PAGE__26

168 11 9
                                    

_Page 26_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*

_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1240398682?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=XUf6U0thucbnMvAx5O3LULkyGkS9C6P%2FVbtkcwUSZ9AIv7qPeMLJaS6zFzWaOqqGn4tZ4PqIhL7Qt%2BXGPCVqEIBULj3t%2BmspEw5zvGuhe0jYJ%2F5E%2ByXStQLSvK6f6GNc_
______________________________
Kallonta yayi irin kallon nan na da gaske kike yi kafin yace "Janan, da gaske kike yi ni ne damuwar ki?" Ta jinjina mashi kai tana share hawayen da suka miƙa mata fuska da bayan hannu haɗe da cewa.

"Yes upcouse kai ne"

"Ok come, let talk between me and you now, idan wani matsala ne sai muyi solving ɗin ta tun yanzu" ya ƙare maganar tare da miƙo mata hannu, hannun ta kalla haɗe da banka masa harara sannan ta kauda kai gefe tana folding hannayenta akan ƙirji, ganin haka yasa ya fahimci me take nufi don haka kawai sai ya nuna mata hanya tare da wucewa gaba suka nufi can gefen da babu mutane sosai,

Saida ya sauke ajiyar zuciya bayan ya naɗa hannayensa shima ya ɗora akan ƙirjin sannan ya ce,

"Now tell me, meye na miki da har ya sakaki kuka ko nace ya haifar maki da damuwa?" Cikin natsuwa da tauna duk wata magana da zata furta ta ce,

"Am sorry yaya asgar for what am going to tell you, sincerely ni ina da wanda ke sona kuma nima nake son sa, shiyasa yanzu da mahaifina ke sanar mun cewa kai ne wanda ya zaɓamun na aura na shiga damuwa da tashin hankali, saboda bansan yanda zan iya rayuwa da wani namijin da bashi ba, amma kayi haƙuri bawai don bana so ka ba, ko ba komai ni dakai duka 'yan uwane kaga kuwa bazan ƙika ba, matsalar kawai shine nariga dana bawa wancan gaba ɗaya ragamar rayuwata" ba tare da ya damu da girman kalaman da suka fito abakin ta ba ya ce,

"And so what Janan, Ina dai bakya ƙi na tunda har kika ce mun zama 'yan uwa, and i know ɗan uwa bazai ƙi ɗan uwansa ba ko?, Don haka ni ban damu da kina son wani a zuciyar ki ba, haka nake son ki kuma zan iya auren ki a haka, with time nasan nima zuciyar ki zata koyi sona a hankali, zancen kuma wai wani na son ki, left to him, ya rage nasa ya haƙura dake ya hutawa kansa, idan kuma yaƙi shima ya rage nasa don shine da rashi bani ba, ina fatar kin fahimta kuma zaki janye wannan damuwar a ranki don kada tahana mana farinciki da walwala"

Kusan mutuwar tsaye Janan tayi jin kalaman dake fitowa daga bakin asgar, cikin ɓacin rai take ƙare masa kallo haɗe da cewa,

"Kada ka yaudari kanka yaya asgar domin zuciyata yare ɗaya take ji kuma take fahimta, a shawarce zaifi kyau ka tattara inaka inaka ka koma inda ka fito kuma ka shedawa iyayen mu cewa ni bana son ka, don haka su nema maka wacce ta dace dakai kuma daidai kai" Tana gama faɗar haka ta juya tabar wajen ranta a ɓace, saurin shan gaban ta yayi tare da haɗe hannayen sa waje ɗaya idanuwan sa a kanta ya ce,

"Pls Janan, ki tsaya mu fahimci juna, wlh komai zai faru bazan iya haƙura dake ba don haka ƙara ma ki tsaya mu walwale wannan damuwar da kanmu" wani irin kallon banza ta watsa masa haɗe dayin tsaki ta raɓa ta gefensa zata wuce kawai ta ji ya kamo hannunta ya maido da ita a gabansa, buɗar bakinsa keda wuya da zimmar yi mata magana yaji ta ɗauke sa mari,

"How dare you zaka riƙamun hannu? Ka ɗauka ni irin 'yan matan ƙasar ka ne da
suka saba zubarwa da kansu mutunci a wajenki, wannan shine banbancin dake tsakanin ka da zaɓin dana yiwa kaina da kuma kai da ake ƙoƙarin zaɓamun, a zahiri ma sam bamu dace ba" tana rufe baki itama taji saukar mari a fuskarta, kafin tace wani abun ta sake ji an ɗauketa da wani marin, mahaifin tane ta gani a tsaye cikin ɓacin rai ya sauke mata waɗan nan maroran da suka kusa gigita mata ƙwaƙwalwa, wani irin kuma ta fashe dashi tare da juyawa tabar wajen aguje, cikin ɗaga murya ya ce,

TUKUICIN SODonde viven las historias. Descúbrelo ahora