Sai da suka ci suka koshi sannan ya dauke ta, suka haye kan kujera.

Tausa ya dinga yiwa Najwa har bacci ya dauke ta bata sani ba.

Jikin ta yaji da zafi har lokacin wannan yasa yai waya asibiti aka kawo masa abinda yasan zai bukata.

A ciki da allura da magunguna. Tana kwance ta farka, kallon sa ta tsaya yi dan ya zuba mata ido ya lula duniyar tunani.

A hankali ta mike, ta kamo hannun sa da ya zuba taguni ta ce,
"Hamma lafiya?"

Murmushi ya sakar mata ya ce,
"Baby na, jikin ki zafi, bari na baki magani kinji."

Ba abinda Najwa ta tsana kamar magani da allura, fuska ta marairaice, ta ce,
"Haba Dai ai zan warware,"

Be kalle ta ba ya janyo first aid box din da aka kawo masa, allura taga yana hadawa, ai tini cikin ta ya duri ruwa.

Kallon ta yayi, ta ce,
"Hamma dan Allah kada kai min allura, bana so."

Ajiyewa yayi ya janyo ta jikin sa, ya rumgume ta, a hankali ya dinga shafa jikin ta har ta lumshe ido, a hankali ya janye Siket din jikin ta.

Allurar ya dauka, ya soka mata, wata wahalalliyar kara ta saki, rumgume ta ya kara yi, yana lallashin ta.

"Yi hakuri my soul mate, shine kadai abinda zan iya miki, sannu kinji."

Kanta ya dinga shafawa a hankali, ya ce,
"Najwa kin shayar dani da abinda ban taba zato ba abinda banyi tsammani ba,  Najwa Allah miki albarka, Ubangiji ya albarka ce, Allah karawa Dady da Mami lafiya da nisan kwana. Hakika ina alfahari dake kina da gurbi babba a cikin zuciya. Ba zan taba iya rayuwa babu ke ba Najwa. Allah miki albarka."

Ido Najwa ta lumshe kawai, Albarka tin daren jiya take shan ta yafi a kirga.

Bacci ne ya kuma dauke ta, daukar ta yayi, ya kai ta dakin ta,  kallon ta ya tsaya yo yana mamakin yadda ya same ta da yadda yaji ta. Najwa ta daban ce, lallai ya kuma yadda da Najwa ta daban ce.

Ya jima yana kallon ta kafin daga karshe ya tashi ya fita.

Shi da kansa ya gyara gidan ya kunna turaren wuta sannan ya koma dakin da take, ya zuba mata ido kamar TV.

Yana zaune, har akai sallah azahar, wannan yasa ya tafi massalaci daga can Dady ya kira sa, ba dan yaso ba ya tafi ya bar Najwa.

Najwa kuwa bata tashi farkawa ba sai karfe uku Najwa ta farka.

Tana farkawa tai sallah, sannan fitowa ta nufi kitchen, abinci ta daura musu, miyar kaji tayi, sai shinkafa da ta zuba mata kayan lambu a ciki. Sai farfesun kayan ciki da tayi. Zubo ta hada wanda ta zuba masa kokonba a ciki.

Sai da ta gama komai ta jere shi a daining sannan ta nufi Bandaki dan yin wanka.

Wanka tayi ta sake tsantsara kwalliya. Cikin riga da siket na atamfa, ta dasa daurin ta ta saka dankunne da sarka da abin hannu.

Sosai ta fito a amaryar ta dama ga lalle kafa da hannu.

Gidan ta kara turarewa tai sallah la'asar sannan ta koma falo ta zauna.

Sai karfe biyar sannan Najib ya dawo, lokacin tana dakin ta.

Fitowar ta kennan yana karasa shigowa falon, da dan gudun ta, ta karasa gare shi, tana fadin,
"Oyoyo My Honey."

Wani dadi yaji abinda be taba samu ba kenan ya dawo gida a nuna anji dadin dawowar tashi.

Hugging nata yayi, shima ya ce,
"Sannu Baby nah "

Ya dago da fuskar ta yana kallon yadda tayi kwalliya kamar ka sace ta ka gudu.

Kiss yai mata a saman idon ta, da wuhan ta. Sannan suka karasa falo.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now