PAGE__12

140 6 0
                                    

_Page 12_

*TUKUICIN SO*💞

*NA*

*BILLY S FARI*💎

*HASKE WRITTER'S ASS..💡*

*Free Book*

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*

INA KUKE MAKARANTA??

INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️

TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B

INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.

DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA

(1000) DUBU DAYA KACAL _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR KU TUNTUBI WANAN NUMBERS DIN_

👇🏼👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
+447894142004
07065283730
______________________________
*S* ai da aka share kusan awa ɗaya kafin su Janan su fito wajen lectures, cike da farin ciki Janan ta ɗauki jikkar ta ta sagala a kafaɗa ta ce wa Amira bara taje ta amso dabino wajen mm data siya ɗazu ta ce ya ajiye mata kafin su fito, wani irin kallo ta bita dashi cike da tuhuma kafin tace,

"Oh! ke ba zaki je practical ɗin bane?"

"Zan je mana, amma sai na samu abunda na sakawa ciki na a capteria tukuna, kin ga idan zaki je taso muje kada ki ƙara ɓata mun lokaci"

Duk da akwai abunda Amira keyi haka kurum taji bazata iya bari Janan taje inda mm ba ita kaɗai, bazata juri ko kallonta yayi ba saboda kayan da ALLAH yayi mata ba duk namiji zai kalleta ba bai ji wani abu ya burgesa a tattare da ita ba, ko dai kyanta, ko ɗabi'unta ko kuma surar jikin ta, dole wani abu ya iya ɗauke maka hankali tattare da ita, kuma bata buƙatar hakan ta faru ga mm ɗin ta, don haka sai ta miƙe ta ɗauki jikkar ta itama ta sagala a kafaɗa, haɗe da cewa,

"Muje ko?"

Ba haka Janan ta so ba, amma nuni yanda ta iya sai kawai ta haƙura suka fita tare suna kaiwa bakin acadamic staff sai ga Ingaski shi da wani lecturer sun ci karo dasu, da sauri Janan ta ɗauke kai tayi kamar bata gane su ba, cike da mutunta Amira ta shiga rissinar da kai tana gaisheshi don yasan ko Amira ba ta so itama dole ta gaishe sun, shi kuwa Ingaski babu yanda za a yi ya haɗu da ita bai ce yana son ganin ta ba, idan kuwa hakan ta faru ba ƙaramin farinciki zata yi ba, don yanda Janan tayi kyau ɗin nan bata fatar su haɗu da mm ɗin ta,

Ai kuwa hakan ta faru don ba kunya suna rufe baki Ingaski ya ce Janan ta biyo shi office ɗin sa, ji tayi kamar ta ɗora hannu saman kai ta ƙwalla ihu haɗe da juyowa ta naɗawa Amira duka a kafaɗa kamar za tayi kuka ta ce,

"Wlh duk sherin ki ne Amira, sarai kin san malamin nan baya biya ta da alkhairi amma ki tsiri gaishe sa, gashi yanzu kin jamun ko banai wa ALLAH dole naje tun da banda hanyar guduwa"

"Ikon ALLAH! Yau ni naga ƙarfin hali, to sai na fasa gaida malami na saboda ke bakya shiri dashi?, Ina kika ji an taɓa haka? Ban da abunki ma ina laifin wanda ya ce yana son ka?" Ta ƙare maganar tana dariya, don kuwa gaba suke da office ɗin nasa, duk yanda Janan taso guduwa hakan bazai yuyu ba, harara ta maka mata haɗe da yarfar da hannu kafin tace,

"Baza ki gane ba Janan, wlh ni zuciyata tana da wanda take so, bance ya yi laifi ba, amma tunda ya ga bana sonsa ai sai ya haƙura dani tunda bani kaɗai ce macce ba a school ɗin nan" har lokacin Amira na dariya ta ce,

"Ehm, yanzu dai jeka kada yaga kin daɗe, ni naje nayi maki order ɗin abinda zaki ci daga nan na biya na karɓo maki saƙon ki a wajen mm"

Tsabar takaici Janan bata tsaya bi takan taba ta nufi office ɗin nasa tana mai ƙudurta abubuwan da zata faɗa masa a zuciya, ita kuma ta buga tsalle haɗe da kimtsa kanta sosai sannan ta nufi wajen su mm zuciyarta cike fal da farin ciki,

Fuska a tirniƙe ta shiga office ɗin nasa babu alamun fara'a ko kaɗan a tare da ita tayi tsaye a bakin ƙofa ba tare da ta ce komai ba hannayenta na akan ƙirjinta rungume da wani practical text book data karɓa hannun class rep ɗin su da zasu fito,

Murmushi Ingaski yayi haɗe da cire glasses ɗin idanuwan sa yana ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa, yayi mintuna biyar a haka kafin can ya ce,

"Gimbiya Janan ƙaraso daga ciki mana" ya ƙare magana yana wani kasar baki haɗe da kwantawa baya akan kujerar da yake zaune, sai da ta furzar da iska abakin ta haɗe da juyar da kanta gefe sannan ta ce,

"Malam gani, ka faɗi mun dalilin da yasa ka kira ko.." bata ƙarasa ba taji yake,

"Tsaya Janan, ai kinsan labarin gizo dai bai wuce ƙoƙi, har yau dai na kasa haɗiye yawuna akanki, gashi kwana biyu kinyi mani wuyar gani, ina kika shige ne haka?"

"Shikenan malam?"

"A'a gimbiya Janan, idan akwai wani abun ma ai sai kin shigo daga ciki za muyi magana a kan sa, ko kin fi so ne ni da kaina na taso muyi maganar anan?" Ya ƙare maganar haɗe da miƙewa ya nufo wajen da take tsaye, ba tare data ankara ba sai dai ta ji hannunsa sama kafaɗarta yana murzawa, ƙoƙarin ƙwacewa ta shiga yi kawai taga ya nufo da fuskarsa zuwa saiti wuyanta yana ƙoƙarin sumbatar ta, cike da ɓacin rai ta ɗago hannu ta wankesa mari tare da turesa gefe tana hawaye, cikin kuka ta fara magana haɗe da cewa,

"Tir!, wa'iya zubillah da wannan rayuwar, meye ribarka malam idan kayi ƙoƙarin lalata wa yarinyar daka kusa haihuwa rayuwa? Wannan itace amanar da iyayen yara ke damƙawa a hannun ku bacin duka sun tattara yardar su da kuma yaƙini akanku cewa zaku kula masu da ƴaƴan su tamkar naku? Ina girman malan takar da kake iƙirarin kana da ita a kaina?, a ina so da ƙauna suka samu gurbi a zuciyar dake da irin wannan mugun nufi acikin ta?, Ina..."

Da sauri ya ɗaga mata hannu cikin ɓaci rai yana zaro mata idanuwan sa da suka kaɗa suka yi jajir haɗe da nuna mata ƙofar fita da hannu yana faɗin,

"Fice mun daga office Janan, zan gwada maki cewa lallai kinyi kuskuren yin shuka a gonar mai hauya, kuma daga yau ki fara ƙidayar kwanakkin baƙin cikin ki acikin makarantar nan, don sai na sa kinyi nadamar zuwan ki cikin ta, kin kuma yi nadamar wannan kyawon da kike dashi da har yake saka ki iya ɗaga hannu ki mari malamin ki, idiot gerrout in my office" ya ƙare maganar cikin ɗaga murya da ƙarfi har sai da ta ra zana, da gudu ta fice daga office ɗin aguje tana kuka...

#comment
#vote
#share.

*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭*

TUKUICIN SOWhere stories live. Discover now