PAGE__48

158 10 2
                                    

_Page 48_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

Kasancewar a chana mm zasu fara sauka idan sun ɗauki passengers kafin su wuce dubai bayan kwana biyu, suyo kwana uku acan suna jigilar kai da komowa a tsakanin ƙasashen sannan su sake dawowa china su ɗebi passenger ɗin da zasu dawo Nigeria dasu ya sa ya yanke shawarar kiran wani abokin sa dake zaune can wanda mafiya lokutta wajensa yake sauka idan yaje ƙasar mai suna Mu'azzam, haifaffen ɗan Nigeria ne a jahar Zamfara, aikine ya kaisa ƙasar a wani kamfanin ƙera motoci, sai kuma ALLAH ya nufi acan zaman nasa yake, bayan sun gaisa ya sanar mashi da cewa yau suna kan hanyar isowa ƙasar yana so ya sama masa ɗaki ɗaya a hotel da zai sauki su Momy acan kafin ranar da zasu koma, sosai abun ya bawa Mu'azzam mamaki daya ji mm ya ce wai ya kama masa ɗauki ɗaya a hotel don zaizo da mutane, murmushi kawai yayi ya amsa masa da to don yasan indai shine kaɗan daga cikin aikinsa kenan, a cewar sa baya son yana ɗora masa lalura shiyasa ko shi sai da yayi da gaske sannan ya amince ya riƙa sauka wajensa a maimakon hotel, don haka kawai ya ƙyalesa ya sa aka gyara ɗaki ɗaya daga cikin ɗakunan dake gidan, cike da farinciki da ya sanar da matar tasa mai suna shahida wacce ta kasan ce ƴar nan ƙasar China cewa mm ne ke tafi da baƙi ta shiga shisshirya masu abunda zasu ci kafin su ƙara so, don itama ba laifi tana da matuƙar son mutane sosai, anan ƙasar ya haɗu da ita wajen aikin sa, wasa wasa kuma suka fara soyayya kuma cikin ikon ALLAH har ta kaisu gayun aure, yanzu haka suna da yara biyu, Haisam da kuma Ƙaisah.

Suna isowa mm ya kirasa suka je suka ɗauki su daga airport shi da Shahida, basu wani jima ba da sauka ba suka isa inda cikin girmamawa Mu'azzam da Shahida suka shiga gaishe da mom, haka ma Razina ta gaishesu itama sannan suka yi masu iso wajen motar da suka zo da ita suka shiga Mu'azzam ya ja suka tafi, kai tsaye hanyar gida mm yaga ya nufa dasu a maimakon hotel kamar yanda yayi tsammani, juyowa ya yi ya kallesa fuskarsa ɗauke da alamun tambaya mu'azzam ya yi kamar bai ganesa ba, ita kuwa Razina tuni fira ta ɓarke tsakanin ta da Shahida kai kace sun saba da juna sai faman zuba idanuwa takeyi kan titi tana kallon gari duk inda suka wuce sai ta tambayeta ina ne ita kuma tana bata amsa cikin harshen turanci kamar yanda tayi mata don ba laifi takan fahimta kaɗan kaɗan, Hausar ce dai har yanzu bata zauna mata abaki daidai ba, ita kuwa Momy tunda suka gaisa bata sake cewa uffan ba saboda yanda jikinta yayi mata tiɓis saboda gajiya, juyowa mm yayi tare da kallon Razina ya ce,

"Ai fa, ba zama ɗan ƙauye ya zo birni, duk kin bi kin ishi mutane da surutu sai kace ke kaɗai acikin motar" dariya Shahida tayi don ta fahimci me yake cewa, sai da ta kalli yanda Razina ta ƙwaɓe fuska jin abunda ya faɗa sannan ta ce,

"Yeah is good, is good, allow her to talk, i like the way she's"

"Nooo..I don't want her to disturb you, she's very talkative"

"Rilly! Wow I like her" dariya Mu'azzam yayi haɗe da kallon sa ya ce,

"Kama fidda bakinka malan, in ba haka ba ka ji kunya don indai Shahida ce to an haɗu da an dace, itama ɗin gwana ce ta bugawa ga jarida wajen surutu"

"ALLAH?"

"Hmmm, ai yanzun nan ne zata baka kunya in kafiye zaƙewa tsakaninsu, shiyasa nake roƙon ALLAH yasa kar yaran nan idan sun girma su biyo ta da ɗan banzar surutu, musamman ma Haisam da babu ruwansa" dariya mm ya kwashe da ita ganin yanda Shahida ta kwaɓe fuska ta madubi tana ballawa Mu'azzam harara jin abunda ya faɗa haɗe da cewa,

"Tab..aikuwa kasan barewa baza tayi gudu ɗan ta yayi rarrafe ba, ai kaima ɗin ba abarka a baya ba indai wajen surutu ne"

"Inaaa...ai ko kaɗan ban kamo ƙafarta ba, parrot ma daya ganta sai da yayi saluting nata har kake wani haɗa ni da ita" ya ƙare zancen cikin zolaya yana ƙyarenta ta madubi haɗe da kashe mata ido, ɗauke kai tayi tayi kamar bata ganesa ba shi kuwa mm ya ce,

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now