PAGE__14

161 6 0
                                    

_Page 14_

*TUKUICIN SO*

*NA*

*BILLY S FARI*

*FREE BOOK*

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*

INA KUKE MAKARANTA??

INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️

TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B

INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.

DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA

(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_

👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730
______________________________
Janan kuwa ko data koma class ta tadda har an kusa ƙare lectures ɗin da aka shiga bada ita ba, bata fi mintuna goma da shiga ba malamin ya fice, juyawa tayi wajen Amira tare da miƙa mata hannu ma'ana ta bata sauƙin ta data karɓo mata wajen mm,

Wata baƙar leda Amira ta ɗauko dake gefenta ajiye tare da ɗari biyar ta miƙa mata tana faɗin,

"Ina kika shige tun ɗazu?"

Bata ce mata komai ba ta amshi ledar tana kallon tarin dabino da kwakwar dake ciki, shi kansa dabinon kaɗai yakai yawan gwango huɗu, kwakwa kuma ƙwallo biyu, ga kuma ɗari biyar ɗin data bashi ya dawo mata da ita, kallon Amira tayi cike da mamaki ta ce,

"Ya naga haka Amira? Kema kin ƙara siya ne aka haɗe mana ne?"

"Kamar ya? Ni dai haka ya bani yace in kawo maki, halama bana daidai kuɗin ki ba ne?"

Har zata ce wani abu sai kuma tayi shiru tunda tasan anjima zasu haɗu, sai ta tambayesa dalilin da yasa zai kwashe kayansa haka ya bata kuma yaƙi karɓar kuɗi, 'yar ajiyar zuciya ta sauke haɗe da kallonta ta ce,

"A'a ba haka bane, am just asking"

"Yawwa, amma kin san wani abu?"

"A'a sai kin faɗa" ta ƙare zancen tana jefa dabinon data kwanɗara a baki,

"Hmmm..Wannan Jabir ɗin na tare dashi baya da mutunci wlh, wai kamar ni zai kalla ya ciwa mutunci a gaban mutane hadda faɗin na jaye na ba mutane waje na je na tsare su da idanuwa kamar na mujiya, wai idan ban tashi yin abunda ya kawo ni ba to naje naba customer ɗin su waje! Kin ga kuwa yanda ya yarfa ni wajen aka dinga yimun dariya?, wlh ALLAH ba don mm ba da sai na tata masa rashin mutunci daidai na kuɗinsa talakan banza talakan wofi"

"To fah!, Iko sai ALLAH, shi talaka bai da ikon yin magana idan aka yimasa ba daidai ba?, Ashe duk ƙarya ce ranar kike yi da kika dinga masifa akan na kaɗe mm nazo nayi zamana a class don bansan darajar ɗan adam ba, yanzu ke wace daraja kika nunawa ɗan adam da kika kirasa da talakan banza talakan wofi?"

"Hmmm Janan kenan, ai bazaki gane irin renin hankalin da gayen nan yayi mun ba ne"

"Naji, bai kyauta ba amma ai wataƙil gaskiya ya faɗa, don in har bakiyi ba bazai ce kinyi ba"

"Ok, kina goyon bayan sa kenan?"

"A'a, ina dai goyon bayan gaskiya ne, akwai cutarwa ka ai bata mutum da yanayin da ALLAH ya jarabce sa da zama ciki, talauci ba shi ya zaɓawa kansa zama cikin sa ba, balle ki goranta masa"

Dariya ta kwashe da ita kafin tace,

"To Malama Janan naji!, irin wannan haƙiƙan cewa da kike yi hakan, kodai kodai?"

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now