"Wallahi kuwa. Ace mutum da kanwar sa be san ta ba."

"Na santa man, kinsan tin da na bar kasar bana ganin ta ko nazo."
"Allah ya kyauta."

Fita Najib yayi, bangaren su Baba yana basu Labari.

Ba wanda yakai su bara'atu murna.

Dady ne ya kalli Mami ya ce,
"Kinga ikon Allah ko? Allah ya amsa addu'ar Baffah da Ummah."

"Abinda na gama tunani kenan. Kaga Baffah akan haka har makka yaje yayi addu'a ashe Allah ya hada su bama mu sani ba. Alhamdulillah ai ni zanyiwa Ummah wannan albishir din."

Ta fada ta nayin dariya Dady ma dariyar yayi, ya ce,
"Uwar Amarya!"

"Wallahi kuwa tuwo na mai na. Kai Alhamdulilah ai kowa yayi kwadayin samun Najwa wallahi."

Dady ya ce,
"Mun gama magana ma, zanje na fadawa su Baffah wata biyu masu zuwa za'ayi komai a gama."

"Toh Allah yasa ayi da mu."
Dady ya amsa da
"Ameen!"

Najib kuwa tin lokacin ya fara shirin zuwa Kano.

Sunyi waya da Najwa be fada mata komai ba sai lokacin da zai zo.

Tin da ya fada mata ta fara shirye shiryen zuwan sa.

Girke girken da zatai masa, da kayan da zata sa duk sai da ta tanade su.

Tana son fadawa Mamin ta tana jin kunya.

Suna zaune a falo, ita da Salim ta ce,
"Hamman Jibi fa zai zo."

Kallon ta yayi, ya ce,
"Waye?"

"Shi man."
"Najwa kenan wallahi kin fiya kunya. Yanzu sunan nashi ma baza ki iya fada ba."

Shiru tayi, kai ya girgiza ya ce,
"Kin fadawa Dady da Mami ne?"

"Hamma wallahi bazan iya ba."
Dariya yayi, ya ce,

"To ya kenan?"
"Ka fadawa musu."

"To shikenan. Kinsan kuwa nan da wata biyu za ayi komai a gama."

Mikewa tayi daki da gudu, dariya yayi, ya nufi dakin Mamin su.

Zama yayi, ya ce,
"Mami 'yar ki dai ta mayar dani dan aike."

"Me kuma ta kuma aiko ka."
"Wai zai zo, shine ta kasa fada."

"Allah sarki Najwa. To menene? Yaushe zai karaso?"
"Jibi ne."

"To Allah kaimu zan fadawa Dadyn naku."
Duk abin nan da ake su Mami ba su san wa yake neman auren Najwa ba.

Mami, ta kalli Salim ta ce,
"Kasan har an kai sadaki da komai. Laife kawai zasu kawo."

"Ikon Allah Abin da zafi zafi haka."
"Wallahi."

"Allah sanya alheri ya kore duk wata fitina."
"Ameen Ya Allah."

Najib ma ya fadawa su Mami, ranar zuwan sa Kano, kuma yasan da an gama komai, daurin aure kawai ya rage da kai laife.

Sumaiyya ya sama ya fada mata duk halin da ake ciki, da zancen auren sa.

Ji tayi kamar tayi bindiga, kudi ya zube mata masu yawa tare da sabuwar mota ban da laife da ya jido mata ita.

Amman duk wannan abin basu burgeta ba. A ranta ta dauki alwashi sai taga bayan matar nan tasa.

A haka ya tafi ya bar ta, zuciyar ta kamar ta fashe dan bakin ciki.

Yana tafiya, ta kira kawar ta Jamila.
"Jamsy!"

"Na'am Summy lafiya kuwa?"
"Ina fa lafiya. Najib ne zai kara aure fa?"

"Aure kuma ana zaune lafiya."
"Kedai bari yanzu mene abin yi."

NAJWA Complete ✔Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang