"Najwa yar kice, kuma kinga ba auren dole bane tsakanin su za'a cuce su akace a raba abin nan. Dan haka kuyi hakuri. Nasan Najwa da hakuri kuma nasan Najwa zata iya zama da kowanne irin mutun ne. To kiyi hakuri amman zanje na samu su Baffah naji daga bakin su."

Hawayen fuskar ta, ta goge,
"Wallahi ni kaina bana son a fasa bain nan."

"Kar ki damu. In Allah yayi Najwa matar Najib ce ba abinda zai sa a fasa kuma komai daren dadewa sai su  auri junan su."

"Allah ya tabbayar da alherin sa."
"Ameen! Bari naje wajen su Baffah."

Ya fita. Gidan su Baffah yaje, a babban falo ya tadda Baffah da yayen sa, sai Najib dake jikin Baffah kamar mara lafiya.

Sunyi jugum jigum, duk tunanin su ya kwace.

Dady na zuwa, Najib yayo wajen sa, yana hawaye yana fadin.
"Dady dan Allah kacewa Najwa kar ta fasa aure na Dady dan Allah."

Hannun sa Dady ya koma, ya koma cikin dakin dashi.

Zaunar dashi yayi, sannan ya gaida Baffah, da yayen sa.

Dafa Najib yayi, ya ce,
"Me yake faruwa?"

"Dady Najwa ce ta kirani tana cewa wai sai na janye batun auren ta. Akan  Sumaiyya."

Murmushi Dady yayi, ya ce,
"Najwa na son ka ko kuwa?"

Kai kawai Najib ya iya dagawa.
"To ka kwantar da hankalin ka. Najwa kamar ta zama matar kace."

"Dady da gaske?"
"Eh! Insha Allahu."

Kallon sa Ya dawo dashi wajen su Baffah. Ya ce,
"Wato Baffa abinda ake ciki shine, Sumaiyya matar Najib yar uwan Su Maman  Najwa ce. wannan yasa ita Najwan bata so ayi abin amman komai ya wuce."

"To Masha Allah."
"Amman yanzu abinda ake ciki ma. Wata kanwar mahaifin Sumaiyya ce tazo gida ta zage su Najwan dan shirme ko tana tunanin hakan zai sa a fasa auren."

Dariya su Uncle sukai, suka ce,
"Kasan mata ai."

"Haka ne?"
Najib kuwa a hankali ya mike yayi gidan su Najwa.

Yana shiga, Mami ta ce ya hau tana sama.

Falon sama ya hau ya zauna, Basma ce ta fito, tana ganin sa, ta taho a gaida shi.

"Kira min Addar ki."
"Toh!"

Tayi dakin Najwa. Tin a bakin kofa take yin sallama taji shiru.

Kofar dakin ta bude ta shige, Najwa ta gani kefe akan gado.

Jijjiga ta take, tana cewa,
"Adda kizo inji Hamma Najib."

Duk jijjigawar da tayi mata bata motsa ba.

Fita tayi da sauri, ta ce,
"Hamma kaga ina ta kiranta bata amsa ba.."

"Bata amsa ba?"
"Eh!"

"Muje na gani."
Dago ta yayi, a lokacin ya gane bama ta numfashi.

Nan da nan ya fara bata taimakon gaggawa, har sai da yaga numfashin ta ya dawo sannan ya samu nutsuwa.

Mami yaje kasa ya sama ya sheda mata duk abinda ya faru.

Mami itama rudewa tayi, Dady ta kira, daukar ta Najib yayi suka nufi asibitin unguwar.

Shi yayi mata duk abinda zata bukata aka daura mata ruwa.

Sai wajen Isha'i ta farka, Lokacin Najib ne kadai a dakin.

Tana ganin shi taji wani sanyi tina abinda ya faru ne yasa ta juyar da fuskar ta da sauri.

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now