayi, ta ce,
"Ka bata abincin ta ci."

Kai ya gyada mata, fita tayi. Kallon sa ya maida kan Najwa wacce take shafa cikin ta.

Tinda ta farka bata ji motsin da ya sabai mata ba. Ko lafiya?

Tausaya mata yayi, ya ce,
"Baby na. Komai ya samu ga bawa mukadari ne, kuma haka Allah ya kaddarar ta mana."

"Haka ne Honey. Me ya faru?"
Hawayen idon sa ya goge ya ce,
"Baby mun rasa Babyn mu."

"Innalillahi wainna illahir rajiun!"
Ta fada a cikin zuciyar ta.

Shiru tayi, kallon ta yayi ya jawo ta jikin sa, yana lallashin ta dan yasan kukan zuci take duk dan kar ta tayar masa da hankali.

Najwa bata taba kara sanin tana son Cikin jikin ba sai yanzu da ta rasa shi.

Tabbas kamar ya sani kukan zuci take dan sai ajiyar zuciya take saukewa.

Sun jima a haka kafin ta daina.

Zaunar da ita yayi ya zubo mata abincin da Mami tayo mata.

Dankali ne da hanta ta dafo mata, sai farfesun kayan ciki.

Kadan ta iya ci dan cikin ta a cunkushe yake.

Suna gamawa cikin ta ya hau ciwo nan da nan Najib ya rikice.

Dr Farouk ya kira, dubata yayi ya ce tasha magani ba wani abu bane, rashin cin abincin da batayi ne kwana biyu shiyasa. Amman a hankali zata daina ciwon in ta ci abinci.

Shifa Najib yana mantawa dashi likita ne, dan indai abu ya samu Najwa rikicewa yake ya manta da komai da komai.

Sai da ta Sha maganin sannan cikin ya lafa mata.

Bacci ne ya sauke ta. Kwanan su Uku suka Koma gida.

Gidan Mami suka koma dan Mami sam taki ta bar mishi Najwa dan har yanzu bata gama warwarewa ba.

Haka ya hakura, kayan da Mami tasa ya dauko a gida shi ya tuna masa da Sumaiyya ma.

Yana shiga gidan yaga shigar ta part din ta ita da wasu kawayen ta.

Bangaren Najwa yayi ya debo mata kayan sawar ta.

Har zai wuce ya ce, bari ya leka gun Sumaiyya.

Zai shiga kenan yaji shewar su, suna cewa,
"Ashe kin rabu da Alakakai."

Suka kara kwashewa da dariya. Be san da wa suke ba kawai ya juya ya bar wajen.

Gidan Mami ya koma, dakin Mami ya shiga dai dai fitowar Najwa daga wanka kenan.

Karasawa yayi ya kamo ta, ya zaunar da ita a gefen gado.

Shi ya shirya ta, sannan ya saka mata kaya.

Kwanciyya tayi dan bacci take ji. Shima gadon ya hau zai kwanta.

Da sauri ta Najwa ta mike, kallon ta yayi ya ce,
"Menene cikin ne?"

Kai ta girgiza ta ce,
"Allah ka tashi ka fita salam Mami tazo ta ganmu tare."

Kallon ta ya tsaya ya ce,
"To shine me?"

"Haba Hamma kai fa baka da kunya ko?"
Baki ya bude yana kallon ta.

Ya ce,
"Nine banda kunya ko?"

Kai ta girgiza,
"A'ah zan nuna miki bani da kunya ne a gaban Mami."

"A'ah Hamma ayi hakuri."
"Naki."

"Shikenan."
Ta fada tana mikewa.

Janyo ta yayi ta fada jikin sa,
"Yi hakuri man."

Shiru tayi tana kokarin tashi daga jikin sa.

Tausa ya farai mata, tausar da rabin ta tsokana ce.

Tini jikin ta yai sanyi tai shiru tana amsar sako da yake aika mata.

Jin shirin yai yawa yasa ya leka fuskar ta.

Idon ta a lumshe, sai murmushi take.

Cakul kuli yai mata ai kuwa da sauri ta mike tana dariya.

"Haba Honey Bacci fa nake yi."
"Na sani amman akwai abinda nake so muyi magana akai."

Mikewa tayi zaune, ta ce,
"Ina ji."


*MS Indabawa*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now