A GIDANMU SUKE Labari ne aka...

By pinky__leemart

436 31 2

A gidanmu suke littafi ne Mai tattare da dumbin nadama inda musulmi ya aure arniya batare da sanin kowa ba ga... More

chapter 1
chapter 2
chapter 5_6
chapter 7_8
chapter 9_10
chapter 11_12
chapter 13_15
chapter 16_20
chapter 21_25
CHAPTER 26_30
chapter 31_35
chapter 36_40
chapter 41_45
chapter 46_50
chapter 51_55
chapter 56_60
chapter 61_65
chapter 66_70
chapter 76_80
chapter 81_85
chapter 86_100

chapter 71_75

8 1 0
By pinky__leemart

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKAR👇
*LEEMART PINKY*
           AND
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

*PAGE 71&75*

Abieee wallahi ƙarya takemin sharri tamin,Abie ban taɓa riƙe hannun wata don naji daɗi ko in aikata zina da ita ba,Abie Jahada ƙanwata ce bazan so in ɓata mata rayuwa ba,Abie ku yarda dani bani bane,bani nai mata ciki ba,taji tsoron Allah tafaɗi gaskiya".

Cikin dakusassiyar murya yake magana idon shi hawaye masu ɗumi suna sauka.

"Wallahi Abie shine ranan yace,"in kawo mai fresh milk,naje na iske shi kwance wai marar shi naciwo,in kulle ƙofa inzo in temaka masa,duk nabi na ruɗe Abie ganin baida lafiya na dafa ruwan ɗumi a kitchen ɗin side ɗin su nazo da towel a tinani na buguwa ne yasa  zan gasa masa,kawai-kawai-kawai".

Jahda ce ke magana cikin muryan ban tausayi kamar da gaske labarin da take badawa.

Bako kunya take saki magana gaban iyayen ta.

Abie cikin tsawa mai cike da tsantsan ɓacin rai yace,"kawai mai munafuka,ki magana ko  inkashe ki tun kafin ki kasheni,dabadin ƙarfin addu'a ba da yanzun kun samin hawan jini keda munafukar uwarki".

"Eh dole kace haka,ancuce mu a hanamu kuka,tou wallahi ko ya aureta ko nakai shi kotu".

Hajiya Jamila ke magana cike da murje ido bako kunya tana ganin asirin su zai rufu.

"Jawahir kije side ɗina ki ɗauko flash a jikin  laptop ɗina ɗakina akwai CCTV za'a ga kom".

Cewan Jahir da yake ƙoarin gyara zaman shi.

Daga Hajiya Jamila har Jahdah lokaci ɗaya suka miƙe suna kallon Jaheer ,ɗakin duk su suka zuba ma ido,kowanne su cike da tashin hankali tsantsa a fuskan shi.

Jawahir ko jiki na rawa ta miƙe tafita har tanacin tuntuɓe,haɗa ido sukai da Jahoor ta galla masa hararan da sai da yaji gaban shi ya faɗi,don cin mutunci a gaban ta ya doke yayanta akan laifin da ba nashi ba.

Munites kaɗan ta dawo ta miƙa ma Abie.

Abie sawa yayi jiki tv bayan ya kunna,Jahir ya zuba ma Jahda ido don ya tsinke da alamarinta wato boka har ciki yai mata.

"Jahir wane folder ne?.

Faɗan Abie kowa ya zuba ma Tv ido zasu sha labari.

Jahir yabuƙace a bashi remote ko aka bashi ya duba folder sai gashinan  kamar a film,tunda  Jahir yashiga ɗakinta yai mata treatment  tai bacci da harhiran da sukai tabashi labarin amfani da boka da yayi da ita awatan ramadan.

Kuka kawai Jahda take bayan ta zube guywowinta a ƙasa.

Hajiya Jamila ta ɗaura hannu akai ta kurma ihu ta faɗi ƙasa tana ta birgima,tana faɗin Jahda shegen bakin ki ya jawo da baki faɗa ba,gashinan ya ɗauka wayyo Allah na.

Kowa zuba musu ido yayi yana kallon su da abinda suka aikata na Allah wadare.

Jahoor da Jadida kamar su shige ƙasa don kunya haka Abie Hajiya Mama kuka kawai takeyi.

Abie hawaye masu ɗumi kebin kumatun sa,kowa a falon nan jikin shi yayi sanyi ya kasa magana,musamman Abu da ya rinƙa zagin Jaheer.

Hajiya Juwairah girgiza kai kawai take tana hawaye tana dana sanin biye ma ɓacin rai tai ma ɗanta baki akan wata banza.

"Jaheer kayi haƙuri ka yafe min rashin fahimtar da nayi maka".

Faɗan Jahoor da jikin shi duk yayi sanyi.

Murmushin da yafi kuka ciwo Jaheer yayi yace,"bakomi Brother Allah ya yafe mana".

"Jamila Allah ya isa tsakani na dake sam bazan yafe miki ba har abada ba ƴaƴana ba ki ba ƴaƴana ba ƴaƴanki,tunda har kina da ƙarfin zuciyar biyema Jumaina takaiki wajan boka".

Faɗan Hajiya Juwairah.

Hajiya Jumaina a tsorace ta tashi tana dukan ƙirjinta tana faɗi

"Baruwana wallahi bansan Jamila taje wajan boka ba,ba hannuna ba ƙaf.....!

"Dakata min munafuka,bake kikazo mana da maganan zuwa gidan boka ba duk maganan da nai muku da tunasarwa ,ashe kinbita kinsa takai ƴarta da yake ita sakaryan mace sauna ce".

Cikin tsawa da ɗaga murya Hajiya Juwairah ke maganan,yayinda ta katse Hajiya Jumaina daga maganan da takeyi.

Nan fa falon ya hargitse da hayaniya kowa na faɗan albarkacin bakinsa.

Jahda kuka kawai take yayinda Hajiya Jamila ba abinda take face zazzare ido cike da tarin borin kunya.

Abie waje yasamu ya zauna bayan ya tsawata ma matan sunyi shiru ,cike da takaici da ƙyama yake kallon Jamila.

Cikin sanyin murya yace,"Jamila kije na....!

"Dakata Jabeer karka sake ka sake Jamila,kabarta da duniya kaɗai zata koya mata hankali,duniya zata gyara mata zama,tunda tana girma tana cin tsakuwa sam bata san shekarun ta naja ba".

Hajiya Mamah ce tayi saurin katse Abie.

Hajiya Jamila nauyayyan ajiyar zuciya ta sauke ,jin furucin Hajiya  Mamah dole ta miƙe tsaye akan Jabeer tanemo saa in ba haka ba ,duk randa munafukar tsohuwar nan ta mace tou zaman ta ya ƙare a gidanan,maganan Abie ya dawo da ita daga duniyar tinanin da ta lula.

Ƙasa yai da kanshi akaron farko da hawaye masu ɗumi da suka sakko a idon shi,yai saurin sa hannu ya ɗauke su don kar agane raunin zuciyar shi,kafin ya ɗago yace," Mamah Jamila ba matar zama bace,Jamila ba uwa ta gari bace,yau inajin kinyar ƴaƴana dana kasa samo musu uwa ta gari,inaga na haɗu da mahaliccina ,mai zance masa?.

Cikin sanyi murya yake maganan.

Take kowa a falon jikin shi ya mutu,ba abinda ke tashi sai sautin kukan Jahda.

"Eh-eh-eh naji ni bata garin bace ,aje asamo na gari,eh tunda anci moriyar ganga dole a gayamin magana".

Cike da borin kunya Hajiya Jamila ke magana da ta murje idonta da toka take zubo zance.

Kowa sai da tabashi mamaki yanda ta murje ido take magana.

Hajiya Mamah ko girgiza kai tayi tace,"ku sani ƴaƴa fa amanane Allah ma ɗaukakin sarki ya bamu,kuma zai tambaye mu amanar da yabamu ranan gobe ƙiyama,tarbiyan ƴa mace in kayita kamar ka tarbiyantar da alumman musulmai ne gaba ɗaya,amma Jamila kin bani kunya,tou wa gari ya waya,aikin bokan yaci,in aikin boka gaskiya ne kibashi wayarki kice yacire miki password,aiki mai sauƙi nabaki".

"Nide wallahi in ni kaɗai yai saura in yafe ma Jamilata shiga aljanna bazan taɓa yafewa ba,duk yanda nake ƙiyayya da mutum bazan kai shi wajan boka anamimin Allah ba".

Faɗar Hajiya Juwaira datake matsan ƙwalla.

"Ummie kiyi haƙuri,komi muƙaddarine daga ubangiji,tun ran gini tun ran zane".

Jaheer ke magana a sanyaye.

"Ya zaai da cikin jikin Jahdah yanzun?

Tambayan Alhaji Jalal,da yake zaune tun ɗazun shiru kamar ruwa ya cinye shi.

"Wannan uwarta zaku tambaya,amma wallahi biyar ɗina bazaiyi ciwo wajan cire ciki ba,sannan kusan makomar mai cire ciki wajan ubangiji mahaliccin kowa da komi".

Abie ke maganan cike da takaici.

Shiru Alhaji Jalal yayi jin abinda yayan sa ya faɗa.

Sannan na sallamata wallahi nacireta cikin ƴaƴana nabar ma Jamila ita,Mamah karkice banji maganan ki ba awannan karan a gaskiya a gaskiya sam bazan iya zama da Jamila ba,damin haka na saketa saki ɗaya,ta zauna a ɗakinta don ƴaƴanta".

Wani kururuwan ihu Hajiya Jamila ta sake tayi kan Jahda ta kama dukan ta tana tattaka mata ciki,da ƙyar aka amashe ta aka fitar da Jahda zuwa part ɗin Hajiya Jasmin.

**********
Tundaga wannan ranan Abie yafita harkan Hajiya Jamila,saide ta hango shi daga nesa.

Jahda ko tana side ɗin Hajiya Jasmin tundaga dukan da uwarta tai mata aka maidata bata koma ba,ko fitowa batayi.

Juliet ko ta ɗau zafi ta ɗaura akan Jahir ko kulashi batayi ko hanya bata bari su haɗa wasan ɓuya sukeyi,don tun a asbiti da taji Jahda tace shi yai mata ciki,bata ƙara shiga cikin mutane ba,bata ƙara sakewa da kowa ba harda Jesica kullum cikin kaɗaici da tunani take,tun abin nadamun Jesica har yadena damunta,tunda taga damuwar bai hanata ci dasha da wanka.

Jawahir ko kula Jahoor tadena yi don yanzun mugun haushin sa takeji ,tunda ya dakar mata yaya agabanta baijira anyi bincike ba.

Jahoor duk ya damu da fushin da takeyi dashi da ƙyar yasamu Hajiya Jasmin ta shirya su.

Hajiya Jumaina ko ba abinda yakeyi face ƙara zuga Hajiya Jamila suka fantama bin bokaye don ganin Alhaji Jabeer ya maidata.

Hajiya Juwairah ko yanzun takama ƴaƴanta ta rungume su tsam,sallah da da ta denayi yanzun tanayi shi sosai tana ma ƴaƴanta adduan kariya ga masheranta.

*WANNAN KENAN*

******
"Jawahir dan Allah kije ki fahimtar da Juliet bani bane sharrine,bata min magana bata ɗaukan wayata,taƙi ko saurarana ta fahimce ni,ban ma ganta ba balle ta saurare ni,inason Jawahir sosai bazan iya rayuwa in bata ba".

Jahir ke magana cikin raunanniyar murya kamar zai ma ƙanwar tashi kuka.

Murmushi tayi tare da shafo fuskan shi tace,"............!

*MRS BASAKKWACEPINKY*

Continue Reading

You'll Also Like

367K 1.2K 47
🔞🔞🔞 warning sex!! you can cancel if you don't like it.This is only for the guys who have sensitive desire in sex.🔞🔞
9.5K 113 34
A WOSO Oneshot book Oneshots of favourite Women's footballers Mainly the Lionesses, Arsenal Women's team,Chelsea Women's team, Man City Women's team...
30.4K 588 39
Short scenarios for your favorite characters! (Well the male characters at least) The characters included are Alastor, Angel Dust, Sir Pentious, Husk...
65.8K 2.4K 43
အချစ်ဦးကသမီးငယ်ဖြစ်ပြီး အချစ်ဆုံးကတော့မောင်ပေါ့။ မောင်ဆိုတာကလဲ သမီးငယ်ဘဲလေ..။