BANI BACE

405 24 4
                                    

*BANI BACE




INNOCENT MARA LAIFI






ELOQUENCE WRITER'S ASSOCOATION




Basira Sabo Nadabo





Wattpad
@
Basira_Nadabo








Ina gaida duk masoya na a faďin duniyar nan kuma naji daďin yadda kuka kasance tare da 'Yar Nadabo ina godiya a gare ku, indan nace ku, ina nufin ni, indan nace ni, ina nufin ku, Nagode sosai bisa addu'oin ku gare ni gashi yau bisa yardan mai Sama zan aje biro na, ina fatan duk wani MUGUN MASOYI yayi hakuri yaso masoyiyarsa yadda taso shi mun daiga yadda rayuwar S.Man ya koma, kamar yadda na fad'a da farko bawai labarin duka bane k'irk'irarre A'ah akwai wani shashi a cikin labarin yafaru da gaske, Naji dadi dana fara da BISMILLAH kuma gashi In Shaa Allah yau na gama da ALHAMDULILLAH. Basira Sabo Nadabo tana godiya Wato na yarda da kalmar Ana Mugun Tare like Taren Tare. Onelurv❤



Dedicated To My Ramalurv durlin





13/08/2017



SHAFI NA ASHIRIN DA TARA DA TALATIN




Ke dai bari kawai Hiedat Allah ne yayi hakan amma bayin kaina bane, kuma Allah ne ya bamu hanya tare da karfin addu'a mun tashi da addu'a dani da Baban ki kawai ina zaune sai ga Umman Sulaiman tazo bayan mun gaisa shine take cemin itafa tana zargin dasa hannun Sulaiman a kisan Yariema don bata yarda dashi ba, shine nake ta bin sahunsa, har ranar daya zo gurinki na farko a gidan yari, bayan ya sallame ki, ina labe a bayan sa suka keb'e da dauda yake ce mawa dauda ya tabbatar kin amsa cewa kece kika kashe Yariema ke Hiedat duk wani movement dinsa nake bibiyar sa, kuma nasa akasa masa ido tare da taimakon boshe, ta bata labarin yadda suka had'u da bala da taimakon da tsohon nan yayi mata, sannan ana gobe za'ayi zama na biyu aka nemi Sulaiman aka rasa ashe yaje ya buya ne saboda baya sonki fito, Hiedat nasha wuya kafin na gano inda yake, sai boshe ne ya kawo shawarar muje MTN Office ya kira garus akan wani aiki suka samu kuma ba karamin kud'i zasu samu ba shine fa akayi tracing d'in inda suke muka kama su, munyi munyi su fad'a mana wanda ya sasu suka ki Sulaiman yasha wuya amma yaki amsa laifin sa, shine da mukazo kotu nayi musu dabarar hadasu da bala uban bayani, kuma suka fad'a amsar cikin sauki

Nayi dariya nace lallai ya cika uban bayani, wato Umma daman S.Man ba sona yakeyi ba Mariya yake so, hmm aiko gashi tayi biyu babu ko ďaya, babu Yariema babu S.Man

Toh Allah ya kyauta ai tayiwa kanta kuwa, yanzu kije ki kwanta gobe zamu karasa, gurin mijina zani

Umma kice ina fushi da mijinki tunda yaki zuwa muyi hira

Haba ďiyar Baba kar kiyi fushi da Baba, Baba ya gaji ne ga mutane sai zuwa Allah ya kyauta sukeyi masa

Toh na hakura, na daina fushi da Baba na

Yauwa koke fa, toh mukwana lafiya ďiyar Umma

A'ah ni ďiyar Baba ney

Au shagwabar ce ta motsa ko, toh yanzu kin girma sai dai 'ya'yanki da Yariema

Oh'oh na fad'a tare da rufe fuska

Ta fita tana dariya

Ina kwanciya wannan barawon ganin iya satan mutane yayi awon gaba dani, bacci nayi wanda na daďe banyi ba don saida Ummata ta tashe ni da asuba

Haka jama'a sukata tururuwan zuwa har ahayarin gidan sarki sunzo tawaga guda tare da kayan aure na, anyi wasa tare da barkwanci, an sanya aure na sati biyu masu zuwa saboda Yariema zai koma ya cigaba da amsar magani, ba zama kullun muna cikin hidima babu tashar yaďa labarai da basu sanar da aure na da Yariema ba, Kadunaw, Kano Taraba ke faďin kasar nan ko ina an sanar, saboda biki na farko kenan a gidan sarki, ranar kamu ne guri ya cika, anata hada hada kuma a ranar za'a fito dani daga inda aka killace ni tun ranar da akasa aure na da Yariema aka killace ni a ďaki guda bana komai, ina fitowa naci karo da fuskar da bazan taba mantawa dashi ba da gudu muka rungume juna sai kukan farin ciki bayan munyi mai isar mune kowa sai sa mana ido sukayi, na ba zeenert labarin abinda yafaru bayan an rabamu tare da yadda Ummata ta gane S.Man ne mai laifi, itama ta sanar dani yadda akayi ta fito a gidan yari kamar haka

Bayan an rabamu na fiskanci matsaloli da dama kuma babu wanda zan fad'awa naji daďi ana cikin haka sai ga wannan barrister nan daya taba zuwa shine ya kara dawowa da kyar na yarda yasa maganar a kotu, ashe Abba bai mutu ba kuma kin san waye ubana

A'ah

Hmm Alhaji Abba

Ahh Don Allah

Wallahi, kedai bari Hiedat Alhaji Abba shine ya haife ni niba 'yar zina bace, bayan ya aure ta daya tabbatar tana da ciki shine ya gudu wai saboda 'ya mace duk rayuwarta wahala ne, shine ya dankara mata saki uku, toh bayan ta haifeni a gurin wata tsohuwn da take zaune da ita, bayan haihuwa na ta nemi hanyar da Abba na yake yawan bi saita ajiye ni akan bola sannan ta labe har saida ta tabbatar daya dauke ni sannan hankalinta ya kwanta, tare da wasika ta ajiye ni akan di 'yarsa ce amma da yake idonshi ya rufe da son yara shi yasa bai gani ba Ummata ce taga wasikar kuma wannan wasikar itace ta fiddani a kotu kuma wannan barrister d'in mijin Ummata ne yanzu haka ina hannun Ummata don bazan iya zama da Abba na gida ďaya ba, kinji takaitaccen labari na

Gaskiya kawata kin auna arziki kuma na miki murna kasan cewarki 'yar sunna ba yadda kike tunani bane Alhamdullah, sai mu tashi mu shirya wai ma tsaya, ya akayi kikaji auren da kuma yadda kika gane gidan nan

Hmm kawata kenan ina zaune jiya ina kallon labarai sai naga an hasko ki keda Yariema da farko ban yarda ba sai na kara gani a labaran fulani bayan tivie sun gama nasu harda address shine fa na fad'awa mama daman tasan da labarinki sai ta bani izini nazo shine kika ganni anan tare dake

Toh yanzu dai tashi ki shirya saboda 'yar mama mai makeup tare da fiedoo duk makeup ne aikin su kuma sun san kan aikin su, kije a fara miki kafin ni na gama

Haka aka tsantsara mana kwalliya kamar bazamu wanke bay, biki yayi biki anyi barin nairori, ado gwanja tare da Isaz M Sheriff sune suka wake mana amarya da ango, naga group da yawa sunzo taya Wahiedat murna , ga Fiedoo novels group da marubuta tare da wanda ma ban ambata ba duk na gansu, su Hauwa Abdullah Sarki sai wani tusa kaji takeyi ajaka ni harta bani kunya saboda a kusa dani take zaune, ga maryam mangal haba kuyi abu Irina classic ladies mana, a cikin abokan ango ne Yariema ďan sarkin zazzaun shima suka kulla abota da zeenert sosai suka shaku, an kai amarya kuma sarki ya amsheta tare da yafa mata alkyabba, bayan tarewa da sati biyu ne amarya da ango suka ďaga sai birnin landan garin masu jajayen kunne.

Muma anan sai muyi musu fatan alkhairi tare da zaman lafiya, suna sauka nima ruwan biro na ya kare.


TAMMAT BI HAMDULILLAH

Allah Nagode maka na kuma Gode maka daka bani ikon farawa lafiya kuma na sauke shi lafiya, Jinjina da yabo su kara tabbata ga MANZON ALLAH, Habibullah, Shafi'ullah Ya Muhammadur Rasulillahi Sallahu Alaihi Wa Sallam.


Sai kunji ni a sabon littafina mai suna ABINDA KA RAINA hausawa sukace shike tsole maka ido,, Nagode masoyan Basira Sabo Nadabo



Wattpad
@
Basira_Nadabo

07/08/2017. 11:45. Am


Karku manta dai

Karamar Su Babban Suce Ni Wato 'Yar Mutan Kd Ce

Basira Sabo Nadabo


Please always Vote and comment

Thanks


Eloquence Writers Association

BANI BACE Where stories live. Discover now