PAGE__5

252 12 4
                                    

_Page 5_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*

_Wattpad@billysfari9 https://www.wattpad.com/1228556252?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=mYrSfXopi0y3oPiu7GUqySjbsXBMVJX43kBOg04%2B5L0d0SbkVf0XnIXAWORHibq7vq5BIwk0Z%2FpKeoPXn9rPR8dsgzC65JLBGFgYtXScDzKTCbinX%2BGfHEnzWXNXigiJ_

*B* atare daya damu da yanda ta d'auke masa kai ba yayi gyaran murya had'e da cewa, "Janan, wai meyasa bakyason kulani ne aduk lokacin dana buqaci hakan daga gareki, kin kuwa san yanda kike azabtar da zuciyata?, Kin..."

Tayi saurin dakatar dashi ta hanyar juyowa had'e da rolling d'in idanuwanta tana fad'in, "oh my God!, malan karka manta nifa d'alibarka ce, all these words bai kamata suna fitowa daga bakinka ba, zasu iya sawa nadena ganin girmanka kuma..."

"Ya isa haka Janan!, Sai akace maki shi malami baya da zuciya? Bayada hurumin yaso duk abunda zuciyarsa ke so ki akan waye?" Ya katseta shima yana yimata wani irin kallon shaqiyanci, sake kauda kanta tayi had'e da cewa,

"Ok, I understand malan kayi haquri am not interested of you, karatu nazoyi ba soyayya ba don haka let me be plsss malan" taqare maganar tare da had'e hannayenta waje d'aya tana baging d'insa, d'an sosa hanacinsa yayi had'e da miqewa daga duqowar da yayi ta jikin tagar motar tata tare da kallonta yace,

"Ok, as you wish, saidai ina so kisani kamar yanda karatu ba zai tab'a yuyu ba har seda cikakkiyar kulawar malami haka shima malami bazai tab'a samun natsuwa ba saida cikakkiyar kulawar abincin zuciyarsa, kece abincin zuciyata Janan, haqqin ciyar da ita yana kanki, idan kin so ki kula da ita nima na kula da sha'anin karatunki idan kuma kink'i kinsan me zai iya biyowa baya" Yana gama fad'ar hakan yasa glass d'in idanuwansa da tunda ya hangota ya cire had'e da juyawa yabar wajen.

Kota kan maganganunsa bata tsaya biba ta ja motarta tabar wajen aguje, batasan meyasa malamin nan ke bibiyar rayuwarta ba duk daba ita kad'aice d'aliba ba acikin makarantar, ba kuma ita kad'aice keda kyauba balle yabi ya uzzurata, da ire_iren wannan tunanin ta isa gida, tun kafin taqaraso makeken gate d'in dake jikin gidan nasu daya kasance mai sensors ne yayi saurin zugewa gefe ta shige mai gadi ya d'aga hannu had'e da russunawa yana gaisheta cike da girmamawa, horn kad'ai tayi masa alamun amsawa tare da zagaye katafaren roundabout d'in dake tsakiyar harabar gidan sannan ta nufi inda aka ajiye don motoci tayi parking motarta tafito riqe da makullin motar da jikkarta a hannu, daidai lokacin mahaifinta shima yafito bodyguard d'insa na biye dashi sun take masa baya zai fita, tsaye tayi tana kallonsa ganin waya yakeyi har saida taga ya qarasa yana qoqarin shiga motar da d'aya daga cikin guard d'in ya bud'e masa tayi saurin zuwa wajen.

"Abba.."

Da sauri ya juyo fuskarsa d'aure ba walwala had'e da cewa,

"What Janan? Har kin dawo daga school d'inne?"

"Eh Abba, barka da fitowa antashi lafiya?"

"Lafiya Lau"

Har zatayi magana sai kuma tayi shiru don akwai maganar da take so tayi dashi ga kuma bodyguard awajen, kallo d'aya yayiwa guards d'in gaba d'aya suka bar wajen don sun fahimci me yake nufi kamar yanda shima ya fahimci dalilin daya hana 'yar tasa maganar da take son yi.

"Ina saurarenki Janan akwai wani abune?"

"Eh Abba, Ina so ne muje wajen grandma idan ka amince"

"Kinyi marmarin tacimun mutunci kenan!"

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now