PAGE__27

131 5 0
                                    

_Page 27_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*

_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1241594347?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=LbkNSq93a4%2FqKT7WcAgw5buJKslmsQs%2BObyPK9nk7oD1l4ae0Ap8C57ICn7cM%2Bcb%2FiG%2BweTpcB3pnFsfC%2F6cAusT73w9cfjc%2Fm7Zya%2FTY71iAdNas6BsOrbLsU0SF0bv_
______________________________
Da sauri Razina dake tsaye tana kallonsa ta ƙaraso wajen tana faɗin,

"Ya mm lafiya?" Ta tambayesa Fuskarta ɗauke da damuwa ganin halin da yake ciki, ɗago kai yayi a hankali shima yana kallonta kafin yayi wani irin ajiyar zuciya haɗe da cewa, "lafiya klw Razina, ya akayi ne?" Sanin da tayi ba lalle ne ko ta matsa masa ya faɗa mata abunda ke samun sa ba yasa itama ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa,

"Kazo inji Momy tana neman ka"

"Ok, he kice gani nan zuwa" ya ƙare zancen haɗe da miƙewa ya shige bedroom ɗin nasu ita kuma ta fita, tana kawowa bakin ƙofa ta hango Jabir na shigowa daga wajen gate, murmushi tayi tana ƙare masa kallo kafin ta nufi wajensa tana wasa da hannayenta tamkar yanda yara keyi, ledar hannunsa daya shigo da ita tamiƙa hannu ta karɓa tana faɗin,

"Oyoyo yaya na sannu da zuwa"

Ƙara faɗaɗa murmushin dake kwance kan fuskarsa yayi haɗe da cewa,

"Yawwa matar, ya kike?"

"Cike da tarin kewarka na wuni, amma ganinka a yanzu yasani tsintar kaina cikin tarin farinciki da kuma kwanciyar hankali" ta ƙare maganar tana tsaresa da wani sihirtaccen kallo haɗe da langaɓar dakai gefe, wani lumshe idanuwa yayi cike da tsokana ya dafe saiti zuciyar sa yana faɗin,

"Wash.." haɗe da ƙoƙarin duƙewa ƙasa, da sauri ta miƙa hannayen ta tana ƙoƙarin riƙosa tare da cewa, "Subhanallahi, hubby lafiya?"

"A a wifey, Ina fa lafiya, don ALLAH yaushe ne auren mu masoyiyata?" Murmushi ta saki tare da miƙewa tsaye cike dajin kunya ta ce,

"Nima kai nake saurare hubby, duk sadda ka tashi a shirye nike nima"

"Yanzu pls" ya faɗa yana marairaice mata murya, zaro idanuwa tayi tana kallon sa kafin tace,

"Hubby yanzu kuma?"

"Eh wifey, Baki ga irin kallon da kikeyi mun bane? Matuƙar zaki ci gaba da yimani irinsa to tabbas bugun numfashi na zai iya tsayawa, musamman idan bakya kusa dani kamar haka" ya ƙare zancen cike da zolaya yana ƙoƙarin aza kansa a saman kafaɗar ta, da sauri ta goce tana turo baki kafin tace "kai ko?" Yanda tayi shima ɗin yayi hadda su maka mata harara, ai kuwa ta dagargaje zata maka masa ledar dake hannunta data karɓa a hannunsa da yake ɗunkunan ta na hijabs ne daya karɓo mata aciki da gudu yabar wajen yana dariya itama ta bisa baya tana dariyar haɗe da cewa, "ALLAH daka tsaya saina maka maka ita a saman ƙaton kannan naka mai kama da nawa"

"Ni ɗin?"

"Eh mana, to meyasa zaka kwaikwaye ni?" ta ƙare maganar tare da maka masa harara, daidai lokacin mm yazo wuce zuwa part ɗin na Momy, ya girgiza kai ganin Jabir ya riƙe kunnuwan sa yana faɗin, "An sorry wifey, never repeat that" har yana ƙoƙarin yin up and down, tsaki ya ja tare da sake girgiza kai akaro na biyu yana kallon Jabir haɗe da cewa,

"Girma ya faɗi, wai yaya ke yiwa ƙanwar sa up and down sekace wasu yara"

"Na dai ji, in hitsari banza ne kaza tayi mugani, malam wannan shi ake kira da salon so in baka sani ba ko wifey?"

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now