PAGE__44

195 8 1
                                    

_Page 44_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

Kasancewar yau saura kwana ɗaya mm yaje ƙauyensu ya sa da marece ya ce Momy da Razina su shirya ya suje gidan grandma gaisheta daga nan suga juna ita da Hajiya, ya so su haɗu da Janan amma a yanayin yanda zasuyi tafiyar bai kamata ace ya haɗu da ita ba, hakan yasa da sukayi waya da ita ya ce tabari zai zo nan gida da daddare suyi bankwana saboda gobe sakko yake so yayi, bata so hakan ba don taso su haɗu gidan grandma susha firarsu, cikin shagwaɓe murya ta ce,

"Amma dai kasan idan kazo nan gida ba wani jimawa zamuyi ba kasan Abba na gari"

"Na sani mana, me kike tsoron ya faru don Abba na a gari"

"Abubuwa da dama gaskiya saboda bana son duk wani abu da zai cutar mani dakai, musamman lafiyarka domin itace tawa"

"Shikenan, kisa aranki in sha ALLAH babu abunda zai faru"

"I wish so" ta faɗa muryarta na nuna alamun ba hakan taso ba, murmushi yayi haɗe da cewa,

"Come on, trust me kinji ko"

"To shikenan sai kazo"

"Good beb, smile make i hear" ta saki wani irin ƙayataccen murmushi da sai da sautin sa ya dakar masa kunne tare dasa hannu ta kulle fuskarta tamkar tana a gabansa, dariya yayi sannan ya ce,

"Ko kefa, sai nazo"

"Bye, ALLAH yakawo ka lafiya"

"Amin" ya faɗa haɗe da kashe wayar, daidai lokacin Momy tafito saye da hijab ɗin ta har ƙasa Razina na biye da ita a baya riƙe da leda a hannun ta,

"Momy kun fito?"

"Eh my son, Ina mutumen naka?, Ko bada shi za a je ba?"

"Ya ma isa, yana waje yana karɓa waya"

"To muje naga ankusa magrib"

Saida ta wuce gaba sannan ya miƙe tabi bayanta haɗe da kallon ledar dake hannun Razina ya ce,

"Meye wannan?"

"Sauƙin Momy ne aciki wai zata kaiwa Hajiya"

"Au! Wai me?, Ko kishi kikeyi da ita kema" ya ɗaya makullin motar dake hannunsa karamar zai doka mata akai tayi saurin janyewa tana dariya,

"Ya mm to meye laifina ma idan nayi, ai Auntynah ta koya mun" murmushi kawai yayi don yasan Jabir ya faɗa mata abunda ya faru ranar, ba tare daya sake cewa komai ba ya wuce gaba abunsa tana biye dashi tana dariya ƙasa ƙasa har suka ƙaraso bakin motar ya buɗe ya shiga ya tayar, Jabir da har lokacin bai gama wayar da yakeyi ba ya yiwa horn alamun shi suke jira, yana juyowa suka haɗa idanuwa da Razina dake ƙoƙarin shiga motar ta dalla masa harara sannan ta shige abunta, ƴar dariya ya yi ganin kishin namu na mata ya motsa mata ganin yana waya haɗe da shafo sideburn ɗinsa sannan ya yi sallama da wanda suke wayar ya kashe,

Har ya shigo motar ko kallonsa bata koma yi ba duk da juyowar da ya yi yana kallon ta haɗe da cewa,

"Sorry Madam na tsaidaku ko? Na ga sai harara ake aikamun da ita, afuwan"

"Oh, kodai ma meye kaika sani kar ka shawa yarinyata kai da surutu" Momy ta faɗa tana kallon Razina da fuskarta kecan gefe tana kallon waje ta cikin glass ɗin tagar motar, murmushi tayi haɗe da sinne kai ƙasa wanda hakan ya sa shima ya yi murmushin tare da maido fuskarsa a gaba yana faɗin,

"Ka kira Janan kuwa"

"Eh, amma bana so muhaɗu shiyasa na faɗa mata cewa zan zo anjima da daddare acan gidan baffan muyi sallama da ita"

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now