Ta karashe maganar cikin shagwaba,
"Sorry Baby na. Kema kinsan jiya naso na dawo amman ban samu dama ba. Gashi yau ma haka. Kiyi hakuri insha Allahu gobe zan sauka."

"Allah yasa."
"Ameen!"

"Amman fa sai mun kara yi a Katsina,"
"Haba dai, A'ah."

"Ina ruwan ki, da su Basma zamu yi abin mu."
Dariya tayi, ta ce,
"Ayi lafiya."

"Yauwah!"
"To yaushe zaka zo kano?"

"Bazan zo ba!"
"Saboda me?"
ta fada da muryar kuka."

"Oo Baby na yanzu ta zama shagwababiya fa,"

"Ni dai ga abinda na tambaye ka nan."
"To shikenan daina kukan."

"Na daina."
"Tayaya kike zaton zan ki zuwa wajen ki haka kawai. Ni da nake son na kasance tare dake a koda yaushe."

"Uhm!"
"Baki yadda ba kenan!"

"Ni bance ba."
Ta fada muryar ta kamar zata fashe da kuka.

"To shikenan bari na fada miki dalili na."
"Ina ji."

Dariya yayi, ya kwaikayi muryar ta, ya ce,
"Ina ji."

"Allah dan kaga ina son ji shine kake jamin rai ko?"

"A'ah a'ah yanzu zan fada miki."
Kukan karya ta fashe masa dashi,

"Yi hakuri, dalilina shine, bazan zo gidan ku ba, sai an san dani koma nace sai an bani ke."

Dariya tayi, ta ce,
"Da gaske?"

"Da gaske nake dan haka ki fadawa Dady, ya bada number wanda zamuje gun sa.
Kinsan da ta waje na ne da tini kin ahekara biyu a gida na.
To kince sai kin gama karatun ki. yanzu kuma ai kin gama ko?"

"Ni zan ma iya fadan ne?"
"To shikenan kar ki iya. Allah wannan kunyar taki karfa ta cuce ni."

Dariya tayi, kawai,
"Allah gobe nake son ki bani dan kafin na dawo na bawa Dady,  jibi suje."

"Ba bincike?"
"Baki yadda dani ba?"

"A'ah! Na yadda da kai."
"To ni na yadda dake ba sai an min bincike ba. Amman ke in munzo sai ayi ko?"

"Nifa bance ba."
"To me kika ce?"

"Sai na turo maka da number dai."
"Shikenan kinci abinci?"

"Yanzu zan ci."
"To kije kici ki dawo muyi wata magana."

"Toh!"
Ta fada, ta mike tana kashe wayar.

Dakin Mami ta shiga, Mami na zaune tana cin Nama.

Zama tayi itama taci ta sha lemo sannan tayi dakin Hamma Salim.

Yana zaune yana waya da Budurwar sa. Yana ganin ta ya bata suka gaisa sannan sukai sallama.

Kasa tayi da kai tana wasa da yatsun ta.

Kallon ta yayi yana dariya ya ce,
"Wai ke har yau kin ki daina jin kunya ta ko?
Nifa yayan kine in baki tambayen abu ba wa zaki tambaya."

Shiru tayi, kallon ta ya kuma yi, ya ce,
"Fadi mana kinji."

Ya kamo hannun ta. A hankali ta ce,
"Yaya daman wanda yake so nane ya ce, na fadawa Dady ya basu Number wanda zasuje gun su dan neman aure na."

Ta fada tana rufe fuskar ta. Dariya ya kwalkwale da ita.

Ya ce,
"Yanzu Najwa akan wannan kike jin kunya ta. Kada ki manta fa ni wanki ne, mene abin jin kunya anan."

Bata bude fuskar ta, ta mike, ta yi hanyar waje, ta ce,
"Hamma dan Allah ka fada masa dan gobe da safe yake spn number."

Ta fita a guje, Mami da Dady da suke Falo, suka bita da kallo.

Salim ne ya fito daga dakin sa yana dariya.

Gefen Dady ya zauna, Dady ya ce,
"Lafiya dai ko?"

Dariya yayi, ya ce,
"Dady kasan Najwa da kunya ai.  Sai kace akan ta aka fara bafulatana."

Dariya Dady, yayi, ya ce,
"Ai kunya ado ce."

"Haka ne Dady."
Mami ta ce,
"Kunyar me take ji to?"

Zama ya gyara, ya ce,
"Ta zo ta fada min ne, wanda suke soyayya dashi, yana son ya turo, shine suke so  address da number wanda zasuje gun sa."

Dariya Dady da Mami sukai, suka ce,
"Najwa kenan."

Dady ya ce,
"Abuja zasuje, sai ka bada Number Abban naku."

"To shikenan!"
Ya mike yayi dakin Najwa.

Najwa na kwance akan gado tana waya da Najib ya shigo dakin mikewa tayi da sauri ta kashe wayar.

*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now