PAGE__37

118 2 0
                                    

_Page 37_

*TUKUICIN SO💞*

*NA*

*BILLY S FARI💎*

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*
______________________________
Janan kuwa ko data isa gida anyi sallar magrib, don haka bata tsaya bi takan kowa ba tawuce ɗakinta kai tsaye, jikkar ta tafara ajiyewa kan gado sannan ta faɗa toilet tayo arwala, tana fitowa ta tada sallah, bayan ta kammala tayi azkar ɗin marece sannan ta jawo alƙur'anin ta dake kan bedside ta shiga karantawa, bata kammala ba sai da taji ankira sallar isha sannan ta rufe ƙur'anin ta tashi ta kabbarta sallah, tana gamawa ta tuɓe kayan jikinta ta faɗa toilet tayo wanka, fitowarta keda wuya wayarta ta hau ruri, murmushi tayi saboda ringing ɗin da tayi mutum ɗaya ne dashi wato masoyinta mm, bata tsaya wani saka kaya ba ta ɗauki wayar tare da ɗaya kiran daya shigo a karo na biyu ta kara akunnuwa,

"Ran yallaɓiyata ya daɗe" mm ya faɗa yana duba wasu takardu daya je ɗaukowa cikin mota, saida ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce,

"Tare dakai yallaɓai, ina wuni?"

"Lafiya klw, ya kike?"

"Alhamdulillah, kai fa?"

"Nima hakan, in jin ɗazu kin samu lecture ɗin?"

"Sosai ma kuwa, ko ka manta kayimun addu'a?"

"Ehmm, kinci abinci?"

"A'a hubby" ɗan zaro idanuwa yayi daidai lokacin daya ciro wani file daga cikin mota yana ƙoƙarin rufe marfinta,

"Me yasa?, So kikeyi yunwa ta kama mani ke ne?, Kin san na faɗa maki cewa dena wasa dacin abinci akan lokaci ko?"

"Kayi haƙuri, ban jima da dawowa ba, sai na tsaya gabatar da salloli, amma yanzun nan zan sauka naci in sha ALLAH"

"Okay shikenan, amma ina kika tsaya ne haka da har kika jima awaje baki dawo gida ba?"

"Naje gidan su Amira dubata ne?"

"What...?" Ya faɗa da ƙarfi har wayar ta suɓuce a hannun ta, cikin mamaki ya ci gaba da cewa,

"Janan kin kuwa san ko waye Amira?, Kin san yanda ita ta ɗauki tarenku kuwa?"

"Na sani mm"

"Noo..baki sani ba, idan kuma har kin sani to wani ɓangaren kika sani ba duka ba"

"Hmm, hubbin ruh kenan! Nasan kaso tis'in da tara bisa ɗari na daga cikin halayen Amira, na kuma san yanda na ɗauke ta ba haka ta ɗauke ni ba, amma ni har ga ALLAH ƙaunar ta nakeyi da zuciya ɗaya, ban taɓa jin abubuwan da take yimun ba zasu iya sa na sauya mata duk da ita ɗin ta sauya mun sosai ba kamar yanda muke ada ba, na kuma ɗauki wannan a matsayin ajizancin ɗan adam da ake cewa ɗan tara ne bai cika goma ba"

"Tirƙashi! Lallai zuciyarki mai kyau ce Janan, amma duk da haka kiyi takatsantsan da ita, ba ina nufin ki rabu da ita ba, amma ki kula dakyau a taren ku, kin san halin rayuwa da kuma halin ɗan adam"

"To shikenan yallaɓai zanyi hakan, ya Momy da Razina?"

"Duk suna nan lafiya klw, ina da kyakkyawan albishir agareki"

"Wow! Are you serious?"

"Sosai kuwa, amma kafin nan ki fara sauka kici abincin, anjima sai muci gaba da maganar mu ko?"

"No hubby bari na saka kayana na suka naci abincin, go ahead ina saurarenka" ta ƙare zancen haɗe da miƙewa ta nufi wardrobe ɗin kayanta ta ciro wando iya guiwa da ves mai faɗitn hannu ta saka saboda yana yin garin da zafi da alama hadari ne ke haɗuwa, sannan ta ciro mayafi ɗan siriri ta ɗora akan ta tafice daga ɗakin tana faɗin,

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now