PAGE__24

139 6 1
                                    

_Page 24_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*

*GA MASU BUƘATAR A TALLATA MASU HAJOJINSU, KO KUMA SABABBIN LITTAFANSU DA SUKE SON FIDDAWA ZASU IYA TUNTUƁAR WANNAN LAMBAR KAI TSAYE TA HANYAR WATSAPP 07040402435*
______________________________
Sun jima a falon suna fira bayan sun kammala cin abincin har da Madam florence tana ƙara basu shawarwari akan halin rayuwa, yayin da Nihal ko jin abunda take faɗa ba tayi balle ta amfani da Alkhairan dake cikin sa, tunani kawai takeyi ina zata samu mafita arayuwarta akan ciwon son dake addabar zuciyar ta, ta wani ɓangaren kuma tunani takeyi na yanda zata shawo kan Abban nasu akan zancen 'yar uwar tata, har suka kammala firar su bata ce ƙanzil ba Janan ta juyo haɗe da cewa,

"Wai Adda bazaki dena wannan tunanin hakan ba?, Tun ɗazu sai magana Madam keyi maki amma kinyi shiru"

"Srry Madam, what are you saying?" Nihal ta faɗa haɗe da sakin wani gauron nishi tana kallon Madam, itama kallon nata takeyi tare da mere baki irin abun nan ya sha maka kai har tana ɗora hannayenta akan ƙirji, ta jima a haka tana kallon Nihal kafin tace,

"Look my doter, don't go and kill your self saboda tunanin wanda baki ma san shi ba, am sorry ba ina ganin laifinki bane, nasan zuciya bata da ƙashi kuma so gaskiya ne, amma ya kamata ki sassauta wa kanki hakan"

"Madam, what are you trying to tell me? Na dena son sa?, What the biggest mistake you are trying to do" ta ƙare zancen tare da janye throw pillow ɗin dake saman cinyarta tana yiwa Madam florence wani irin kallo mai cike da tsantsar reni da tarin tambayoyi,

"Noo...ba haka nake nufi ba, ina nufin kirage wannan tunanin da kikeyi akansa, saboda bana son kisake shan wahalar da kika sha kwanakin baya na ciwon zuciya"

"And so what idan nasha wahala akan sa?, can't you know that tunanin shi ne kaɗai ke sa ma mun natsuwa tare da ragemun raɗaɗi da zafin da nake ji azuciya ta? So lemme tell you one thing madam, wlh even if am gonna die bazan dena tunanin sa ba, and don't ever try to tell me dis again, just leave me, haka nake buƙata kuma haka zanyi" ta ƙare zancen cikin fushi tare da jifa da pillown sannan tamiƙe ta bar wajen,

Kasa cewa uffan Madam tayi sai ma binta tayi da kallo tana taka upstairs ɗin har ta shige, girgiza kai Janan tayi tare da dafa kafaɗar Madam florence ta ce,

"Am so sorry Madam, halin Adda Janan kenan, sam bata saurarar kowa akan duk abinda take so, shiyasa kika ga nima na ari wannan halin this time, let her be tunda ita ta saka kanta, kawai muyi mata addu'a"

"But i pity her Janan, tana shan wahala fa idan ciwon ya tasar mata"

"I know, but ya zamuyi da ita tunda haka take so?"

"Oh ALLAH, have mercy on her, be cause zai iya taɓa mata lafiya" ta ƙare zancen tare da ɗaga hannayenta sama tana addu'a, nan ma sun ɗan jima ita da Janan suna sake ɗan taɓa fitar kafin suyi saida safe ta haye sama ita kuma ta wuce kitchen tana rarrage 'yan aikace aikacen da zatayi gobe, tana tsakar yi Abba ya leƙo ya ce "Madam gobe za a yi baƙi a gidan nan, ko akwai abunda kike ganin za'a iya buƙata da babu?"

"No sir, just that the remaining meat in the freezer is little"

"Nevermind with that, all i want , make sure that the house is very clean and i will handle the remaining issues"

"What about the food sir"

"Don't mind that"

"Ok sir" ta ƙare zancen haɗe da miƙewa ganin ya juya yabar wajen,

TUKUICIN SOOnde histórias criam vida. Descubra agora