PAGE__35

129 3 0
                                    

_Page 35_

*TUKUICIN SO💞*

*NA*

*BILLY S FARI💎*

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*
______________________________
Sosai grandma ma ta tausayawa irin halin rayuwar da mm suka tsinci kansu lokacin da suka rasa iyayen su duk data wani ɓangaren ta jinjinawa matar data riƙe su sosai, don ba kowa yake da wannan zuciyar ba yanzu, a hankali tayi ajiyar zuciya haɗe da kallon mm da idanuwansa sukayi jajir saboda ɗacin da yaji na tunawa da irin kisan wulaƙancin da aka yiwa iyayensa a gabansa, ji yake gaba ɗaya komai ya koma masa sabo tamkar yanzu abun ya faru, cikin tausayawa ta ce,

"Kayi haƙuri Muhammadu, dukkanin mai rai mamaci ne, su kuma wuɗan nan bayin ALLAH dake faman zalintar mutane suna rabasu da rayuwar su da duniyoyin su ALLAH ka shiryesu in masu rabon shiryuwa ne in kuma basu da rabon shiryuwa ALLAH kayi mana maganin su"

"Amin Hajiya" ya bata amsa yana ƙoƙarin danne abunda yake ji na taso masa a zuciya,

"To, duk da dai na ce bazan sake yimaka wata tambayar ba, zan so in san ko wace baiwar ALLAH ce wannan data taimaki rayuwar ku haka, sannan kamar yanda ka ce ɗazun ka kammala karatu yanzu haka kana aiki, to meya kaika makarantar su Janan har kuka haɗu, kuma meyasa baka sake waiwayar ƙauyen ku ba ko ALLAH zai sa ka riski wasu daga cikin ƴan uwan mahaifinka ko na mahaifiyar ka?"

"To Hajiya bari nafara amsa maki tambayar ki ta biyu, dalilin ɗaya kaini makarantar su Janan shine neman wani abu da nakeyi don kaucewa abinda zai jawo damuwa cikin rayuwar mu ni da ƴan uwana sai nake sana'ar dabino saboda na samu na cimma nasara akan wannan abun, sai kuma zancen rashin komawata ƙauye mu, a gaskiya ƙwaƙwalwa ta bata taɓa kawomun wannan tunanin ba saboda ganin agabana aka kashe iyayenmu gaba ɗaya, sai nake ganin idan ma na koma hakan bazai amfane mu ba tunda koda muka baro ƙauye gaba ɗaya ya watse, babban dalilina kuma shine babu abunda muka nema muka rasa awajen baiwar ALLAHr da muke tare da ita, sai wannan tunanin bai zo mun a ƙwaƙwalwa ba gaba ɗaya, Momy wata irin uwace da tsayuwar ta agaremu ya kauda dukkanin rashin jigo na rayuwa, macece mai matuƙar karamci da haƙuri, imanin ta da kuma yaƙinin ta akan ALLAH ke ƙaddarta komai na rayuwa yasa bata da baƙinciki da kuma ƙyashin taimakon kowa, ta riƙemu irin riƙon data yiwa ɗan ta ƙwaya ɗaya tilo duk dako mahaifinsa baya raye ba tare da tayi duba da irin rashin karamci da kulawar da ita akayi mata da ɗan ta ba, fatana shine ALLAH ya faranta zuciyarta kuma ya yar mata damuwar fili data bayyane" cike da damuwa Hajiya da idanuwanta suka fara cika taf da ƙwalla tunawa da abunda suka yiwa matar ɗanta da jikan ta saboda son zuciya ta ce,

"Amin ya ALLAH Muhammadu, duk inda ake karamci wannan baiwar ALLAH tayi maku kuma ubangiji kaɗai ne zai iya biyan ta wannan taimako data yi ba tare da dubi rashin alaƙar dake tsakanin ku da ita ba, abun da mu muka kasa yiwa matar ɗan mu da yaron ta saboda kawai banbancin yare da addini duk dako ɗan mu ya musuluntar da ita, amma..." Sai kuma ta kasa ƙara sawa saboda kukan da yaci ƙarfin ta, abune wanda ya daɗi yana ci mata zuciya ta rasa wanda zata faɗawa taji sanyi, sai gashi sanadiyar labarinsa yau tafara fitar dashi, kuka takeyi sosai cike da nadamar abunda ya faru ba tare daya hanata ba har sai da tayi mai isarta tayi shiru don kanta, gyaran murya yayi haɗe da gyara zamansa kafin yace,

"Kamar dai yanda akoda yaushe Momy ke faɗa, ko wane abu na tafiya ne bisa tsarin ƙundin ƙaddarar rayuwar da ALLAH ya tsarowa bawa, taimako abune mai kyau ga duk wanda ALLAH ya bawa ikon yi, ba sai ga wanda ka sani ba hatta wanda baka sani ba zaka iya yi masa, ALLAH ya tsaro hakan zata faru, don haka haƙuri ya kamata kiyi Hajiya sai kuma atuba a nemi hanyar gyara kuskuren da aka aikata"

"Muhammadu tuni na tubarwa ALLAH akan wannan kuskure da muka aikata, sai dai taya zan gyara bayan na yakuce su daga jikina da kuma ahalina, inda nake tsammanin zan samesu na kasa samun su awajen, su kuma gaba ɗaya sunyi fushin zuciya sun kasa dawowa garemu, kuma na tabbata ba kowa ya jawo hakan ba sai Usman" hajiya takai zancen tare da sake fashewa da wani kukan, sosai mm yaso bayyana mata cewa yana tare dasu ganin irin tarin nadamar da tayi acikin idanuwan ta, amma sai yabar hakan a zuciyar sa har sai zuwa nan gaba sai yayi mata bazata, baki ya shiga bata tare da addu'ar ALLAH ya bayyana su, ya kuma bata shawara akan tafi gaba da addu'a in Sha ALLAH nan kusa bada jimawa ba zasu dawo gareta, kuma hakan ya matuƙar kwantar mata da hankali sosai, inda ta sake jin ya shigar mata rai fiye da tunani, ɗago kanta tayi tana kallonsa haɗe da cewa,

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now