PAGE__18

170 6 2
                                    

_Page 18_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*

*KIN SAYI SHIRINMU NA TOP TEN, TAKUN HASKE BATCH B?, IDAN BAKI SAYA BA MAZA KI HANZARTA KI MALLAKI NAKI TA HANYAR WUƊANNAN LAMBOBIN DOMIN SAMUN ƘARIN BAYANI
+447894142004, 07065283730, LITTAFAI BAKWAI DA SHIRE-SHIRE HAR GUDA UKU MASU MATUƘAR ƘAYATARWA AKAN NAIRA DUBU ƊAYA (1000) KACAL, ƳAR UWA GWADA KI GANI IDAN KINA CIKIN WUƊAN DA SUKAYI RASHIN BATCH A ƊIN MU, NA TABBATA BAZA KIYI NADAMA BA😍*
______________________________
Da sauri gaba ɗaya suka juya tun daga mm ɗin, Janan har zuwa Jabir dake sallamar wasu 'yan mata da suka zo siya dabino, cike da mamaki suke kallon gefen da bishiyar take tare da hango mutum a jikin ta duƙe, Jabir ne ya fara isa wajen kafin ƴan matan su rufa masa baya sannan Janan da mm suma suka bi bayan su, duƙe take ta saka kanta cikin cinyoyin ta tana darzar kuka, kan kace me tuni taron ɗalibai ya lulluɓe wajen, Jabir ne yayi ƙarfin halin matsawa kusa da ita don duk an zata aljanune ke damun ko wace a wurin jin yanda take gunki,

"Ke baiwar ALLAH lafiya?" Jabir ya faɗa yana ƙoƙarin matsawa kusa da ita, jin ba muryar wanda take tunani bace ya sa tayi banza dashi ba tare da ta ce ƙanzil ba balle har a sa ran zata ɗago tayi magana, Janan ce ta ƙara so wajen kasancewar sai yanzu ne ta tuna cewa Amira ce fa ta gani saye da irin wuɗan nan kayan yau, a hankali ta miƙa hannu cike tsoro tana ƙoƙoƙarin taɓa ta haɗe da cewa "Amira..." Ai kuwa kafin ta rufe baki tana jin muryar ta tayi wani irin kukan kura tayo kanta don dama cike take da ita tana faɗin,

"Baza mu ƙyaleki ba, sai mun kashe ki.." zaro idanuwa mm yayi a daidai lokacin da Amira ta kaiwa Janan wata irin shaƙura, yana faɗin,

"Subhanallahi, don ALLAH ku taimaka" tare da nuna su yana kallon ƴan matan dake wajen, ga mamakin sa kawai sai yaga duka sun dare suna ihu ko wace ta kama gaban ta, ɗaiɗai ku ne suka tsaya suna kallon ikon ALLAH suma ɗin sun ja baya saboda tsaron kai,

Janan kuwa abun ma dariya ya bata tayi tsaye tana kallon yanda Amira ke faman cukuikuya mata ɗan kwalin abayar data yi rollin dashi, cike da tsoron kada Amira ta cutar da ita mm ya ce,

"Pls Janan kiyi wani abu mana kada su cutar dake"

"Barsu na gani mm, me zasu iya yimun bacin gaka tare dani, ko sun manta cewa ni ƙawar tace"

"No bazan iya kallon wannan cin zarafin da take yi maki ba, zan fa iya karyata idan na ƙaraso wajen, kawai kiyi wani abun" ya ƙare maganar cikin ɓacin rai yana ji kamar yaje ya fizge Amira daga jikinta ya faffalla mata marora,

Tuni Janan ta fahimci babu wasu aljanu a jikin ƙasar tata don tunda tazo wajen take addu'o'i, kawai pretending ne takeyi, wanda bata san dalilin ta nayin hakan ba, murmushi kawai tayi haɗe da jawota ajikinta ta rungume ta raɗa mata a kunne, "Stop pretending haka Amira, zafa a iya gano ki, me yake faruwa ne haka har kike tunanin ɗaukar wannan ɗabi'ar a matsayin mataki?, Koma dai meye kiyi gaggawar sauya sa don gab yake da zubar maki da mutunci"

Wani irin kuka Amira ta fashe dashi tare da faɗuwa a ƙasa dirshan kamar wata ƙaramar yarinya tana faɗi

"Ke ce silar komai Janan, ko meye ya faru dani ke kika jawo, gaba ɗaya mutanen dake wajen suka maido hankalinsu ga Janan suna kallo cike da mamaki jin abunda ƙawarta ke faɗa, ɗan sinne kai Janan tayi ƙasa tare da takowa ta zo inda take zaune,

"Ban fahimceki ba Amira, taya kike tunanin zan zamo silar faɗawarki cikin irin wannan mummunan yanayin, kin ga tashi muje class koma meye mayi magana acan" ta ƙare zancen tare da miƙa hannu da nufin riƙota, tasa hannu bibbiyu ta tureta da ƙarfi har sai da ta faɗi ƙasa kanta ya bugi wani dutsi dake wajen ta saki wata irin azaba biyar ƙara saboda azabar buguwar da tayi, da gudu mm ya rugo haɗe da ɗurƙusawa a daidai saiti kan Janan daya fara zubar da jini, cikin ɓaci rai ya ɗari kai yana kallon Amira dake tsaye tana murmushin jin daɗin yanayin da Janan ke ciki, ba tare data ankara ba taji an ɗauke ta wasu irin zafafan maruka guda biyu da har sai da suka kusa sa ta dena gani, cike da mamaki ta dafe kunci tana kallon mm da idanuwan sa gaba ɗaya suka sauya sukayi jajir saboda tsananin ɓacin rai,

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now