Wayar sa ya dauka ya fara yi mata magana.
"Sumaiyya daga ganin ki ma nasa kina da hankali da tarbiyya, batun ko kina da wanda kike so kuna banga alama ba, dan nasan kema zaki so samun miji kamar Najib. dan na tabbata yafi wanda kike so in da akwai ma. Dan Allah ki yadda da mu.  Ba da yaudara muka zo ba."

Ko da Sumaiyya taga sakon dariya tayi, ta ce,
"Allah sarki ai nagama samun miji insha Allahu."

Wata ziciyar kuma ta ce,
"To in kuma bashi da kudi fa."

Dayar zuciyar ta ce,
"Ai daga gani ma yana da kudi. Ke ni ko ban da kudi ina son sa haka."

Ta fada tana sauka daga whatsapp din nata.

Shiru shiru yaga Reply amman shiru, wannann yasa ya kira Number ta, sai da tayi ringing sau biyu sannan ta daga.

"Ranki ya dade kar a gaji damu."
Ya fada cikin sanyin murya.

Murmushi tayi, ta ce,
"Ba komai. Ya kake?"

Dadin amsar da ta bashi yasa ya saki murmushi shima ya ce,
"Lafiya Alhamdulilah. Ya kika je gida."

"Lafiya!"
Ta fada a sharen nan.

Murya ya dan gyara ya ce,
"Amman yau zaki zo kai amarya ko?"

Summy ta ce,
"Wallahi, saboda Hauwa ta takura min se nazo."

"Ai kam ya kamata kizo, zan zo gida na dauke ki."

Dadi taji a ranta, amman a fili ta ce,
"A'ah nagode zan zo kawai."

"To shikenan. Anjima mayi magana ki huta lafiya."

Suna gamawa ta daka tsalle tana murnar babban kamun da tayi.

Shi kuwa Najib kallon Khaleel kawai yake, yana kara jin son sa a ran sa.

Khaleel da baya kule kule amman yau shi ake garawa duk da bashi ke so ba.

Dariya ya sheke da ita yana cewa.
"Bro ai ko, babyn taka bata wahalar da kai haka ba."

Harara sa Khaleel yayi, ya ce,
"Eh saboda naga ana wahalar da kai, shiyasa na dauke maka wannan wahalar kar abin yai maka yawa."

Fuska Najib ya dan hade, ya ce,
"Kai Ware!"

Dariya Khaleel yayi, ya ce,
"Naji."




*Najwa* ce zaune gefen Mami, rike da littafin fikihu tana duba shi. Ajiye shi tayi, Mami ta kalleta, ta ce,
"Ya dai?"

*Najwa* ta kalle ta, ta ce,
"Mami na gaji ne."

"Sannu toh, In miki tambaya daya man."

Gyara zama *Najwa* tayi, ta ce,
"Ina ji Mami!"

Mami ta fuskan ci, *Najwa* ta ce,
"Dame ake kawar da Najasa?"

*Najwa* ta ce,
"Mami ana kawar da Najasa da *ruwa* me kyau, Ubangiji madaukakin sarki, ya ce,
"Lalai mun saukar muku da ruwa daga sama, mai tsarki."
Tsarki da ruwa shi ake kira da Istinja'a

Ana kawar da najasa Da *kasa,* dan kawar da abinda ya makale na najasa, na jikin tufafin mata, ko takalmi, ko taimama.
An karbo hadisi daga Humadatu, Allah kara mata yadda,  ta ce,
"Ni na tambayi Ummu salama, matar Annabi tsira da amincin Allah sukara tabbata a gareshi.  Ta ce,

"Ni na kasance mace mai dagayen tufafi, kuma ina tafiya ta wajen Najasa, Sai Ummu salama ta ce,
"Manzon Allah tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya ce, "Abinda yake bayan sa an tsarkake shi."
Abu dauda ya rawaito shi

Wannan yana nufin abinda ta tako na najasa in tabi ta kan kasa to kasar ta tsarkake shi.

Manzon Allah (SAW) ya ce, "idan dayan ku ya tako najaa a takalmin sa, hakika kasa mai tsarki ce a garshi."
Wato kasar ta tsarkake abinda ya kwaso.

NAJWA Complete ✔Donde viven las historias. Descúbrelo ahora