Kayan da Najib ya soyawa Lil N ya mika mata ta mikawa Khadija.
"gashi inji Hamma."

Kallon ta yayi, Ya ce,
"In jita dai. Nawa na nan zuwa."

Sukai sallama bayan sun yi musayar number junan su.

Har gida ya maida ita lokacin Baffah ya dawo suna falo shi da Ummah.

Yana ganin su ya saki fara'a ya ce,
"Kun dawo?"

"Eh Baffah mun dawo. Ya gidan?"
Najwa ta tambaye shi.

"Lafiya lou."
Sannan suka gaisa da Najib yana jansa.

Najwa ita dai tana mamakin Najib ya ja su Baffah yaje yaja su Abbah.

Tana farin cikin samun miji da ba ruwan sa.

Sai wajen karfe tara ya Mike yayi  wa Su Ummah sallama.

Ummah ce ta kalli Najwa ta ce,
"Kije ki rakashi man."

Mikewa tayi, tabi bayan sa. Tafiyar ta ya jiyo wannan yasa ya juyo yana kallon ta.

Murmushi ya saki, ya ce,
"Najwa tafiyar taki ma daban take."

"Ni dai muje."
Dariya yayi, ya ce,
"Bama zaki tsaya kiji ba kenan."

Har mota ta rakashi sukai sallama ya tafi.

Daki ta tafi tayi wanka ta haye gado. Kiran sane ya shigo dan har yaje gida.

"Love!"
"Na'am Hamma ya hanya?"

"Hanya lafiya. Ya na baro ki."
"Lafiya klo."

"Baby na gobe nake son na koma gida fa."
Gaban ta taji ya fadi.

Duk da tana matsa masa ya koma wajen matar sa da aikin.

"Amman Hamma kuma shine baka fadamin ba."

"Kiyi hakuri Baby na, bana son ki shiga damuwa ne."

Dan murmushi tayi, ta ce,
"To ya zanyi, amman da kafadan ai."

"Ayi min affuwa bazan kara ba to."

"Shikenan Allah kaimu goben."

"Ameen. Wallahi Ina kara son ki Najwa saboda hankalin ki da hakuri. Wannan yasa nake kara kwadayin zamowar ki matata."

"Hmm Hamma kenan. To kije ki kwanta sai da safe kiyi alwala da sallah kinji."

"Insha Allah sai da safe."

Sukai sallama. Wani abu taji ya tare mata kirjin ta. Tasan ba komai bane sai kishin Najib.

To ya zatayi, tinda Allah ya daura mata son shi.

Alwala taje tayo tayi sallah tana Rokar Allah ya rage mata zafin kishi.

Ta jima tana addu'ar sannan ta koma kan gado.

Bata kara sanin tana son Najib ba sai yau, gashi Najib ba nata bane ita kadai.

Kuka ta fashe dashi, ta jima a kwance dan sai wajen karfe uku ta samu tayi bacci.

Karfe biyar mike tayi sallah ta koma.

Ummah kuwa tin da ta tashi taga Najwa bata fito ba tasan ba lafiya ba.

Dakin ta, ta shiga ta ganta a kwance tana bacci.

Falo ta koma. Sai karfe goma ta tashi daga bacci.

Wanka tayi ta shirya cikin wata doguwar purple din riga.

Batayi kwalliya ba daga hoda sai man lebe sai turare da ta fesa.

Falo tayi, Ummah ta hanga, akan kujera, gefen kafar ta, ta karasa ta gaida ta.

Amsawa Ummah tayi tana leka fuskar ta,
"Najwa! Lafiya?"

"Lafiya lou Ummah."
"Amman naga idon ki ya kunbura haka."

"Lah Ummah wallahi bacci ne banyi ba jiya shiyasa."

"Saboda me to?"
"Kai nane yake dan ciwo."

"Sannu to, tashi kije kici abinci kisha magani."
"Toh!"

Ta mike, har ta fara tafiya ta juyo ta ce,
"Ummah yau fa Hamma zai koma."

Murmushi Ummah tayi, ta ce,
"Haka ya fada min."

Gaba Najwa tayi kitchen ta shiga tea kadai ta sha. Ta zauna tunani.

Sai daga baya ta tashi ta kwaba cake, tayi beaking nashi, meat pie ta soya shima dayake akwai dambun nama wannan yasa nan da nan ta gama ta nade su a foilpaper.

Sauran ta diba tayi falo dasu. A falo ta hage shi a kasa gefen Ummah.

Ummah na waya, har ta juya, ya kira sunan ta.
"Najwa!"

Wannan yasa ta juyo, falon ta karaso kanta a kasa.

Farantin ta ajiye a gefen Ummah, ta durkusa tana gaida shi.

"Ina kwana?"
Shiru taji wannan yasa ta dago tana kallon sa.

Kallon ta shima yake, mikewa tayi ta shige daki.

Sai da ta tabbatar da Ummah ta gama waya sannan ta dawo falo.

A gefen Ummah ta zauna. Kallon ta Ummah tayi, ta ce,
"Najwa je ki, ki samar masa abinda zai ci be karya ba."

Mikewa tayi jiki a sanyaye tana tafiya kamar bata da lafiya.

Shi dai kallon ta yake kawai yana ganin canjin da ta sauya daga jiya da dare zuwa yau.

Kitchen din ta shiga ta dauko dankali ta feraye ta dafa ta kwakwule cikin.

Nama ta nika ta hada da attaruhu da albasa, ta soya sama sama sannan ta cusa a cikin dankalin.

A cikin ruwan kwai ta dinga sakawa tana soyawa.

Tana gamawa ta daura ruwan kunu, motsi taji daga bayan ta. Juyawa tayi.

Ido biyu sukayi dashi, yana kallon ta. Kasa tayi da kanta,


*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now