BANI BACE

186 21 0
                                    

*BANI BACE

     INNOCENT MARA LAIFI



*ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION





Basira Sabo Nadabo




Ina sonku kawaye na

Maryerhm Ishaq

Zee Maryam

Ummu Ramlah

Ummu nadiyya

Aunty Baraka

Allah yabar zumuncin Amin Ya Allah

Sis Respectable, I Salute You my love


_Dedicated to Ramaluv_



2/08/2017



SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI


A ranar alhamis yayi dai dai da bikina sauran kwana takwas na dawo daga amso dinkunan da zansa ranar bikina, a dai dai United bus After Breweries Nigeria PLC na hadu da Yariema ina kokarin yi masa bayani sai wani yazo ta bayan shi ya caka masa wuka, amma wallahi ban kashe shiba, ku yarda dani wallahi BANI BACE

Bayanin me kike kokarin yi masa kenan

Na share hawaye na, ina kokarin yi masa bayani ne akan yayi hakuri inhar ni matar sace zai aure ni, in kuma niba matar sa bace bazai aure ni ba saboda ance matar mutun kabarin sa

Malama Wahiedat ya akayi mutanen dake gurin sukaga lokacin da kika soka masa wuka, kuma gashi yanzu kuma kince bake bace kince wani ne, haba wannan ma bayanin naki hankali bazai dauka ba, ko kuma zaki ce mana ba kece wahiedar da aka gani tare da yariema ba a wannan lokacin?

Nayi shuru bance komai ba

Yayi tattaki zuwa gaban teburin su ya dauko wuka a cikin farar laida yace ya mai girma mai shari'a wannan shine wukar da Wahiedat Abdullah ta kashe Yariema Abbas, ya mai shari'a ko wannan shaidar ta isa ya yankewa Wahiedat Abdullah hukunci ba tare da an wahalar da shari'a ba nake so kotu tayi duba da lamarin ta yanke hukunci ba tare da batawa kotu kuma tare da ayarin mai martaba lokaci ba, nagode ya mai shari'a daga haka kuma ya koma ya zauna ya cigaba da dube duben sa

Barrister Sulaiman ko kana da abin cewa

Barrister Sulaiman ya mike tare da gyara zaman gilashin dake fuskar sa yace ya mai girma mai shari'a, inaso a duba al'amarin wannan baiwar Allah bai kamata ta amsa laifin daba itah ta aikata ba alhali bata furta da bakinta ba, ya kamata aga wa'anda suke gurin abin yafaru a gaban su, su faďa ma kotu itace ta aikata kuma tare da shaida mai karfi,  da wannan nake rokon kotu data ďaga sauraran wannan karar zuwa wani ďan lokaci ya mai shari'a, nagode da haka yayi sallama ya koma gurin zamansa

Alkali yayi rubuce rubucen sa sannan ya ďago kai yace bisa hujjojin da barrister'n me kara ya bayar, kotu tayi duba da nazari mai nisa ga al'amarin kotu ta ďage sauraran wannan kara izuwa talatin da ďaya ga watan 7 shekara ta 2017, alkali ya bubbuga gudumar sa kowa ya mike, alkali ya fita sannan kowa ya fara fita, nima sojoji suka ingiza keyata cikin bakar motar su, ina kalan Ummata da Babana amma ba daman nayi musu magana haka, ina kallan su har muka fita a kotun, muna isa suka jefar dani suka cigaba da bani gwale gwale gashi sun rabani da Muzeenat balle ta bani hakuri ko zanji dadi....... Yau sauran sati ďaya a koma kotu kuma kullun sai S.Man yazo duk bayan kwana biyu yana tambayata amma kullun amsar itace BANI BACE na kashe Yariema, har ta kama yau litinin 31 ga watan bakwai shekara ta 2017, kowa ya hallara amma banda barrister Sulaiman, abin yayi mugun ďaure min kai, shikenan zasu lakaba min laifin da banawa bane, na fashe da kuka mara sauti babu abinda nake bukata sai mutuwa ta ďauke ni saboda asiri na ya gama budewa bani da sauran hanyar kubcewa saboda S.Man shine wanda na dogara dashi shima gashi baya nan, babu mai kareni sai Allah, amma kuma bana son mutuwa ta ďauke ni har sai gaskiya tayi halinsa saboda nasan Allah bazai taba tozarta niba ina tare da Allah kuma shine zai kare ni, ya Allah gani a hannun ka wanda na jin gina dashi gashi shima bai zoba oh ya Allah ka kareni Ya Allah, har alkali yazo barrister Abubakar ya gabatar da shaidun sa kuma ya roki alkali ya yanke min hukunci dai dai da laifina

Alkali yayi rubuce rubucen sa, ya ďago kai yace bisa dogon nazarin da kotu tayi ta kara ďaga wannan zama har zuwa 17-08-2017 saboda rashin halarta mai kare me kara, alkali ya buga tebirin sa kowa ya mike alkali ya fita, yan zaman kotu sai tofin ala tsine suke min wasu suce bani da laifi wasu kuma suce laifina ne don kawai mutun yace baya sona shine na kashe shi, magana kalala har na isa mota ina kuka mara sauti a haka muka isa gidan yari


*Shafin babu yawa kuyi hakuri dashi nagaji ne

_Masu korafi kuyi hakuri, labarin babu yawa In Shaa Allah na kusan saukewa karku damu, kudai ku cigaba da bina

*Eloquence Writers Association


Karamar Su Babban Suce Ni Wato 'Yar Mutan Kd Ce

      Basira Sabo Nadabo


Follow Me And Vote My Story On Watpad @ Basira_Nadabo

BANI BACE Where stories live. Discover now