"Najib kana son ka hada ni da kawaye na ko?"

"Mami kiyi hakuri."
"Najib ka kiyaye ni, wallahi a cikin Nabila, Rahama da Rumanat ka fitar da daya dan na gaji, yara na binka kana wulakanta su."
Tayi maganar cikin fada.

"Mami yanzu dan Allah duk cikin, yaran da kika lissafo wace me irin tarbiyyar da nake so.
ita Nabila, ta saba da gata, ba kwaba ta sangarce! mami yarinyar da na ganta a Dubai da wani, Mami ita zaki min sha'awar aure, Yarinyar da bata da wani ilimin addini ta dauki boko ta daurawa kanta."

Shiru ya karayi,  ya cigaba da magana.
"Rahama kuma da kike magana akai, kinsan Rahma kinsa sam bata da kunya da tarbiya, in ba rashin kunya ma tayaya zasu ce suna sona dan Allah.
Kinsan duk dan sun ga iyayen su na da kudi shiyasa sam basu da tarbiya gani suke zasu iya taka kowa su zauna lafiya.
Duk da nasan suna shakkata, Mami tayaya zata kular min da ya'ya na har su samu irin tarbiyyar danake so.
Mami ba sharri ba wallahi har shaye shaye takeyi."

"Rumanat kuma dakike magana akanta, ita kuma kin dai san ta sarai, kinsan irin shigar da take, kullum cikin fitar da tsiraicin ta take, ga yawon tsiya ga kula kawayen banza. Ga rashin Tarbiyya har tace zata taba namijin da ba muharamin ta ba."

"Mami wadan nan duk tayaya zan so auren su, kinsan irin macen da nake son aure. Dama ace kyawu nake nema nasan dukka ukun zan hada.
To amman bashi nake nema ba inganci nake nema, ya'ya na nake ji. Manzon Allah yace, Mu auri mace dan kyanta, tarbiyyar ta, dukiyar ta, nasabar ta, ilimin ta.
Mami aciki wadan nan abubuwan, bazan taba iya auren macen da bata da tarbiyya ba, da wacce bata da ilimi ba.
Zan iya auren mace mara kyau, wacce bata da komai, wacce take a gidan marayu.
Amman bazan iya tunkarar mara ilimi da tarbiyya ba Mami."

"Ina kwadayin samun ya'yan da Annabi zeyi alfahari dasu ranar alkiyama. in kuwa ina son samun haka to Mami yana da kyau na nema musu uwa ta gari.
Mami dan Allah kiyi hakuri ki cigaba da taya ni da addu'a."

Kai Mami take jinjinawa tinda ya fara maganar tana kuma kara son yaron nata.

Itama tasan maganar sa gaskiya ce, dan ko ta kan danta ma izina ce, yadda kowa ke son sa da alfahari dashi.

Kowa nason mu'amala da Najib, kowa na saka masa albarka. Dole shima yayi wa ya'yan sa wannan kwadayin, bazai taba yi musu kwadayin zama abin zagi da kyama ba.

"Allah maka albarka, *Najib* lallai na dada yabawa da hankalin ka, kuma na yaba da tunanin ka. Allah baka mace ta gari."

"Ameen Mami nagode."
"Ba komai. Tashi kaje sai ka dawo."

"Toh!"
Ya fada yana mikewa, ya ce,

"Natafi."
"A dawo lafiya ka gaida Hajiya Nusaiba, ka dibar mata dankali, da doya.

Najib ya durkusa yana mata godiya.
"To Mami an gode "
Ya juya ya tafi.

Baba Tani ce ta fara magana. Ta ce,
"Gaskiya Hajiya ki godewa Allah da ya baki wannan yaron me hankali, ki kuma cigaba da masa addu'a dan yaron ki daban yake, kan a samu kamar sa za'a dade, abinda mazan yanzu ba ruwan su da tarbiyya ko ilimi, su kawai fara ko mayya ce, haka fa suke fada. amma sam wanna be rudarsa duk kyawun yaran nan. ki godewa Allah."

Murmushi Mami tayi jin an yabi yaron ta, ta ce,
"Wallahi Baba kullum cikin godewa Allah nake, dan alkairan Najib yawa su dashi, wani abun ma sai dai naji labari daga baya."

"To kinsan duk saboda me yaron ya kasan ce haka, saboda samun iyaye na gari da yayi, kinga kuwa shima ai dole ya kara kwadayin hakan."

"Haka ne Baba."
Daga nan suka shiga hirar su.



*INDABAWA**NAJWA*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻


NAJWA Complete ✔Where stories live. Discover now