PAGE_34

114 3 0
                                    

_Page 34_

*TUKUICIN SO💞*

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*
_____________________________
Bata wani jima ba a part ɗin Hajiya Zee don suna gaisawa ta wuce gida abunta ba tare da ta bari ko sallama sun sakeyi da Abba ba kasancewar har lokacin drivern ta na nan a haraba yana jiran fitowar ta, A ɓangaren mm kuwa sosai Momy taji daɗin yanda ya labarta mata cewa Hajiya ta karɓe sa hannu biyu tare da yimasa fatan ALLAH ya tabbatar da alkhairi, bayan kwana biyu da mm ya shirya ya je gidan grandma kamar yanda ta buƙata,

Tarba ta musamman Hajiya tayi masa inda tasa aka shirya masa abinci mai rai da kuma lafiya aka dama masu fura ta sha nono da madara aka saka masa fridge, lokacin da mm ya ƙara so gidan kai tsaye ta bawa baba mai gadi damar shigowa dashi har cikin falon nata, a lokacin tana zaune tana faman jan carbi, don bata jima da gama sallar walha data saba yi a koda yaushe ba, cikin girmamawa ya shigo ya zauna har ta kammala sannan ya ɗan rissinar da kansa ƙasa yana gaisheta, murmushi tayi sannan ta ce,

"Ashe dai mijin nawa da gaske yake yi, ai nazata ma ka manta da zancen gaba ɗaya"

"A'a Hajiya, ni dake neman farincikina taya zanyi in manta?"

"Lallai kam, da kayiwa kanka sakkiyar da ba ruwa, don kan waigoni lokacin daka tuna zaka tadda har na ba wani ita" cike da tsokana irin ta kaka da jika mm ya ce,

"Ai kuwa da kotu ta rabani dake da kuma kowaye kika bawa matata" dariya Hajiya tayi haɗe da ƙwalawa mai aikinta kira sannan ta ce,

"Ya iyayen naka? In jin dai duk lafiya suke?"

"Lafiya klw Hajiya, amma dukan su ALLAH yayi masu rasuwa"

"Ayya.. Sannu Muhammadu, ubangiji ALLAH ya rahamshe su"

"Amin" ya faɗa yana jin ɗacin rashin iyayen nasa a ƙasar zuciyar sa daidai lokacin,

"Rabi akawo masa abinci ko?" Hajiyar ta faɗa lokcin da mai aikin nata ta ƙara so cikin falon tana tsane hannunta da zanen dake jikin ta, bata ce komai ba ta juya ta je ta haɗo masa abincin a ƙaton tray ta kawo ta ajiye masa agabansa sannan ta juya ta bar falon,

"Muhammadu ga abinci nan ka taɓa da ƴan ruwa kafin na ɗan zaga, bari nazo?" ta faɗa tare da miƙewa ta nufi bedroom ɗin ta, gorar ruwan dake kan tray ya fara ɗaukowa da zimmar tsiyayawa yasha sai kawai yaga an miƙo hannu an karɓa, ɗago kan da zai yi suka haɗa idanuwa da Janan cikin wata doguwar riga brown colour mai haske data kusa sadewa da jikin ta, sosai tayi masa masifar kyau saboda sun kwana biyu basu haɗu ba sai dai waya, a hankali ya lumshe idanuwan sa kafin ya sake buɗe su akan kyakkyawar fuskarta yana faɗar,

"Subhanallahi khaliƙul azhim, fatabarakallahu ahsanil khaliƙin, nurul alb daga ina haka? Masha ALLAH gaskiya kinyi kyau sosai"

Janan na dariya tare da zuba masa ruwan a cup ta miƙa masa tana faɗin, "kai hubbin ruh, karfa ka fasa mun kai, duk kyan da nayi na kaika?" Saida ya kurɓi ruwan idanuwansa na akanta tana ƙoƙarin zuba masa abincin sannan ya ce,

"Ai kinma fini ranki shi daɗe, bar abincin nan kada ki zuba" kallonsa tayi cikin idanuwa haɗe da cewa,

"Girkin ne na Hajiya yau baza ka ci ba?"

"A ƙoshe nake shiyasa, musamman ma dana gaki sai naji na ƙara ƙoshi"

Wani ƙayataccen murmushi ta sakar masa haɗe da ajiye plate ɗin a gefe sannan ta rufe warmer ɗin cikin jin daɗin kalaman sa ta ce,

"To shikenan mijina, dama ina kishin kaci girkin ta ba nawa ba, ina kwana, ka tashi lafiya?"

"Lafiya klw matata, ya kike?"

"Alhamdulillah"

"Ya karatun?, Kar dai ince yauma tserowa kika yi?"

"Ai kuwa kamar ka sani" ta faɗa tana dariya tare da zaunawa akan kujerar dake kallon tasa, ɗaure fuska yayi tamkar ba shi ba haɗe da miƙewa tsaye yana faɗin,

"Indai akaina zaki fara guduwa wajen lectures bara na tafi abina"

"Nooo..mm wlh ba haka bane" ta faɗa kamar zatayi kuka, sallallamin da suka ji Hajiya na rafkawa da salati yasa mm komawa ya zauna tare da kafeta da idanuwa alamun zamu haɗu dake, sake marairaice fuska tayi haɗe da riƙo kunnuwanta alamun ban haƙuri ya kauda kansa ya maida inda Hajiya ke ƙoƙarin zaunawa tana faɗin,

"Yau naga barbaɗa ni hafsatu, ke kuwa daga ina waya gayyato ki kika zomun gida bagatatan ba zato ba tsammani? Ina Muhammadu nace ya dawo yau ina nemansa ba ke ba?" Saida Janan ta kalli mm dake murmushi sannan ta maida kallonta ga grandma tana turo baki haɗe da cewa,

"Yo tunda kika ce mijina ya dawo ai kamar kince nima na dawo, saboda duk inda kikaga wata dole zakiga Zarah awajen"

"Tofah, kuji fi'ili, to wace Zarah"

"Ga ni"

"To naji, yanzu dai tashi ki bamu waje zamuyi magana"

"To Hajiya, yanda duk kika ce, akwai fura?" Ta miƙe tare da nufar wajen fridge, tun kafin ta ƙara sa ta ce,

"Ke..ke..ke, dakata, jeki can kitchen ki tambayi rabi baza a rasa wata ba, wacce kenan ta Muhammadu ce"

"Kai Hajiya abun miji ai na mata ne ko hubbin ruh" ta ƙare zancen tare da buɗe fridge ɗin ta ɗauko furar tana kallon mm sannan ta kurɓa

"Kai, wannan haɗin furar na musamman ne Hajiya, gaskiya tare zamu sha dashi"

"Ai sai kiyi kwaɗayayyiyar banza, kawo masa nan ki ajiye kada na sake mantawa da ita" saida ta sake kurɓa kusan sau uku sannan ta rufe fridge ɗin ta zo ta kawo masa furar ta ajiye a gabansa sannan ta wuce can cikin gida inda rabi take, shi kuwa binta yayi da kallo tamkar zai haɗiye ta saboda yanda duk wani motsi nata ke sake tafiya da hankalin sa,

Ƴar gyaran murya Hajiya tayi kafin takira sunan sa itama idanuwanta na akansa, cike da jin kunya ya shiga sosai kansa haɗe da amsa mata da, "Na'am Hajiya"

"Ina so kayi haƙuri da tambayoyin da zanyi maka kuma kabani amsa tsakani da ALLAH, zanyi maka su ne saboda nasan yanda zan ɓullo wa lamarin mahaifin Janan bawai don na wulaƙanta kaba ko kuma wani abun, ko ɗaya bana nufin hakan"

"Hajiya kada ki damu da duk wata tambaya da kike son yimun domin ko musulunci ya yadda da ayi bincike acikin sha'anin aure, kuma in Sha ALLAH zaki sameni mai faɗar gaskiya ga duka amsoshin tambayoyin ki"

"Masha ALLAH, Nagode daka fahimceni" saida ta ɗan yi shiru sannan taci gaba da cewa "Muhammadu, ɗazu na tambayeka akan ya iyayen ka suke, sai kake shedamun cewa ALLAH yayi masu rasuwa, abun tambaya anan, dama can ku ƴan asalin wannan gari ne ko kuwa?, Ya sunan mahaifinka?, Meye sana'ar ka?, A ina kake zaune yanzu?, Wu ɗan nan sune kaɗai abunda nake son ji dangane dakai, daga su kuma babu wani abu da zan sake buƙatar sani akanka, suma ɗin na tambayeka ne saboda mahaifin Janan kamar yanda na faɗa maka tun farko, da kuma wata matsala da nake gudun sake faruwar makamanciyar ta acikin zuri'a ta, ina fatar kuma hakan bazai zame maka damuwa ba?"

"In sha ALLAH Hajiya, farko dai sunana, Muhammad Muhriz, sunan mahaifina kuma Muhammad, iyayena ƴan asalin jahar nan ne, amma a ƙauyen caranci suke da zama su da mafiya yawan ƴan uwansu, noma da kuma kasuwanci sune sana'ar mahaifina kafin ALLAH yayi masa rasuwa a sanadiyar ɓarayi da suka afka ma ƙauyen namu, an haifeni a can kuma acan nafaro rayuwata ni da ƙanwata mai suna Razina, mutuwar mahaifina da mahaifiyata su suka zamo silar gudowar mu ni da ƙanwata muka dawo wannan garin da zama...." Nan yaci gaba da labartawa grandma ma yanda rayuwarsu ta kasance bayan zuwan su a wannan garin har zuwa yanzu daya mallaki hankalin sa ba tare daya ɓoye mata komai ba.

*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU*👏😭

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now