Kasa sakewa tayi kanta a kasa.
"Najwa Ina fatan kin aminta dani. Najwa ni me son kine, na jima da son ki a raina. Kece farin ciki na."

Duk rashin surutun Najib yau bakin sa yaki rufuwa.

Zuba yake mata bayanai yake a kan duk yadda yake son ta.

Ya kasa yin shiru, Najwa kuwa shiru tayi tana sauraron sa.

Duk yadda tayi tunanin sa yawuce nan.

Gaskiya ya mata, kuma daga maganar sa ma ta fuskanci, ko shi waye.

Da kyar ya barta dan kasa barin ta yayi.

Itama tin bayan rabuwar su, ta fada kogin tunanin sa.

Sun rabu da shi akan gobe zai zo yai musu sallama kafin ya tafi.

Washe gari karfe tara suka shiga jarabawa, inda sha daya har sun fito.

Suna fitowa suka hange sa daga jikin motar sa.

Kasa tayi da kanta, suka karasa gun sa.

Dan durkusawa tayi ta Gaida shi. Amsa wa yayi idon sa kyar akan ta.

Zahra ce, ta ce,
"Har ka fito kenan."

"Eh wallahi, nazo naga Baby na na wuce."
Fuska Najwa ta rufe da tafin hannun ta dan kunya.

"To shikenan ni bari naje, sai munyi waya Allah kiyaye hanya."
"Ameen Zahra Nagode fa "

"Ba komai."
ta fada tana yin gaba

Kallon sa ya komar dashi kan Najwa.
"Baby nah!"

Shiru tayi,
"Toh! ni zan tafi, sai munyi waya."

Muryar ta yajiyo me dadi da sanyi tana masa addu'a.
"To Allah kiyaye hanya Allah kai ka ya dawo da kai  lafiya. Allah tsare."

Kallon ta ya tsaya yi, yana ta amsawa daa
"Ameen Ameen!"

Shiga yayi ta rufe masa kofa tana daga masa hannu.

Sai da taga tafiyar sa, sannan ta nufi hanyar hostel.

Zahra na ganin ta fara yin dariya ta ce,
"Baby ya soyayya."

Duka takai mata, ta ce,
"Bana so."

Kayan su suka hada, suka debo aka saka a motar gidan su.

Lokacin suka tafi gidan Mami har ta hada musu kayan abinci kala kala.

Wanka sukai sannan suka zauna, cin abinci.

Kwanciyya Najwa tayi dan yin bacci. Tinawa tayi da Najib wannan yasa ta dauki wayar ta, ta tura masa sako me dadi.

Yana sauka yaji karar wayar sa, dauka yayi, sakon Najwa ya gani.

Wani murmushi ne ya sauka akan fuskar sa wanda besan lokacin da ya fita ba.

Gidan Mami ya fara sauka dan ya samu abinda zai ci ya huta kuma.

Yana shiga yai wanka sannan ya ci abinci.

Bangaren sa na da ya shiga, ya kwanta bashi ya tashi ba sai yamma.

Lokacin ya kuma ganin wani text din nata.

Mamaki ne ya lullube shi, ganin Sumaiyya da take matar sa ma bata damu dashi haka ba.

In ya tafi in har be kirata ba, to baza ta taba kiran sa ba.

Sumaiyya duk abinda take so, Najib na mata shi. Kudi kuwa kamar me kullun zai dire mata.

Abunda yake hada shi da Sumaiyya shine rashin son yin aiki. Bazata taba gyara waje ba.

Haka nan bata son kitso, jikin ta dai zatai wanka sau da a rana, tai kwalliya amman kanta ba ya samun gyara sai ta gadama zataje saloon a tsefe a wanke a sake wani.

Sai rashin girki sam bazata masa girki ba. Duk yadda yake da son abinci amman baya samu dan in ya dawo sai dai ya samu abu me sauki ya dafa ya ci.

Bangaren sa kuwa zai iya cewa bata shiga sau biyar ba. Bare taga ya baci ta gyara masa ma.

Ga rashin kula, wai taga yayi dare ko yai tafiya ta kira sam babu wannan.

Sai dai in tana neman wani abu ne. Abin na damun sa.

Gashi wai safiyya tayi ta gaishe shi ya dawo daga aiki a tarbe shi ko ai masa sannu da zuwa duk bazai samu ba.

Be taba ganin ta da Alkur'ani ba bare yaji tana karatawa.

Shi da yake son mace me addini sai gashi Allah ya hada shi da Sumaiyya.

To ya godewa Allah kuma a koda yaushe yana mata addu'ar shiriya.

Har a isilamiyya ya saka ta amman bazai ce ta taba zuwa ba.

Ga rashin Sallah akan lokaci. Gashi bata son zuwa gaida su Mami. In yace yazo suje sai ta kawo wani abun.

*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now