PAGE__1

701 24 2
                                    

_Page 1._

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free book*

_Bismillahirrahmanirrahim, wannan littafi bana kud'i bane(free book) ne don faranta zukatan masoyana, haqqin mallakata be, banyarda wani ko wata su saidamun dashi ba ko kuma su karanta mani abu ta YouTube har saida izinina!, na fad'a banyarda ba har saida izinina📵❌, don haka akula!😍_

  *A* guje ta shigo cikin makarantar da mota kasancewar qarfe 8:00am na safe take da lectures, gashi kuma har takwas da rabi ta soma wucewa, sanin da tayi cewa babu jituwa tsakaninta da malamin da zai d'aukesu darasin yau da safe d'in  saboda irin malaman nan ne masu muguwar matsala had'e da takurawa ga d'alibbai yasa ta sake take wutar motar ba tare da ta damu da dokar rashin yin gudu akan titunan makarantar da kewayenta gabanta na wani irin muguwar fad'uwa, ALLAH ALLAH kawai takeyi ta ganeta a cikin ajin duk da tasan zuwanta adaidai wannan lokacin baqaramar matsala zai iya haifarwa tsakaninta da malamin ba matuqar ta riskesa aciki,

Tana wannan tunanin ne ba tare data ankara ba daidai lokacin da take qoqarin karya hannunta tashiga kwanar da zata sadata da b'angaren da suke daukar lectures d'in tayi saurin taka wani irin wawan burkin da yasa har seda kanta ya kusan buguwa da sitarin motar sanadiyar jin ta bugi wani abu da batasan ko meye ba agabanta, da sauri ta d'ago kanta cikin tashin hankali had'e da zaro idanuwa tasa hannayenta biyu ta safe kanta tana fad'ar "innalillahi wa'inna ilaihirrajiun" cikin firgita da kid'imewa ganin aika aikar da tayi,

Wani kyakkawan saurayine dake sana'ar saida kwakwa da dabino ta kad'e dake qoqarin fitowa jikin kwanar adaidai lokacin data kawo da ake kira MM MAIDABINO wato (Muhammad muhriz mai dabino), sai d'alibbai suka qire sunan suna kiransa da MM MAIDABINO saboda yayi masu sauqin fad'a, duk da irin tarin raunin da sana'arsa tasa ta nuna ajikinsa hakan bai hana tsala-tsalan 'yan matan dake makarantar bibiyarsa da kalmar so ba, saidai kash! Shi ba wannan bane agabansa, don kuwa yaqi basu dama ko sakar masu fuskar da zasu samu bayyana hakan agaresa, kawai shi dai abunda ya sani kuma ya saka a gabansa baiwuce sana'arsa ba, wacce a kullum yake d'auka a matsayin rufin asirinsa a idanuwan mutane, mutum ne shi miskili da bai fiye son duk wata harkar da zata sakashi doguwar magana ba har saida dalili, yanada tsatstsauran ra'ayi da kuma kwar jini sosai, shiyasa duk qwaqwar 'yan matan dake bibiyarsa basa iya tunkararsa kai tsaye su bayyana sirrin zukatansu, yanada sanyin hali sosai da sauqin kai wanda sune suka janyo masa tarin soyayya da kuma dad'in mu'amala acikin mutane, sosai yakan fahimci yarinyar da duk tazo wajensa da manufin soyayyar aranta saboda sauyin da dafin so ke saurin haifar mata alokacin ba tare da sanin taba, amma yana ganin hakan ko mutunci yake da yarinya zaiyi saurin sauya mata fuska ta yanda da kanta zata shiga taitayinta tare da had'iye abunda tázo dashi aranta, sau tari 'yan mata nashan yin fad'a akansa ba tare daya sanma sunayi ba sai dai in ya ji labari acikin makarantar, shima girgiza kai kawai zaiyi yace ALLAH ya kyauta, kyakkyawane naqin qari dake da hasken fata sosai tare da matsakaicin tsayi da kuma qiba, a yanda jikinsa ya nuna azahiri bazaka tab'a cewa shid'in mabuqaci bane har sai ka ankara da irin kayan da yake sakawa kala biyu da akoda yaushe suka zame masa tamkar wasu yunifom, doguwar riga jallabiya baqa da take had'awa da wani wando bula sai kuma wani yadi ruwan kalar ganye riga da wando irin d'unkin mutanen qauye da ake kira zauren d'ari, wanda yauma su d'inne ajikinsa,

Fitowa tayi da sauri cikin motar tana yarfi da hannayenta had'e da nufar wajen data hango wani abokin sana'ar tasa da ake kira Jabir ya tallabosa, take ta sake kid'imewa tare da qarasawa wajen ganin yanda goshinsa da hancinsa ke fidda jini sai faman lumshe idanuwa yakeyi dake nuni da cewa ya bugu sosai ba kad'an ba, acan gefe kuma baronsa ne ya kife gaba d'aya a qasa komai dake ciki ya watse akan titin, dafe goshi tayi kamar zatayi kuka tare da kallon kayan dake qasa zube sannan ta juyo ta maido kallonta agaresa,

TUKUICIN SOHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin