A GIDANMU SUKE Labari ne aka...

Von pinky__leemart

436 31 2

A gidanmu suke littafi ne Mai tattare da dumbin nadama inda musulmi ya aure arniya batare da sanin kowa ba ga... Mehr

chapter 1
chapter 2
chapter 5_6
chapter 9_10
chapter 11_12
chapter 13_15
chapter 16_20
chapter 21_25
CHAPTER 26_30
chapter 31_35
chapter 36_40
chapter 41_45
chapter 46_50
chapter 51_55
chapter 56_60
chapter 61_65
chapter 66_70
chapter 71_75
chapter 76_80
chapter 81_85
chapter 86_100

chapter 7_8

27 1 0
Von pinky__leemart

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*🏡A GIDAN MU SUKE🏡*

®️🏝
*ZAFAFA WRITTERS FORUM* *...*📚✍🏻
[  '''Zafafa writers is a union for enlightening people to learn hottest things that relate marriage, love and religion.
Zafafa writers is a union to enlight women''']
*https://www.facebook.com/110224494006508/posts/ 110225604006397/?substory_index=1&sfnsn=mo*

                *_Z• W• F•🏝_*

MALLAKIN MARUBUTA BIYU:- 👇
*LEEMART PINKY💖*
           _DA_
*MRS BASAKKWACE*

_WANNAN LABARIN DAGA FARKON SA HAR ƘARSHEN SA SADAUKAR WA NE GA IYAYEN MU ALLAH UBANGIJI YA ƘARA MUSU LAFIYA DA NISAN KWANA,DA DUKKAN MUSULMAI BAKI ƊAYA,YA ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU TUNDAGA ZAMANIN ANNABI ADAM HAR ZUWA YAU._

*MAƘIYA AITA ACI GABA DA HAƘURI IRINSU O'O DA O'O😂*

JINJINA GA -: _MASOYAN GA MASOYAN MU GABA ƊAYA_


*PAGE 7&8*

"Har suka bar kofar gidan Jennifer Bata daina d'aga masu hannu ba Saida suka bar layinsu sannan ta daina waigensu sosai take Kuka kamar wace aka cirewa Rai juyo da kanshi alhaji Jabeer yayi yamaida dubansa gareta sosai kukanta yake taba Masa zuciya har ga Allah ya tsani yaga macce na zubda hawaye wani zafi yakeji a zuciyar'sa  shiyasa duk inda Mace take alhaji Jabeer Yana ganin girmanta sosai Kuma yana girmama mace ko wace irice balamma wannan da yake gani amanace agaresa gyaran murya yayi yaja glass din fuskarshi 'kasa sannan yace

"Jennifer This cry is enough for you to take away all your worries and I will never hurt you."

'Dago da kan'ta Jenifer tayi da rinanun idanun'ta da suka kada sukayi ja saboda azabar kukan da takeyi ta maida dubanta gareshi kamar wace zatayi magana sai Kuma tayi shuru gyada Masa kanta kawai tayi alamar tou.

Murmushi yasakar Mata yace "I love you so much Jennifer I will never let you down".

Murmushi ita tasakar Masa  tace "thanks" share hawayen idanun'ta tashigayi saboda Jenifer duk da tana arniya Amma tasan girman manya duk yanda babba yayi Mata magana bazata taba kin karbar maganar shi ba shiyasa ko agarinsu tsofafin garinnasu suke saka Mata albarka ba kamar sauran yaran garin ba.

Sosai alhaji jabeer yaji dadin yanda yaga ta karbi maganar sa ba gardama ko rashin karba murmushi yakarayi Dan daga gani yasan bazatayi taurin kaiba yasamu kalar macen da yake fatar samu gyara zamansa yayi yamaida dubansa ga alhaji Ibrahim da tuni yanan Yana lekasu ta mirror din motar sai murmushi yakeyi Dan yasan abokinsa ba abaya ba wajen iya sarrafa mace ya gwane a wannan fannin din harara Alhaji jabeer ya wurga Masa Dan yalura da irin kallon da yakeyi masu Sosa keyar kansa yayi sannan yace "ango ango".

Ango kasha kamshi mijin mace biyu na hajiya Jamila ga Kuma Jenifer duk Kai kadai Allah dai yataya riko abokina.

Murmushi Alhaji jabeer yayi saboda  har ga Allah yaji dadin wannan kirarin da yayi Masa sosai suna cikin Wannan wasan barkwancin ne har suka iso Jahar kebbi Sha'aban super market suka Fara shiga Saida yayowa familys dinsa sayaya sosai sannan yashiga mota suna Kama hanyar gida gabanshi yashiga dukan uku_uku Amma sai yadake yacije saboda tsaf ya karanchi hajiya Jamila idan taga yanayi Mata sulu_sulu shiyasa take Kara yimasa masifa suna Isa kofar gida'n sukayi Horn Mai gadi da gudunsa yazo yabude masu gate yanayi masu sannu da zuwa suna Danna kansu acikin gidan ya'yanshi suka fito sunayi Masa oyoyo Amma Banda hajiya Jamila dake bedroom dinta tana bacci bama tasan sun isoba hajiya kaka ce kawai itama tana gidan sama tana hangosu

Firfito wa sukai daga motor
inda jikin Jennifer yayi mugun sanyi bayan taci kuka ta koshi idanuwanta harsun gaji da kumbura.


Suna gafda shiga cikin gida'n inda yaran gaba daya suka fito suna musu oyoyo suna bin Jennifer da ido inda Jenifer ke sanye da weeding gown kanta lullube da veil fari  yayinda gashin kanta aka gyara shi ya kwanta a bayanta luf-luf.

Binta kawai sukeyi da kallo  Jadidah da take da kimanin  shekara takwas tace,"Abie wacece wannan munyi sabuwar y'ar aikine Abie?.

Kallon'ta yayi tare da watsa Mata mugun kallo kafin yace,"karki dameni d surutu".

Yayinda Jawahir da Jahdah Wanda kansu guda suka kafe Jenifer da ido.

"Kama hannun su Abie yayi yace mushiga ciki ko".

Yana magana Yana kallon su.

Gyada kansu sukai amma idon su day hankalin su na wajan Jenifer.

Gaba yai suka bishi a baya inda Jadida ke bin Jenifer da harara ta kasan ido harsuka shiga babban falon su  yace ma Jenifer ta zauna.


Dai-dai lokacin Hajiya Jamilah ta fito anci kwalliya an caskare kyau ga saurin Nan na gado ture kaga tsiya tana washe hakora tace,"sannu da zuwa Alhaji ", sai Idonta karaf a kan Jennifer.

Baki ta bude gaban'ta na tsanan ta fadi don tunda tai tozali da yarinyar nan gaban'ta ya Fadi,butar uba ta fada a zuciyar ta  kafin ta kuma cewa Alhaji wannan mai kayan arnan fa,bade sabuwar Y'ar aiki mukayi ba?,Ina ka samota?.


Kallon'ta yayi ya girgiza kai ya fada bedroom dinsa.

Wani kallo ta watsa ma  Jenifer kafin taja dogon tsa'ki mtsww ta juya tabi bayan mijinta.

Jenifer ko zama tayi tai tsuru-tsuru yayinda Jahadah da jawahir suka zuba Mata na mujiya sai wani kallon'ta sukeyi kamar sun saku t v yayinda  jadida  ta wuce  game room dinsu taje taci gaba da buga game.

Hajiya kaka ce ta sauko daga sama Jenifer tana ganinta ta zube 'kasa tana gaidata tace "Good evening marh" murmushi hajiya kaka tasakar Mata ta daga Mata han'nu alamar sannunta itama sunkuyar da kan'ta 'kasa Jennifer tayi sauke glass din ido hajiya kaka tayi sannan tace mata "what is your name" ?

"My name is Jennifer Daniel"

Wow nice name "which state are you from"?

"Am From Adamawa state am living in DEMSA local government"

"Okay" inji cewar hajiya kaka a takaice cewa Jennifer tayi "follow me"

"Okay marh" inji cewar Jennifer da mamakin hajiya mama yakamata yanda taga tana turanci bama gargada aciki balai kuskure biyar bayan hajiya kaka Jennifer tayi suka haura sama wani d'aki taga hajiya kaka ta nuna Mata tace tashiga aciki akwai komai acikinsa ta nuna Mata toilet da komai godiya har 'kasa Jennifer ta duka tanayiwa hajiya kaka godiya sosai hajiya kaka taji dadin yanda taga Jennifer na Bata girma tayi soboda hajiya kaka akwai son girma murmushi tayi Mata tace "kada ki damu anzama daya kishiga toilet Yanzu kiyi wanka kishirya sai akawo maki abinchi". Tana Gama fadar hakan Bata jira meh Jennifer zatace ba ta juya tayi ficewar ta.

Biyar d'akin da kallo Jennifer tayi lungu da sako maida dubanta tayi ga makeken gadon d'akin Masha Allah ba acewa komai murmushi tayi tayi tako biyu ta Isa wajen gadon ajiye jakar hannun'ta tayi ta zauna akan ga'do tana Kara 'karewa dakin kallo.

Turo kofar akayi tayi saurin saisaita nutsuwarta masu aikin gidanne suka shigo dauke da kuloli kala_kala suna ajewa agabanta gaidata sukayi a tunaninsu batajin hausa sai sukaji tace "nagode sosai"

Mamaki ne yakamasu dukansu murmushi sukayi Mata suka juya sukaja kofar dakin suka tafi saukowa tayi ta Fara bude abinchi da aka kawo Mata kala Kala rufewa tayi Takoma inda take ta zauna


********
"Alhaji kamin bayani wancan yarinya wacece,wallahi in yar aiki ce baniso ka kaima Hajiya Mama".

Atsai tsaye take maganan ba taushi balle tausasawa take wa miji magana.

Harara alhaji jabeer ya wurga Mata sannan yace "Wai Dan Allah hajiya Jamila har yaushe ne Zaki zama kamar sauran matane ? Ke shikenan bakisan yanda zakiyiwa mijinki magana ba cikin ruwan sanyi ba kullun sai dagawa mijinki da hankalinki kikeyi Dan Kinga Ina d'aga maki kafa bafa tsoronki nakeji ba kawai Ina daga maki kafane wallahi".   Dan Allah Dan Annabi alhaji kada ka dagamun kafa kayi ta jibgana shikenan banida damar tambayar ka Dan Naga kazomun da wata arniya diyar kafirai Mai warin najasa  acikin gida tou wallahi sai kagayamun a inda kasamota Dan naganta da irin shigarsu ta arnaye idan zasuyi aure.

Wani kallo alhaji jabeer yake binta dashi juyawa yayi ya janyo tawol dinsa yacire kayansa zaishiga toilet Kennan ta shige gabansa tana cewa "wallahi alhaji bazaka shiga wanka ba sai kagayamun inda ka samota ce Mata yayi "kome Kenan hajiya kaka zatayi maki bayani" Yana Gama fadar hakan ya tureta gefe yashigewarshi toilet ya rufo.

Zage zage hajiya Jamila tafara da cin mutunci inda take shiga banan take fita ba kamar ita da sa'arta Saida tagama cin mutuncinta sannan tabar Masa d'akinsa ta wuce nata tana Dan neman masifa.

********
Hajiya Mama tasa an gyara ma  jennifer  part ɗin dake gefen nata  ta shiga tai wanka.

Hajiya Jasmien ta kira matar ɗan autan ta,wanda yara suke kira da aunty amarya ta ce ta kawo mata kayanta kafin asayo mabaƙuwa.

Hajiya Jasmie tunda taga Jennifer taji ta shiga ranta sosai da sauri ko taje ta kawo mata kayan nan suka zauna suna ta hira,duk da jennifer bata wani sakewa dasu,itako sai jan ta take a jiki harta fara sake jiki.

*******
Ƙarfe takwas da mintoci kowa ya hallara a dianing room ɗin gidan ɗan ƙasa yaran da iyayen.

Jennifer kanta a ƙasa abincin ma kaɗan-kaɗan takeci.

Inda kowa na gidanan kusan hankalin sa na kanta.

Alhaji Jibril Ja'afar Ɗan ƙasa babban ɗan Jaafar ɗan ƙasa ne yake ƙoƙarin miƙewa shida mai ɗakin sa Hajiya  juwairiya  mahaifiyar  Jaheer   da jawahir  su kaɗai  Allah ya basu ,inda Jaheer  bai ƙasan yana Germany yana karatun masters digree ɗin shi a fannin kasuwanci.

Hajiya Mama kallon su tayi cike izza da taƙama tace,'Abban yara kuzauna akwai abinda zamu tattauna yana da mahimmanci kowa yaji ya saura-ra".

Komawa yayi suka zauna  da shi da hajiya Juwairah    .

Bayan kowa ya kamala cin abinci ƴan aiki sunzo sun kwashe komi  sunkai kitchen.

Hajiya Mama tai gyaran murya ,hankalin kowa ya koma gareta.

"Dafarko dai kunga baƙuwar fuska acikin mu wanda bakusan wacece ba".

Shiru tayi ta zuba ma Jenifer ido ,yayinda jennifer kanta na ƙasa gabanta na tsanan ta bugu.

Hajiya  Jamila hakanan kawai taji gabanta ya yanke ya faɗi  ,a firgice take kallon Jennifer.

Hajiya Mama taci gaba da faɗin,sunan ta Jennifer  amaryan Jabeer ɗana,a hanyar su na dawo daga damaturu Allah ya haɗa shi  da ita ya aura".

Hajiya Jamila a wani tsorace tatashi  tana zazzare ido tare da dukan ƙirjinta da hannu tai baya zata faɗi  ,Abie yai saurin taro ta ta faɗa jikin sa.

Hajiya Mama da kowa hankalin shi ya koma kansu,don duk cikin  su babu wanda hankalin shi bai tashi ba da maganan Hajiya Mama.

Azabure Hajiya Jamila ta miƙe ta shaƙo wiyan Jennifer ta shaƙare tana ihu da kururuwa da ƙƴar Abban  yara da Hajiya Jasmie  suka ƙwaceta ,idonta duk ua firfito don ba ƙaramin shaƙa tai mata ba.

Abie ko kasa taɓuka komi yayi.

Jamila kashe ƴar mutane zakiyi don kinga ba ƙabilar ku ɗaya ba?,Jamilah kiji tsoron Allah ashe baki da imani haka,wallahi Jamila kika ƙara taɓa yarinyar nan sai kinga abinda zan miki  ,sannan da amincewa ta aka auro yarinyar nan,sannan ba wanda zai tilasta mata,ni na isa da ƴaƴan da na haifa in ku surukaina ban isa da kuba".

Ahasale rai ɓace Mama ke maganan.

Kowa shiru yayi yai tsuru-tsuru,don sun daɗe basu ga ɓacin ran Hajiya Mama ba irin na yau ba,shiyasa kowa ya shiga hankalin shi.

"Wallahi Hajiya bazan zauna da kishiya ba,ke miyasa surukar ki bata amince an miki ba,sannan uwata itama ai bata da kishiya,don haka bazan zauna da kishiya ba,kishiyar ma arniya".

Cike  da rashin kunya take maganan.

Jasmie tayo kanta zata fara magana,don bata ɗasawa da duk matan gidan , bata biye musu sam harkan gabanta kawai takeyi.

Da hannu Jalal ya gwadata,kasan kasancewar tana mugun tsoron mijinta yasa tayi baya tayi shiru.

"Rashin kunyar naki yakai kizage mahaifiyata a gabana Jamila?.

Ranshi ɓace yake maganan,kafin yaci gaba da faɗin,"Jamila kij.......!

"Dakata Jabeer karka sake ka saketa kabarta ta zauna ta ƙunshe baƙin ciki,don dole sai ta zauna da kishiyar da bata so".

Jamila shewa ta buga tare da tafa hannaye tace,"wallahi sake ni Jabeer in ka sakeni tafi nono fari,mai ake da maciyi amana,Allah ya tsine ma aurena dakai tunda kai min kishiya,nan idonta ya rufe ta rinƙa zuba ruwan rashin mutunci ga Hajiya Mama ta hana kowa ya tanka mata.

Daga ƙarshe ɗaya bayana ɗaya suka watse suka barta.

Jabeer bin amaryan shi yayi ɗaki suka kashe boos  a daren.

Jasmie  ko taji daɗin wannan kishiya da akai ma Jamila.

Don Jamila kullum maganan ta bata ba kishiya,yin kishiya sai ɗan gado,wato wanda uwar shi keda kishiya habaicin da kullum take ma Jasmie kenan kasan cewar matan baban ta huɗu ne.

Tundaga wannan lokacin  Jamila ta dasa kujeran rashin mutunci, ta koya ma ƴaƴanta salo-salon  rashin mutunci su rinƙa ma Jennifer,hata Hajiya Juwaira da Hajiya Jumaina suka ƙara dasa ƙungiya,inda suke Jennifer ma bata isa ta zo ba,part ɗin su sai na Hajiya Jasmie kawai take zuwa.

Jawahir Allah ya ɗaura mata son Jennifer kullum tana liƙe da ita inde ba  tana makaranta ba,Hajiya Juwairah tayi bugun amma  ina a banza harta gaji ta ƙyaleta.

Duk ranan girkinta itake abinci da kanta basai ƴan aiki sunyi ba,tou ranan matan gidan da ƴaƴan su basa ci,Jawahir kaɗai keci,da Abie zaima Jamila magana,Hajiya Mama ta hana ƴaƴanta duk suyi ma matan su magana.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi ba daɗi,wata rana farinciki wata rana baƙin ciki,duk ranan sunday Alhaji Jabeer da kanshi yake kai   ta church dake maƙeran gwandu dake birnin kebbi,abinnan ƙara ƙona ran Hajiya Jamila yake,don Alhaji bai taɓa tuƙata a motor ba koda suke soyayya driver shi ke tuƙata,amma ace wannan arniya shike kaita coci.

Shirye shirye ake gidan na dawowan  Jaheer ƙasan,Hajiya Juwaira sai murna take haka ƴan ƙannan shi.

Ƙarfe huɗu driver yaje ya ɗauko shi a filin jirgi ya kawo shi gida ,bayan yayi wanka yayi sallah yaci abinci,kafin ya kwanta ya ɗan yi bacci.

Bayan ya tashi ya ƙara wani wanka yasa kaya ya feshe jikin shi da turaruka kafin ya fita side  ɗin Hajiya Mama mahaifiyar mahaifinshi.

Hajiya Jasmie da Jennifer na zaune sun sata a tsakiya sai hira suke ya shigo ya gaida su.

Ɗan taɓa hira suke amma hankalin shi na gun Jennifer don bai santa ba.

Mama ce ta dube shi tace,"itace amaryan Abien ku sunan ta Jennifer".

Ɗan waro ido yayi kafin yace,"Woow yaushe Abie yai aure ban sani ba?.

"Kimanin wata uku kenan da yayi aure".

"Allah sarki Allah ya basu zaman lafiya".

Kafin daga bisani ya miƙe ya shiga duk sauran part ɗin iyayen nashi.

Yanayin yanda yaga ana tsangwaman jennifer a gidan sam abin bai masa daɗi ba,shiko baiga aibun ta don ba wanda zaice ba musulma bace yanayin shiganta har tafi su Hajiya Jamila shigar mutunci.

Alhaji Jabeer ya shirya harda hajiya Mama da Jaheer da Jasmie da JENNIFER  suka je ƙauyen su jennifer an musu tarba irin ta mutunci kwanan su uku suka dawo da tarin tsara,iyayen ta sunyi farincikin ganin ƴarsu ta canja ,Alhaji Jabeer ya musu alƙawarin turo motor a zo a ɗauke su har gida akai su sokoto.

Bayan wata huɗu da auran Jennifer da Jabeer ciki ya bayyana ajikinta inda ran Hajiya Jamila yai baƙiƙirin ya ɓaci,tafara sheganta cikin da ita da ƴan fadan ta,yayinda Jabeer bai ce mata komi ba don yasan yanda ya samu matar sa,don haka bazai taɓa zarginta ba.

Bayan wata tara Allah ya sauketa lafiya inda ta haifa ƴan biyu masu kama ɗaya sak,iyayen ta sunso akaita gida   amma Hajiya Mama tace ina abarta anan Yayarta Tina tazo ta zauna da su,rananan suna yaran suka ci sunan Juliet  da jesica,ita ta zaɓa sunan da aka sa ma ƴaƴan inda Alhaji Jabeer yace bazai tauyeta ba in sungirma suna shaawan musulinci sai musulinta.

Haka taci gaba da renon ƴaƴanta Jasmie  na tayata da hajiya mamah.

Suna da shekara ɗaya  da rabi,dare ɗaya Allah ya saukar ma Jennifer da ciwon ciki na ajali wanda bata kwana ba rai yayi halinsa,inda akaba ƴan uwanta sukai mata jana'iza yanda sukeyin nasu .

Hajiya Mama,Abbie Jasmie ,jaheer jawahir su akai ma mutuwa sunji mutuwar sosai don duk saida sukai ciwo,musamman Abie don ladabi da biyayyanta kawai yake tunawa,yaso ace ta musulinta kafin ta bar duniya da ko makawa babu aljanna zata shiga,don yanda tai biyayyan aure yanda bai taɓa tsammani ba.

Tundaga nan riƙon su Jesica ya koma hannun kakanin su,inda da ƙyar Abie ya bar musu su,saida Mama tasa baki ya barsu,amma duk wata yana hanyan adamawa wani lokaci a jirgi wani lokaci a motor haka yake zuwa yai kwana biyu ya wuce yai musu shatara ta arziki  ,basu tashi dawowa gidan ba sai da suka kai shekara  ashirin.

Inda aka dasa tsanhwama su  fiye a wanda akai ma uwarsu,wajan Jaheer kawai suke jin daɗi da Hajiya Mama da Hajiya  Jasmie sai Jawahir da take nuna musu ƙauna,saɓanin sauran ƴaƴan da basa tank mutuncin su wulaƙanta su kawai suke.

_WANNNAN KENAN_

*CIGABAN LABARI*

MORE COMMENTS
MORE TYPING

*IT'S PINKY BASAKKWACE*

Weiterlesen

Das wird dir gefallen

139K 5.6K 69
โžฝJust short love stories...โค โ‡โค๏ธ. โ‡๐Ÿ–ค. โ‡โ™ฅ๏ธ. โ‡๐Ÿ’™. โ‡๐Ÿฉท. โ‡๐Ÿค. โžฝ๐Ÿ’›Going on. โžฝ๐ŸฉตComing up [Ignore grammatical mistakes. I will improve my writing gradual...
109K 3.3K 25
A fire incident at his(Kim Jae-soo) husband's home while he (Baek Ji-Hu )was away made Kim Jae-soo return to his third year of university (he was reb...
70.3K 4.9K 54
Shubish oneshots because why not. Mainly fluff with a little angst on the side. Ps- I wanted to write like a long story but I lack a good main plot a...
28.1K 623 4
ู…ุฏูŠู†ู‡ ู…ุจุงุญ ููŠู‡ุง ูƒู„ ุดูŠ ุจุงู„ุงุถุงูู‡ ุฅู„ู‰ ุงู„ู…ุดูŠ ููŠ ุงู„ุดุงุฑุน ุนุฑุงู‡ ุงูˆ ุญุชู‰ ุงู„ู†ูŠูƒ ููŠ ุฒู‚ุงู‚ ุงู„ุดูˆุงุฑุน ูˆ ุฃู…ุงู… ุงู„ุนู„ู†