PAGE__23

130 4 0
                                    

_Page 23_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*

*GA MASU BUƘATAR A TALLATA MASU HAJOJINSU, KO KUMA SABABBIN LITTAFANSU DA SUKE SON FIDDAWA ZASU IYA TUNTUƁAR WANNAN LAMBAR KAI TSAYE TA HANYAR WATSAPP 07040402435*
______________________________
Murmushi Jabir yayi haɗe da cewa "yo ai dole na kalleka malam, wannan tsattsauran gargaɗi da kake yiwa 'yar mutane sai kace wadda ta ce zatayi wuf dakai ai yayi yawa, ina laifin wanda yace yana sonka?"

"Ai kuwa ka yi a kunnen Janan, don tun yanzu dole tasan irin zaman da za tayi dakai"

"Ka ga mr.luv!, Rufani ka saya ni a hannun Janan kar mutuncin da nake dashi a hannunta ya tuɗe"

"Ya dai fimaka malam, anan fadar babu mai faɗa naji inba ita ba"

"Eh, ai na tabbata hakan"

Jabir ya faɗa tare da miƙewa yabar ɗakin, shi kuwa yaci gaba da latsar system ɗin zuciyarsa cike taf da tunanin Janan,

A ta ɗaya ɓangaren kuwa jifa Amira dake kwance akan gadon asibiti tayi da wayar ta haɗe da fashewa da kuka tana faɗin,

"Na tsaneki Janan, wlh na tsaneki irin tsanar da ban taɓa yiwa wani mahaluƙi ba aduniya, shin me kika fini dashi ne da mm zai so ki kuma ya amshi soyayyarki fiye da yawa?"

Mahaifiyarta ce dake shigowa riƙe da buta lokacin tayi saurin ƙarasowa wajenta ganin tana kuka tare da riƙo hannunta tana faɗin,

"Amira lafiya?, Me kuma ya faru dake?"

"Umma baya sona, ya tsaneni" ta faɗa cikin kuka haɗe da ɗora kanta sama cinyar mahaifiyar tata data zauna kan gadon kusa da ita, ajiyar zuciya umman tata ta sauke tare da juyar da kanta tana kallon wayar ta data jefar ƙasa, "innalillahi wa inna ilaihirrajiun, ashe Amira ban isa in faɗa maki ki ɗauka ba? Bana faɗa maki cewa ki fita sabgar Yaron nan ba tunda da bakinki kika faɗamun cewa akwai wacce yake so take son da ba?"

"Umma na kasa jurewa ne wlh, kullum safiya sai ƙara son sa nakeyi"

"To tunda shi bai ma san kina yi ba don me da bazaki haƙura ba"

"Umma ya sani wlh, ya sani yanzu na faɗa masa"

"Da kanki?" Umman ta tambayeta tana zaro idanuwa cike da mamaki,

"Eh Umma, shine wai yace na haƙura akwai wacce yake so shi, kuma nasan ba kowa bace face Janan"

"Ikon ALLAH, to tunda har kinsan da hakan to ki haƙura mana"

"Wlh bazan iya haƙura dashi ba umma, ta fasan ni nafara son sa, amma ta je ta munafucceni suka ƙulla soyayya dashi, wlh ko zan mutu bazan bar mata shi ba, sai dai dani da ita kowa ya rasa"

Sallallami ummanta ta saka tare da ture kanta dake saman cinyar ta tana faɗin,

"Anya Amira lafiyar ki ƙalau kuwa? Kar fa kije ki jawowa kanki fitinar da tafi ƙarfin ki, Janan ba sa'ar yinki ba ce, daga ni har ke kin san dadyn ta zai iya sakawa a ɓatar damu idan kikayi yunƙurin aikata wani abu ba daidai ba, shin ana so dole ne? Kuma ita meye laifinta da zaki ɗauki karan tsana akan ɗa namiji ki ɗora mata"

"Ba a yi umma, amma badon ta shiga rayuwar sa ba wlh bazai taɓa rejecting soyayya ta ba, kin kuwa ga ita ce mai laifin"

"To tunda an riga da an gama ai sai ki haƙura, ubangiji kema ALLAH ya fiddo maki da wanda ya fishi"

"Umma ki dena yimun irin wannan addu'ar, wlh nasan babu namijin da yafi mm a wannan zamanin, kawai dai ki roƙamun ALLAH ya bani shi kuma yasa ya soni ko baya so"

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now