PAGE__42

237 4 0
                                    

_Page 42_

*TUKUICIN SO💞*

*NA*

*BILLY S FARI💎*

Ɗora hannunta Momy tayi akan Razina dake saman kafaɗar tata tana kuka, ta ce

"Aah autan Momy meye abun kuka anan kuma?, Ai ba jimawa sosai zaiyi ba"

"Momy suna yin faɗa da ya Jabir, bana son haka sam"

"Commooon, ai haka sukeyi akoda yaushe, matuƙar abu ya faru tsakanin su tofa sai sun hau sama sun faɗo suke daidaita, yayan naki ne zuciya tayi masa yiwa, pls kiyi ƙoƙari ki sauya mun shi kinji ƴatah?" Ta ƙare zancen tare da ɗago fuskar Razina dake saman kafaɗarta, tayi saurin maida kan ƙasa tana wasa da yatsun hannunta haɗe da cewa,

"Bazan iya ba Momy, wlh nima tsoronsa nake ji aduk lokacin daya sauya irin haka"

"Don't worry kinji ko ƴatah, ina yimasa addu'a sosai na tabbata kuma da taimakonki zai sauya da izinin ALLAH"

"I wish that Momy" ta faɗa tare da ɗago kai tana kallonta, ta sakar mata murmushi alamun ƙarfafa guiwa da kuma sa ran da take dashi akanta wajen sauyawar yaron nata sannan ta shige cikin gida, ƙarasawa bakin gate dake buɗe ita kuma tayi ta rufe sannan ta wuce part ɗin su ta gyara kafin Jabir ɗin ya dawo, don dama wasu lokutan ita ke gyara masu idan mm bai samu gyarawa ba, don shi mutum ne mai tsananin tsabta da baya son zama da datti, shiyasa duk lokacin da wani uzuri ya hanasa gyarawa sai ya kira Razina bayan sun fita yace ta shiga ta gyara masu, hakan yasa abun ya zame mata jiki ko makaranta taje ta dawo zata shiga part ɗin ta duba, idan ba a gyara ba sai ta gyaro tayi masu turare sannan ta jawo ƙofar ta rufe masu,

Ganin har sun kusa isa airport ɗin Jabir baice komai ba yasa mm ɗago kai yana kallon sa, ba tare daya damu da kallon da yakeyi masa ba ya ja wani iska ya furzar ta baki haɗe da ɗage hannunsa ɗaya daga sitarin motar yana dubin agogon hannunsa, murmushi mm yayi haɗe da cewa,

"Alhamdulillah, zuciyar ƴan mazan ta kwanta kenan, wannan irin iska daka furzar haka ai sai kasa ya ɗage motocin dake gaban mu" murmushi ya saki ba tare daya auna ba haɗe da kauda kansa ta gefen glass ɗin motar yana ƙoƙarin danne dariyar dake son zo masa jin abunda mm ya faɗa, wai ya ɗage motoci, sai kace wata guguwar iska?, Kamar ya shiga zuciyarsa ya ji abunda yake faɗa kawai yaji ya ce,

"ALLAH ina faɗa maka iskan nan daka fitar ko guguwa albarka, don ALLAH jb karage fushin nan haka, nasan grandma bata kyauta ba, atleast ko barayi komai ba alokacin ya ci ace ko sau ɗaya ne ta dakatar daku daga tafiya, sai ALLAH yasa batayi hakan ba, wannan kuskure ne kuma laifine ta aikata" sai alokacin Jabir ya juyo yana kallonsa haɗe da cewa,

"Ka yarda da hakan da tayi kuskure ne kuma tayi laifi?"

"Na yarda, amma ai itama ta fahimci hakan kuma tayi nadama shiyasa kaga tana neman yafiya, in son samu ne kayi haƙuri ka kuma yafe mata kamar yanda Momy tayi, na tabbata zaka samu wani farinciki a zuciyar ka"

"Babu wani farinciki da baku bani ba aduniya kai da Momy, farinciki ɗaya ya rage mani shine ku aura mani Razina, dana samu wannan shikenan na samu dukkanin farincikin duniya daga gareki ba sai na je neman sa a waje ba" ganin har yanzu da saura Jabir bai sauka ba ya sashi haƙura da cigaba da maganar har sai zuwa nan da kwana biyu  tare da cewa,

"Shikenan, yanzu dai ɗan hanzarta lokaci na ƙurewa kuma amanar Momy, Janan da kuma kaka na hannunka kafin na dawo, ka kula mani dasu sosai" wani kallo Jabir ya jefa masa sannan ya ci gaba da tuƙinsa, kamar bazaiyi magana ba sai kuma can ya ji ya ce,

"Ka manta baka haɗa da tsohon naku ba" dariya mm yasa har yana dukan dashboard ɗin motar kafin yace, "to shikenan ka haɗa duka dashi ka kular mani dasu sosai" daidai lokacin Jabir yakawo ƙofar shiga airport ɗin ya turo kan motar ya shiga ya samu wuri ya yi parking haɗe dayin tsaki, ya ce

TUKUICIN SOTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon