"Sumaiyya!"
Ya kira sunan ta.

"Na'am!"
Kai ya jinjina ya ce,
"Anjima da magariba za ayi party, dan haka zan aiko a dauke ku shikenan."

"To sai anjiman."
Ta kashe waya tana kallon kawar ta da ta shirya mata duk plan din ta.

Kawar  ta ce,
"ko kefa!"
Summy ta ce.
"Ke dai bari."

Sukai shiru saboda shigowar wasu kawayen Sumaiyya. Kallon
"Yau fa zamu daga. Amman naga ko maganar bai yi min ba...."

Wayar ta ce, ta katse mata tunanin tana kai duban ta taga Najib ne.

Dagawa tayi, ta ce,
"Ya ne?"

"Maganar tafiya nan zan miki, karfe sha biyu zamu daga dan haka ki zama cikin shiri."

"To shikenan sai anjima."
Ya kashe wayar.

Ihu ta dauka ta ce,
"Tafiyar fa na nan. Amarya zata zauna gadin gida kenan."

*******
Tin karfe biyar ake wa Najwa kwalliya inda har Magariba ba a gama ba.  iya gajiya Najwa ta gama gajiya daman jikin ta ba gwari ga rashin cin abinci da ta kasa ci.

Ana gamawa ta saka wata doguwar rigar material baki, me ado golding stones, golden jaka da takalmi ta dauka.

Haka nan dankunnen ta da sarka duk golding ne. Ina ka ga farar mace cikin bakin abu.

Kowa ya shirya dan har an debe jama'ar dake cikin gidan.

Najwa aka bari kawai ita da Mami dan Najib be karaso ba.

Najwa na daki, Mami ta aiko Talle ta fito da ita dan Najib na falo yana jiran ta.

Talle na shiga taga Najwa ta saki baki tana kallon ta.

"Anty ke ce kuwa? Wannan in Ya Najib ya ganshi ai sai ya zauce."

Murmushi Najwa tayi ta ce,
"Ke kin fiys tsokana."

"Uhnn tashi muje yana kasa yana jiran ki."

Ji tayi gaban ta ya fadi. mikewa tayi a hankali ta bi bayan Talle, tafiya take kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki.

Wanda tafiyar kan ta ba karamin daukar hankali take ba. Najib tin tana stair ya zuba mata ido, yana sanye da wata golding colour shadda wacce sai kalli take, kansa sanye da hula kalar kayan sa. Gashin kan sa ya kwanta ta gefe.

Fuskar sa sai fitar da sheki take,  har ta karaso be san ta karaso ba saboda kallon da yake mata. ba karamin hankalin sa ta dauke ba.

Sai da Talle ta zungure shi sannan ya motsa. Kallon ta yayi ya ce,
"Malama tafi ki bawa mutane waje."

Dariya ta yi ta ce,
"Eh ai na gama maka tinda na dauko maka ita. Bari nai muku hoto ko?"

Ta dadauke su, tana dariya.
"Gaskiya Ya Najib kun dace da juna."

"Kije ana jiran ki."
Ido ta bude tayi waje. Da saurin ya matsowa wajen ta. Baya tayi, tana kallon sa.

Binta yake yi tana kara matsawa har ya kaita jikin bango, hade ta yayi da kirjin ta yana shakar kamshin turaren ta.

"Hamma!"
Ta kira sunan sa, cikin shagwaba.

Hannun sa ya saka ya zagayo dashi ta kugun ta.

Wani irin abu taji na yawo a jikin. Kamar yadda shima ya ji.

"Baby u look soo beautiful than every day."
"Naji pkease sake ni kar Mami tazo kaga yanzu zata sauko."

"Wacce Mami da ta riga da ta tafi."
Ido ta zaro kirjin ta na tsanan ta bugo.

Hannun sa ya saka yana shafa fuskar ta zuwa saman kirjin ta. Idon ta, ta matse tsam, kirjin ta ne ya tsanan ta bugu.

Bakin sa ya matsar dai dai nata, dai dai lokacin da wayar sa ta hau bugawa.

Dauka yayi yace,
"Mallam gani nan."

Ya kashe wayar. Yana rumgume ta a jikin sa.
Tashin bugun kirjin ta yaji ya dago ta da  sauki yana kallon ta.

"Lafiya kuwa?"
Ya tambaye ta yana daura hannun sa akan kirjin ta. Bugawa yake da sauri da sauri.

"Oh haba My Naj mene abin tsoro common kar ki damu ba abinda zan miki kinji."

Kai ta gyada hannun ta ya kamo, suka fita lokacin Khaleel na tsaye a jikin motar da zasu shiga.

Wata Golding colour mota ce, ta ido ma kasan motar taji kudi.

A bangaren Sumaiyya kuwa tana can an mata kwalliya ta shirya cikin wani less ja, an nada mata blue din head da yake shine adon jikin sa.

Kawayen ta su biyar duk sunyi kwalliya amman daga ganin su kai kasan yan duniya ne. Dan babu kamun kai a tare dasu sam.

Waje da ban aka ware musu shi, inda aka cika musu gaban su da kayan abinci da aka tanada.

Yan uwa da yawa sun hallaci partyn haka nan kawayen Mami duk sun je.

Wajen ya cika da manyan mutane masu kudi, haka abokan Najib duk sunje kowa ka gani a gun ba baya ba.

Bangaren kawayen Najwa ma sunyi kyau sunyi anko cikin wani milk din material sai bakin abu da suka daura akan su.

Hamma Salim ma yayi adon sa cikin wata milk din shadda. Basma kuwa wani farin material ta saka me adon yello a jiki an mata dauri da yellown abu.

Momyn Zahra, ma ba a bar su a baya ba. Kowa yayi ado na kece raini duk wajen ba baya kowa yayi kyau.

Sai karfe bakwai aka fara maganar zuwan su ango da Amarya.

Ita Sumaiyya ana can ana zuba ido aga shigar da amarya tayi.

Kawayen Amarya da abokan ango su suka shigo da ango da amarya ana musu likin yan dubu dubu.

Har aka karasa wajen zaman su. Ana daukar su hotuna. Wajensu ya cika da jama'a kowa nason daukar su.

Sumaiyya kuwa yadda taga Najwa ba karamin tada mata da hankali yayi ba.

Dan batai tsamanin ganin ta a haka ba. Kyawun Najwa ba karamin firgita ta yayi ba.

Haka nan ganin dacen su da sukai da Najin shima abin ya tada mata da hankali.

Duk sai ta ganta ta dishashe. Kasa koda motsi tayi.

Bangaren ango da amarya kuwa duk an watse an barsu su kadai.

Anaci an sha, sannan kawayen amarya duk sun cashe, inda aka kira ango da amarya da su fito fili.

A tare suka mike suka fito Najib na Rike da hannun ta.

Summy kuwa kamar tayi kuka dan takaici, duk yadda kawayen ta suka so suje suyi musu liki ki tayi.

A can kuwa duk yan uwa sun rufe su, suna musu liki ana hotu na.

Sumaiyya kuwa daga karshe tashin kawayen ta tayi suka fita daga hall din gaba daya.

Anyi partyn lafiya an tashi lafiya. Inda kowa ya nufi gidajen da ya sauka.

Ango da Amarya na mota za'a maida Najwa gida.

Najib ji yake kamar ya saka ihu in ya tuna zai tafi ya bar Najwa.



*Indabawa*

NAJWA Complete ✔Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt