Ganin zasu fita ne yasa ya barsu kaf ya tsaida su.

Bangaren sa ya nufa dan watsa ruwa. Yana shiga da gajiya ya tadda an hada masa ruwa.

Murmushi yayi a ransa dan yasan ba Summy ce da wannan aikin ba.

Dan tin daga harabar gidan yaga canji kuma yasan Mami ita ta aiko su dan su dan yi masa gyara.

Wankan yayi cikin farin ciki dan ruwan sai kamshi yake masa.

Sai da ya shirya ya nufi bangaren ta.

Tana zaune tana sana'ar tata ta kallo, tin wankan safe vata karayi ba.

Fuskarta sai maiko take yi. A gefen ta ya zauna.

Kallon ta yayi, itama haka dan tayi kewar sa.

Mamakin ta yake, bako sannu da zuwa bare ai masa ya hanya.

"Ya gidan?"
Shiya tambaye ta.

"Lafiya? Ya kake?"
Mikewa yayi be bata amsa ba.

Dan ba wannan abin ya kamata ya fito daga bakin ta ba.

Daining ya nufa, Fulas din dake daining din su kansu abin kalla ne.

Be taba ganin su a gidan ba, to ita da ba girkin take ba tayaya zai gansu.

Fulas Fulas din ya bude wani kamshi je ya doki hancin sa.

Masa ce an mata miyar nama miyar kanta abar a ce banda wani kamshi da take fitar wa.

Yawu ya hadiya. Zubawa yayi ya fara ci. Ji yayi kunnen sa kamar zai cire dan dadi.

Abincin yake ci cikin kwanciyar hankali a ransa ya a cewa wannan ba girkin su Bara'atu bane.

Summy kuwa kamshin girkin shi ya taso ta daga kallo  da take, dan ita ma sai taji yunwa.

Fried Rice din ta zuba ta fara ci kai ta fara gyadawa dan dadin girkin.

Yana gamawa da masar ya dauka ya saka a friji haka ma fried rice din.

Falo ya koma ya zauna biyo shi tayi ta zauna akan cinyar sa.

Kirjin ta, ta manna da nashi, tini hankalin sa ya tashi.
Romancing junan su suka fara daga nan ya dauke ta cak yayi dakin baccin sa da ita.

Su Najwa na komawa gida suka fara hada kayan su dan monday zasu fara lecturer.

Mami duk ba dadi taji, amman ya zatayi, goma ta arziki ta hada musu inda tasa a nema musu jirgi dan gobe suke son dira a kano jibi su wucce Katsina.

Gata kuma sai makaranta. Dady ma sai da ya basu kudi me yawa har airport suka raka su. Sai da suka ga tashin sanan suka juyo.

A kano ma suna dira har an zo daukar su. Mamin Najwa da murna ta tare su.

Inda da yamma ta kaisu shopping da kanta daga nan zooroad suka wuce ta karbo kusu dinkunan su.

Da dare kuma sukaje yiwa kakannin su sallama.

Kowa sukaje sai dai ya sanya musu albarka tare da addu'a.

Washe gari suka mika Katsina. Inda acan ma sai kewar su ake yi.

*Bayan Wata Biyu*

Karatu yayi nisa dan har sun kusa fara jarabawa first semester level three.

Komai lafiya yake tafiyar musu, inda har lokacin Najwa bata kula wani bare har ta tsaya da su.

Mami tini ta aika wa su Najib da yar aiki. Duk rashin son yar aiki da bayayi.

To yaya zaiyi sai yanzu ya gane daman can Sumaiyya kazama ce bata damu da ganin datti ta gyara wajen ba.

Haka nan girki ba iyawa tayi ba. Wannan yasa sai ya dawo da dare yake girka abinda zai ci.

Dan shi bazai iya cin abincin waje da na masu aiki ba.

Ita kuwa wani sabon san jiki ne ya same ta dan wanka ma da kyar take iya yi kullum yini take kallo sai chatting da kawaye.

Katsina ya kara shiryawa zuwa, wannan zuwan ba karamin addu'ar yayi na Allah ya hada shi da ita ba.

Tin da ya dira ya fara jin kwarin gwiwa wannan yasa yai wanka ya shirta ya fita.

Su Najwa kuwa sun koma hostel saboda jarabawar da suka fara.

Bikin wata mate din su za'a yi wannan yasa suka shirya zuwa Green house dan siya  mayafan da zasu amfani da shi.

Kamar hadin baki shima ya shirya ya tafi store din dan siyan abubuwan da zai danyi amfani dasu.

Shigar su kenan shima ya iso wajen, ciki shima ya shiga ya fara daukar abinda yake so.

Sai da ya gama tsab sannan ya nufi wajen biyan kudin.

Kamar daga sama ya hango ta tsaye a gun tana biyan kudin.

Kallon ta ya tsaya yi sosai, ganin zai kara rasa damar sa yasa ya ajiye kayan ya bi bayan su.

Motar da suka shiga yabi baya, a hankali a hankali har suka  karasa bakin gate din makarantar su.

Bin su ya cigaba dayi har suka karasa bakin hostel din su. Sai da suka shiga sannan ya samu wasu yan mata ya ce,
"Dan Allah yan matan can neke son ku kira min."

Kai yarinyar ta jinjina kai ta ce,
"Allah yasa su zo, dan basa kula samari."

Ta fada tana yin cikin dakin nasu.


*INDABAWA*

NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now