A GIDANMU SUKE Labari ne aka...

By pinky__leemart

436 31 2

A gidanmu suke littafi ne Mai tattare da dumbin nadama inda musulmi ya aure arniya batare da sanin kowa ba ga... More

chapter 1
chapter 2
chapter 5_6
chapter 7_8
chapter 9_10
chapter 11_12
chapter 13_15
chapter 16_20
chapter 21_25
CHAPTER 26_30
chapter 31_35
chapter 36_40
chapter 46_50
chapter 51_55
chapter 56_60
chapter 61_65
chapter 66_70
chapter 71_75
chapter 76_80
chapter 81_85
chapter 86_100

chapter 41_45

8 0 0
By pinky__leemart

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDANMU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKAR👇
*LEEMART PINKY*
           AND
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

JINJINA GA -: _MASOYAN GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_

*PAGE 41&45*

"Nifa in gaya miki Jawahir yarannan tun daga uwarsu har su ba wanda ya taɓa min abu ƙi ko abun Allah wadare hakanan kawai ban son su ban ƙaunar su".

"Amma de Ummie sam hakan bai kyautu ba wallahi,yanzun Alal misali Ummie hakanan kawai kiga wani ko wata sun ɗaura min karan tsana ya zakiji a ranki?.

Shiru Hajiya Juwaira tayi kamar mai nazarin wani abu,can kuma ta ƙara duban ƴar tata tace,"wallahi bazan ƙaunace shi ba har abada,wai kinsan soyayyan dake tsakanin ɗa da uwa kuwa,koko kin san soyayyan dake tsakanin wanda ya nuna yana son ɗan ka,kibari ki aure zaki tantance yanzun ko mai zan faɗa miki bazaki fahimta ba".

Murmushi Jawahir tayi tare da tashi daga kishingiɗan da tayi ta gyara ɗaurin kalabinta tace,"Ummie duk kinsan da wa ƴannan amma kike nuna musu kyara don ba addinin mu ɗaya ba,kyaran da muke gwada musu bazai sa su musulinta ba,ba abinda zai jawo ma musulinci illa a rinƙa cewa ashe haka musulincin yake,basu son mutane,ƙyamar wa ƴanda ba addini ɗaya suke ba,amma in muka ja su a jiki,ba ƙyama balle kyara hakan zaisa suji suna ƙaunar addinn mu suji har suna sha'awan shiga".

"Tou tabbatacciya baki abin magana mai bakin tsuntsu kawai,nizaki tasa a gaba da wa'azi,tun kafin a haifeki nasan nan tashi kiban waje,don ko musulinta yau sukai bazan bari in haɗa jini dasu ba,sabida mutane zasu rinƙa nuna ni anacewa ga surukan tubabbu".

Cike da masifa tana zaro manyan idanuwan ta take maganan.

Dariya Jawahir tasa tare da miƙewa ta fita,don Ummie su ta haddace faɗan daba gairi ba dalili.

*******
Awajan party da su Jadidah suka je da ƙyar suka sha a wajan maza.

Mata masu wayo ne da sunga ankusa tashi suke kama hanyar gidan iyayen su don gudun ɓarna a wajan ɓatattun maza.

Da yawan matan sun tafi sai tsiraru irin su Jahda daJadidah da wasu ƙawayen su,inda da ƙyar suka sha suka bar wajan kayan su duk a yayyage  Allah ya kawo wani soja ya cecesu.

Koda suka dawo gida anshiga sallah isha'i ba wanda yasan sun dawo kamar yanda ba wanda yasan fitar su.

Koh Hajiya Jamila batasan shigowar su ba,suna can ɓangaran Hajiya Jumaina suna tufka da warwara.

*******
"Wai Ammie har yanzun aikinnan shiru Jahir fa ko kallona baiyi balle ya kulani".

Cike da damuwa Jahda ke gaban mahaifiyarta tana mata magana

"Mtseww shiɗin banza,kina zaune zaizo yana risina miki yana miki daɗin baki,a lokacin zaki juyashi kamar kin samu masa  a tanda anan zai gane cewa duk kyan takalmi ƙafa zai taka".

Cike da kwantar ma ƴarta da hankali take maganan.

Murmushi tayi tace,"wallahi ranan Ammie da sai an haɗa party gagarumi a garinnan".

"Ki kwantar da hankalin ki kawai kin same shi kin gama,in zanyi yawo tsirara sai kin aure shi namiki alƙawari baki da miji sai shi awannan duniyar".

*LALLAI WANNAN HAJIYA JAMILAN MAGANAN KI SAM BABU TAUHIDI A CIKIN SA,KINƁATA SOSAI🤦‍♀️*

"Ammie da kin gama min komi danasan ni ƴar gata ce sosai,wallahi ina son sa sosai Ammie da zan iya cire son shi a zuciyata dana yarda ƙwallan mangwaro na huta da ƙuda".

"Inhar ina numfashi bazama ki yadda ba ,sai kin shanye kin tanɗe tasa".

"Allah yasa Ammie na".

Rungume juna sukai suna murmushi mai nuna tsantsan farin ciki.

*********
"Wa ƴannan akwatinan na mainene Jabeer?.

Hajiya Jamila ne kebin saitin akwatina biyu da aka gama shigowa dasu part ɗinta aka jera  da kallo.

Zama yayi kan kujera mai mazaunin mutum huɗu ya cire hulan sa ya aje a gefe ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya  yace,"duba de ki gani nasan kayan zasuyi miki".

"Induba maine kamin bayani".

Ɗaga kafaɗun shi yayi cikin  halin ko in kula yace,"kayan faɗan kishiya ne,nasamo wata yarinya ƴar ƙarama mai tarbiya da ladabi da biyayya,akwai girmama na gaba da ita uwa uba kunya".

Tunda ya fara magana tai mutuwar zaune tana kallon shi baki buɗe hanci buɗe.

Bai damu da yanayinta ba yaci gaba da faɗin ,fatana kartazo gidanan a lalata min ita ko da yake side ɗin kusa da Jalal zata zauna jibi ne ɗaurin auran ,abinne yazo da gaggawa shiyasa ban faɗa miki ba uwar gida,wallahi sam ban shirya ba bansan zan ƙara miki kishiya yanzun ba naso sai kin fi haka tsufa".

Yana magana hankalin shi kwance sai karkaɗa ƙafa yake kamar sabon basarake.

"Munafuki algungumi nizakazo ma da daɗin baki,tou wallahi ka gaya mata ta tanaje lakafani da butan wankan gawa na shigowa gidannan".

Ranta ɓace take maganan kamar zata fashe da kuka,shiko ko ajikin sa danne dariya kawai yake don baiso ta ƙwace mai.

"Ni zaaci amana a yaudara,arinƙa min kishiya duk matan gidanan ba wacce aka raina aka tsana kamana mijin kowa bai mata kishiya saini".

Miƙewa yayi ya ɗau hulan shi ya gyara mata kari ya sa akai ya kalle ta da kyau kafin yace,"kishirya kishi da ƴar shekara sha shidda inkin zubar da girman ki ko ta takesa tsafff",yana gama faɗa ya juya da sassarfa ya haura sama don wata dariya da take cin sa.

Shiru tayi tarasa bakin magana.

*********

"Hajiya!Hajiya!!Hajiya!!! fito abokin kuka shi ake gayama mutuwa".

Da sauri Jumaina ta katse wayar da takeyi ta miƙe ta taro Hajiya Jamila tana faɗin lafiya mai ke faruwa?.

Fashewa Hajiya Jamila tayi da kuka ta faɗa jikin Hajiya Jumainah.

Hajiya Jumainah ta tsorata don bata taɓa ganin Hajiya Jamila na irin wannan kukan ba.

Daƙyar ta lallasheta da ban baki tayi shiru ta gaya mata abinda ke faruwa.

Wani lailayo kafirin ashar Jumaina tayi ta watsa ma Abbie.

"Wallahi Hajiya mijinki ya rainaki,da nice sai dai gawar shegiyar yarinyar kamarki ace namiji ke miki iskanci miye baki dashi,gobe ki shirya muje gidan mallam a kashe mana tsinanniya".

"Yanzun ma dan dare yayi ne wallahi da muntafi".

Cikin shaƙaƙƙar murya take maganan.

Nan Jumaina tarinƙa zugata tana ɗaurata a hanyar tsiya tana ƙara shigewa.

******
"Abbie aure kuma?.

Faɗan Jadidah da Ammie su take gaya musu yanzunan shigowar su suka ga akwatina suke tambaya na waye.

Mtseww nifa na tsani Abie baya son mu baya son Ammien mu  sam,ni ko gaidashi nayi ma baya amsawa shiyasa nadena gaidashi ko a hanya inkun yarda na tsani inga Abie inbanda rashin imani Ammie zaiwa kish".

Faɗan Jahdah da take tsaye ta riƙe ƙugu.

Kasheta da marin da akayine yai sanadin haɗiye maganan da takeyi.

Kallon wanda yai marin sukai lokaci ɗaya ,sam basu san shigowar shiba tou yaushe ma ya dawo ƙasar basu sani ba.

Ƙara ɗaga hannun yayi zai kai mata mari yaji an riƙe mai hannu ta baya.

Ahankali yake bin hannun da kallo tabbas wannan hannun Abbie na daba Abbie bane sai yasa hannu ya buga ma kowa waye ƙulli a ciki.

"Jahoor karka ƙara dukan ta,inde wannan ƴar ce na salama ma uwarta ita tuntuni zata yi abinda yafi haka".

Abbie ke magana ransa ɓace yana riƙe da hannun Jahoor  lokaci ɗaya ya sake ya dafo kafaɗan shi.

Jahoor ko idonshi yayi jaaa tsantsan ɓacin rai ya bayyana akan fuskan shi ,don baiso ko kaɗan yaga yaro na raina babba,wai yaushe aka haife Jahda da harzata rinƙa gayan magana akan mahaifin su ƙwafa yayi lokaci ɗaya.

Duk mutuwan tsaye sukayi don sun san halin Jahoor in ransa ya ɓaci komi iyawa yake idon shi da jinsa da ganin sa ɗaukewa yakeyi,sai ya aiwatar da abinda yayi niya yake samun natsuwa.

Abbie ko jan shi yayi sukai waje don sanin hali yafi sanin kama yasan zai iya mata duka na ban mamaki yanzun nan.

Shikuma Abbie yasa ma ransa sa musu ido duk abunda suke ɓoyewa watarana zai bayya,ba ataɓa cewa gaskiyan mutum ya ƙare ba sai de ace ƙarya ya ƙare.

"Yaushe kashigo Jahoor?, ban hanaka irin wannan tafiyar ba da ba sanarwa sai de aganka kwatsam".

Murmushi yayi harsai da kumatun shi suka lotsa.

Alokacin nasamu daman ƙare mai kallo wooow mashaAllah duk kyawun Jaheer ashe akwai wanda yafishi.

Jahoor kenan ɗan fari awajan Alhaji Jabeer da Hajiya Jamila, dogone fari tas fatan shi irin kalan larabawan iraq ,yana ɗauke da dogon fuska,mai ɗauke da dogon hanci kamar pencil da manyan idanuwa masu matuƙar ɗaukan hankali.

Gashin giran sa a kwance yake luffff kamar an gyara masa ,yayinda manyan idanuwan sa ke ɗauke da dogayen gashi kamar an masa ƙari,bakin sa ɗan cikuli kamar cokali bazai shiga ba ,yayinda wani ƙayataccen saje da yasha gyara ya ƙarama fuskan ado da kyawu,gashin kansa kwance yake luf-luf  gwanin ban shaawa sheƙi kawai yake.

Yana da faffaɗan ƙirji da tsukakken ƙugu kamar na mijin zaki ,hatta yatsun ƙafarshi da na hannun shi abin kallo ne.

Mata na yawan kawo masa hari amma basu samun fuska,don Jahoor wani kalan murɗaɗɗan na mijine miskiline ajin farko,in ba kamai farin sani ba bazakace yana ko magana ba,zaka iya zaman hour goma dashi maganan da zai fito a bakin shi bai wuce a irga ba.

Baya wasa sam baison raini, akoda yaushe yana da zafi akan ƙannan shi,don inyana nan ko ƙwaƙƙwaran hayani ƙannan shi basayi gudun  horon *CAPTAIN JAHOOR*.

Tun Jawahir na ƙarama ta shiga ransa,gani yake kamar ƴan uwantaka na jinine,don yafi sakewa yai mata wasa akan sauran ƙannan shi mata,abu wasa-wasa har ya girma,ko ƴan aiki maza ya tsani yaga suna mata magana ,ya rinƙa haɗa mata rai da masifa ba gairi ba dalili,da ƙyar take shawo kansa.

Dayaga ba sauƙi sai Allah ya furta mata manufarshi akanta inda take ta amshe sabida yayan nasu bai rasa komi ba wanda ɗa namiji mai nagarta ke dashi,uwa uba son ibada,kyauta da kyautata ma alumma,matsalan shi miskilanci tunda ita bai mata bata da damuwa.

Soyayya suke da Jawahir soyyya mai tsafta,duk da kullum sai sunyi faɗa amma basa iya fivemunites ɗaya bai nemi ɗaya ba,wannan shi ake kira da so na haƙiƙa,komai masoyinka kema bai kamata kai fushi dashiba.

Duk soyayyan nan da sukeyi ba wanda yasani a dangin su, aɓoye suke gina kayan su suke ba ma junan su farin ciki.

Yanzun haka dawowan da yayi ita kaɗai ta san da dawowan shi,shima don karyaga fushi akan fuskan ya faɗamata da badin haka ba sai de ta ganshi kwatsam kamar saukan ruwan saman ogosta.

"Abbie wallahi nayi two hours a gidanan".

Yana maganan yana sosa ƙeya cike da alamun rashin gaskiya.

"Kaci abinci de ko?.

Murmushi ya ɗanyi kaɗan na gefen baki yace,"kai Abbie kamar  yaro naci a ɓangaran Ummie yanzun ma daga can nike".

Dukan wasa irin na ɗa da uba Abbie yakai masa dai-dai lokacin da suka ƙarasa wajan da aka tanadar don shan iska.

Zama sukai  a tare  Abbie yace,"Jahoor har gobe tunda kana gabana kai yaro ne,nima nan da nake gaban mahaifiyata tana kallona ina  kallonta inde ba mai rabawa ya raba ba nima yaro ne".

Sauke sanyayyan ajiyar zuciya yayi tare da lumshe sexy eyes ɗinshi yace,"hakane Abbie".

******
"Cabɗi yaushe mai halin fir'aunan nan yadawo".

Faɗan Jahda dake dafe da ɓangaran da tasha mari.

"Barni dashi wallahi inde nice na zuƙuna na haifeshi sai na gyara mai zama,ƙarya akai uban nashi mutunci ne dashi,ya daɗe bai sallama min kuba,ina da zanin da zan goyaku rass a bayana".

Rai ɓace Ammie ke maganan kamar zata fashe da kuka don baƙin ciki.

"Wai yanzun da gaske jibi zaa ɗaura ma Abbie au.......!

Jadidah ce ke magana cikin sanyin murya kamar kazan da ƙwai ya fashe mata a ciki,tunda taga Jahoor jikinta duk yayi sanyi.

Mai takura musu ya dawo,bai kunyar ci musu mutunci a gaban kowa,Allah yasa yanda suka ganshi kwatsam suneme shi suga ya ɓace kamar anyi walƙiya an ɗauke.

"Ke dalla kimani shiru da maganan aurannan".

Cikin tsawa ta katse Jadidah wanda saida yasa hanjin cikin ta ya motsa.

"Ammie  wallahi Abbie ɗinan mugun ɗan rainin wayo ne wai ƙarin aure".

Faɗan Jahda da take riƙe da ƙugu.

"Kiramin Iya ta kwashe kayannan in yi abinda zuciyana ya gayamin dasu".

*TOOHHHHHFAAAA*

*GA ABBIE ZAI ƘARA AURE*

*GA JAHOOR YA DAWO*

*SHIN MAI HAJIYA JAMILA ZATAYI DA KAYAN FAƊAN KISHIYA????*

*SHIN INSUNJE GIDAN BOKA AIKIN ZAICI KUWA???*

*YA MAGANAN AIKIN DA BOKA YAI AKAN JAHIR???*

*AMSAN DA DUK WASU BAYANAI SUNA SHAFI NA GABA,COMMENTS ƊINKU SHI ZAISA MUCI GABA DA WARWARE MUKU ZARE DA ABAWA*.

PINKYBASAKKWACE.

Continue Reading

You'll Also Like

11.9K 128 37
A WOSO Oneshot book Oneshots of favourite Women's footballers Mainly the Lionesses, Arsenal Women's team,Chelsea Women's team, Man City Women's team...
90.6K 2K 49
Alissa Iris De Leรณn the daughter of both the Spanish and Italian Mafia. A week after she was born she was sent away from her 2 brothers to live with...
26.8K 3.5K 24
sแด สœแด‡ส€แด‡ ษช แด„แดแดแด‡ แดกษชแด›สœ sแด‡แด€sแดษด ๐Ÿธ แดา“ แด›สœแด‡ แดแดsแด› แด…แด‡แดแด€ษดแด…แด‡แด… ษชแด›แด  sแด‡ส€ษชแด€สŸ แดแด€แด…แด…แด€แด sษชส€โค๏ธ..สœแด‡ส€แด‡ สแดแดœ ษขแดœสs ษขแดแด› แดกษชแด›ษดแด‡ss แดา“ แด›สœแด‡ ษดแด‡แดก แดŠแดแดœส€ษดแด‡ส แดา“ แดแด˜แด› แดแด‡แดส™แด‡ส€s แด€า“แด›แด‡ส€ แด›สœแด‡ ส™แด...
32.1K 2.3K 31
ยซ แž แžนแž€ แžขแŸ’แž แžนแž€ แŸ— แžแŸ’แž‰แžปแŸ†แž˜แžทแž“แž…แž„แŸ‹แž”แžถแž“แž”แŸ‚แž”แž“แžทแž„แž‘แŸ แžแŸ’แž‰แžปแŸ†แž…แž„แŸ‹แžฒแŸ’แž™แž”แŸ‰แžถแžŸแŸ’แžšแžกแžถแž‰แŸ‹แžแŸ’แž‰แžปแŸ†แž€แŸ’แž“แžปแž„แž“แžถแž˜แžŸแŸ’แž“แŸแž แžถแž˜แžทแž“แž˜แŸ‚แž“แžšแžœแžถแž„แž”แŸ‰แžถแž€แžผแž“ ยป ยซ แžšแžœแžถแž„แž™แžพแž„แž‘แŸ…แž˜แžทแž“แžšแžฝแž…แž‘แŸแž‡แžปแž„แž‚แžปแž€ แž”แŸ‰แžถแž˜แžทแž“แž”แžถแž“แž‚แžทแžแž›แžพแžฏแž„แž›แžพแžŸแž–แžธแž…แŸ†แžŽแž„แž”แŸ‰...