BABI NA DAYA

8.9K 385 5
                                    


NI'EEMA
Zulaiha Rano

1
Cikin sauri ta shiga gidan idonta taf da hawaye, hannunta rike da jakarta ta makaranta, budurwa ce wacce ba zata wuce shekara goma sha biyar ba. Kai tsaye wurin Maminta dake zaune a ɗaya daga cikin kujerun falon nufa tare da fashewa da kuka. Mamin tsayawa ta yi tana kallonta sai dai ba ta ce komai ba har ta yi mai isarta sannan tayi shiru, a hankali Mami ta kai hannunta tana share mata hawayen sannan ta fara magana "Yau me ya sami Ni'eemata take irin wannan kukan? Bayan ta yi min alƙawarin ta daina kuka a kan ƙaramin abu?"
Tashi ta yi ta zauna tare da kallon Maminta ta ce "Mamina dole ce tasa na yi kuka a yau, kina jin fa duk yaran gidan nan sun dawo daga school ni kuwa can suka baroni, domin cewa suka yi babu waje a motar alhalin kuma akwai wajen, sam! Ban damu ba na taho a ƙasa idan da sabo na saba da halayyar su, abin da ya fi ba ni haushi ina shigowa su Maryam suka fara yi min dariya habaici, ban dai tankasu ba na cigaba da tafiya burina na iso sasanki don na gaji yunwa nake ji, ban ankara ba sai jin saukan mari na yi a kuncina, ina ɗagowa sai na ga Suhaila ce ta ɗaura da ce min ai ni "Shegiya ce agola wacce ba ni da uba, wai da cikin shege a ka haifani." Ta dire maganar tana tsananta kukanta.
"Amma me nake faɗa maki kullum? Ba na ce ki daina damuwa da duk wani abu da za su faɗa maki ba? Shi kenan ke kin fi son kina rayuwa cikin ƙunci a kan abin da ba gaskiya ba ne?" Mami ta yi tambayar tana tsare Ni'eema ido.
"Wallahi Mami da sam! Ba na damuwa da maganar su, amma yanzu kam dole na damu don har a school haka suke cewa kawayena ba a san Abbana ba, don Allah Mamina ki yi haƙuri da gaske ne bani da uba? Ni din shegiya ce kamar yadda suke faɗa?" Tun kan ta kai ƙarshen maganar ta hawaye suka wanke fuskar Mami, ta kasa furta komai sai hawaye wani na koran wani.

Jikin Ni'ima ya yi sanyi ƙalau hankalinta ya yi masifar tashi, da ganin hawayen Maminta, muryar ta na rawa ta ce "Mamina ni ce na ɓata miki rai ko? Don Allah ki yi haƙuri kar ki yi fushi da ni wallahi ba zan ƙara saka ki kuka ba, kuma In sha Allah ba zan kuma tambayarki ina Abbana yake ba, ki daina kuka please Mamina." Ta ƙarasa maganar tana share wa Mami hawaye.
Murmushi Mamin ta yi fuskar ta da sauran hawaye ta ce "Sorry my Baby ba ke ce kika ɓatan rai ba hasalima tausayinki ya sani kuka, haƙiƙa kullum cikin tausayawa rayuwarmu nake yi, na taso cikin rashin gata haka na haifeki a rashin gata ki kai rayuwa cikin rashin gata, amma duk da haka ba zamu butulcewa Allah ba, don yana sane damu kuma zai kawo mana ɗauki cikin rayuwarmu, fatana ki cigaba da addu'a komai tsanani yana tare da sauƙi, kwana kadan laƙanin sunanki zai bayyana a garemu.

Murmushi Ni'eema ta yi cikin jin daɗin bayanin Maminta ta ce "To Mami Allah ya tabbatar mana da Alhairi."
"Amin my daughter tashi maza ki je ki cire uniform kici abinci, gashi har lokacin Islamiya ya gabato." Tashi Ni'eema ta yi tana faɗin " Mami me kika dafa mana ne yau?"
"Doya da miya, na san kuma kina sonta sosai ko?" Mami ta bata amsa cikin jin dadi.
"Yes Mami bari nazo na sankameta." Ni'eema ta gama maganar tana nufa bedroom ɗinta.
Girgiza kai kawai Mami ta yi cikin tsananin son 'yarta, haƙiƙa Allah ya bata 'ya mai hankali da nutsuwa uwa uba kuma ilimi. Tana wannan tunanin Ni'eema ta dawo hannunta ɗauke da plet da kofin drink, zama ta yi tare da yin Bismilla ta soma cin abincin ta cikin nutsuwa.
" Tun da naga kin sami nutsuwa anjima idan kika dawo school zan baki labarin Abbanki." Mami ta faɗa tana kallon Ni'eema.
Wani tsalle Ni'eema ta yi cikin murna sai gata gaban Mami ta ce "Da gaske Mamina? "
"Eh in sha Allah." Mamin ta tabbatar mata.
Ganin lokacin islamiya ya yi ya sa ta koma wajen da abincinta yake, ta ci gaba da ci cikin sauri-sauri don kar ta yi latti, ƙarfe uku 4:15 pm ta kammala shirin ta sannan ta fito, a lokacin Mami ta shiga bedroom don haka can ta bita tana faɗin "Mamina na gama shiyawa zan wuce?"
"To Ummyn Maminta ga kuɗin transport nan ki ɗauka Allah ya tsare ya bada sa a ki kula ki kama kanki."
"In sha Allah zan kula" Ni'eema ta yi maganar tana kama hanyar fita. Ni'eema dai Yarinya ce kyakkyawa doguwa ce kuma fara, tana da dara daran idanuwa kuma farare, tana da yalwataccen sumar kai dana gira, yarinya ce nutsatssiya mai hankali, ita ce 'yar fari wajen Maminta sai ƙannanta maza su biyu. Asalin sunanta Khadijah sakamokon ta ci sunan Kakarta ne Maminta ke kiranta da Ni'eema tarbiyya mai kyau Mami ta ba 'ya'yanta.

Ƙarfe shida aka tashe su daga makarantar, bata ɓata lokaci ba ta sami Nafef ta yo gida, tana shiga su NAZIR DA SAGIR wato ƙannanta suka dawo, don dama in suka tafi makaranta sai 6pm ake tashinsu.
Da sauri suka isa gareta tare da rungumeta suna faɗin, "welcome back Aunty." Shafa kansu ta yi tana faɗin "Yawwa ƙannaina ku ɗin ma sannunku da dawowa fatan kun yi karatu lafiya?"
"Lafiya Lau." Suka bata amsa sannan suka nufi hanyar sashinsu.

NE'EEMA COMPLETEWhere stories live. Discover now