BANI BACE

207 16 0
                                    

*BANI BACE



INNOCENT MARA LAIFI




ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION



Basira Sabo Nadabo


Wattpad
@
Basira_Nadabo






Wannan shafin nakune Readers d'in *BANI BACE* a duk inda kuke ina alfahari daku Allah yabar mu tare Amin Ya Allah. Basira Sabo Nadabo tana godiya, Ana mugun tare like taren tare Onelurv





Dedicated To My Ramalurv



12/08/2017



SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI DA TAKWAS


Kaji kunyi kuma wallahi bazan taba yafe maka ba MA YAUDARIN MASOYI, zaka gamu da karshe ka kuma In Shaa Allahu azabar da Allah ya tanarda ma yaudara irinka azaba ne mai tsanani kuma wallahi Allah bazan taba yafe maka ba, ta fashe da kuka, aka wuce dashi

Sai ga Kopir dauda, Ummata tace aina fad'a maka saika rasa aikin ka macuci an dauke ku aiki tare da rantsuwar kare hakkin al'umma babu cin amana amma sai kuci amanar kanku kuna tunanin gwamnati kuka cuta kanku kuke mawa, gwamnati tana iya iyawarta don ganin baku wulakanta ba amma sai kun san yadda kukayi kuka wulakanta kanku da kanku, sannan abin bakin ciki saiku zaga baya kuna zagin gwamnati kuma in za'a bincika ire irenku kune kuke fara zagin gwamnati kafin civilian suma su fara, gadai ishara nan akan dauda ko kunayi a boye watarana sai asirinku ya tonu, ruwa cikin cokali ya ishe mai hankali wanka, ku tafi dashi ga rashin aiki ga gidan wuya zaka ďanďana abinda kayiwa 'yata

Ummanmu rabu dasu Don Allah, umma mun gode sosai da kika kubutar min da farin cikin rayuwata niko a gobe ma a daura ina sonta a haka ni tsoron naija nakeyi kuma Ummanmu

Kai Yariema tuwon gidan ku, ko kunya ta bakaji irin na sirikai ko

Hajia in kun gama wannan shirmen sai kuzo mu koma gida gashi can gida ya cika makil saboda an haska wannan shari'ar a gidan TV na AIT da LIBERTY tare da DITV, sai kirana akeyi Don Allah kuzo mu tafi

Yan zaman kotu sai murna suke min kowa kagani cikin farin ciki da annashuwa saboda an rage mugun iri a doron kasa

Muna isa gida naci karo da motar gidan Aunty Cute, Zarah Bukar group tare data Sis Khadija Candy, da Hausa Novels Only da Aunty Rufaida Omar kai harda Aunty Rashida Kardam daga gefena kuma motar kungiyata na hango wato Eloquence Auta sai ďaga min hannun yakeyi

Ummata tana ta washe baki saboda irin karar da group's dina da kungiyata suka min na tayani murnar kubuta daga mugun zargen S.Man

Muna shiga ciki kowa sai murna da san barka donba yin Ummata bane Allah ne kawai ya kubutar dani, kowa so yake yaga ya sani dariya cikin su Aunty Cute na shige sai hira mukeyi, group d'in Maryam Ameen Musa ma ba'a barsu a baya ba da SISIN MAMA tare da group d'in Aysher Sada Machika da Anielurv group kai kowa nagani a gidan su Hiedat, bayan kowa ya tafi da karfe 11:00 Am muna zaune ni da Ummata labarin irin gwale gwalen da nasha harda labarin kawata Muzeenat ta tausaya mata tare da fatan itama ta fita daga wannan gidan, Ummata ta bani labarin irin wahalar da suka sha kafin ma a amsa karar a kotu nace

Umma wai ya akayi kika gane S.Man ne ya aikata hakan kuma har kika samo shaidodi a cikin kan kanin lokaci ba tare da kinsha wani wahala ba duk da kin rigada kinsha wahalar tun a baya amma baki gane bakin zaran ba, Allah umma har yanzu inna tuna S.Man shine gangster d'in abin yana daure min kai, shin daman masoyi yakan zama babban makiyi ne ko kuma dai a kaina ne hakan ya fara faruwa ko kuma nice dai mara sa'a a duniya umma, duk cikin kuka take magana

Kiyi hakuri Hiedat kibar kuka kowa da tashi kalan kaddarar ke kuma taki kaddarar kenan toh saiki godewa Allah daya baki ikon cinyewa, ki daina kukan nan kinji



Eloquence Writers Association


Karamar Su Babban Suce Ni Wato 'Yar Mutan Kd Ce

Basira Sabo Nadabo


Wattpad
@
Basira_Nadabo

BANI BACE Where stories live. Discover now