BANI BACE

219 19 0
                                    

*BANI BACE



INNOCENT MARA LAIFI



ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION




Basira Sabo Nadabo


Wattpad
@
Basira_Nadabo





Sis Shamsiyya ina tayaki murnar kammala littafinki, Allah yasa sak'on da kika isar ya riske wanda akayi don su. Amin Ya Allah, Eloquence tana tayaki murna



Sis Muhie India, Er love, Gimbiya a fadar daya dace Momcy'n 'Ya'yanta, ina sonki kullun da ko yaushe, Allahu yabar mu tare Amin, Ina jindad'in novel d'inki my pyaar😘





Dedicated to my Ramalurv



11/8/2017



SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA

Nagode Yariema, ya mai girma mai shari'a ina rokon alfarmar kotu data bani dama na karshe wanda kuma shine shaida ta karshe a wannan zaman kuma shine zai kara tabbatarwa da kotu cewa Wahiedat tana tare da MUGUN MASOYI ne domin kuwa ba son Allah da ma'aiki yake yi mata ba, ina son kotu ta bani daman kiran baba tshoho da boshe


Kotu tana son ganin ku idan kuna kusa, suka fito tare da tsayawa a gefen su S.Man

Na taka zuwa gaban su nace, baba ya sunanka

Sunana malam sani

Baba kasan wa'an nan kuwa, ko a wani guri kun tab'a haduwa

Kwarai da gaske nasan su farin sani nayi musu

Baba ko zaka fad'awa kotu alakarka dasu

Alakana dasu ba wata alaka bace face ni bara nakeyi a dai dai gurin da abin yafaru kuma akan idona akayi komai har yadda suka shirya kashe Yariema saboda sun san hanyar wucewar sa kenan, to bayan sun soka masa wukane suka nemi da nayi shuru karna fad'awa kowa, sun had'a baki da jami'an tsaro akan cewa Yariema ya mutu, bayan sun kaishi asibiti ne, har asibitin da Yariema yake naje bayan na binciko asibitin saboda naji mummunar kullun da suke son kullawa na kashe shi a can asibitin, ni da kaina tare da taimakon mahaifiyar Yariema muka sace shi daga asibitin zuwa birnin london, da yan sandan da case d'in yake hannun su, suka dawo basu ganshi ba shine suka ce ya mutu don gudun kar a kore su a bakin aikin su kuma suka d'aurawa yarinyar nan alhakin kisan, saboda lauya Sukaimanu ya cika su da kud'i harda jami'in dake lura da sashin gidan yari kuma suka tirsasata amsar laifin da bana taba iya abinda na sani kenan, toh kuma da naga innayi shuru za'a kashe wacce bata da hakki shine ranar da kika zo shagon bala naketa kallon ki har kika gama hirar ku dana gane ke wata jami'a ce shine nata binki har zuwa gidan ki domin na fad'a miki abinda yake faruwa, amma sai kika bace min a kasuwa, shine nata rokon Allah ya kara had'ani dake sai kuma muka had'u duk da barazanar kisan da bala tare Sukaimanu suke min baisa naji tsoro ba saboda nasan sai kwanana ya kare zan mutu

Toh baba mungode zaka iya komawa ka zauna

Toh nima na gode


Boshe ko zamu san menene tsakaninka da barrister Sulaiman

Tsakanina dasu dai ni abokin garus ne da naji abinda suke kullawa da kuma sanarwar da akeyi a tashar Freedom a FILIN IN DA RANKA shine banyi kasa a gwiwa ba nazo nan na nemeki na baki copy d'in kaset d'in da nayi akan duk wani plans dinsu tare da taimakon garus gaskiya iya abinda na sani kenan

Malam boshe mun gode kuma zaka iya komawa ka zauna

Ya mai shari'a wannan sune hujjojin da nake dasu kuma da wannan nake neman kotu ta wanke wacce ake zargi ta kuma durfanar da masu laifi tare da tara mai tsoka nagode, ta koma ta zauna, da ganin fuskarta kasan tana cikin farin ciki saboda yau burinta zai cika, kamar yadda ta fad'a a baya bisa yardan Allah zata fitar da Hiedat ko da karfin Addu'a ko kuma da karfin bakin ta

Toh sai muce Allah ya had'a miki duka biyun domin addu'a shine kan gaba kafin bakin, readers mu taya umman Hiedat murnar kubutar da 'yar gudaliyar yarinyar ta

Alkali yace shin ko lauyar wanda ake kara kana da magana

Bani dashi ya mai shari'a

Alkali yayi rubuce rubucen sa sannan yace bisa dogon nazari tare da tattaro duk wani hujjojin da kotu tayi ta wanke Wahiedat Abdullah daga zargin da ake mata, shi kuma barrister Sulaiman kotu ta bada damar a daure shi daurin rai da rai tare da horo mai tsanani tare da tarar naira miliyan biyu saboda yaci mutuncin kakin dake jikin shi

Shi kuma garus kotu ta bada umurnin a kashe shi ta hanyar harbi da bindiga saboda masu irin halayar sa su razana kuma su gane abinda sukeyi bashi da kyau

Bala mai shago kotu ta bada dama a daure shi har tsawon shekara ashirin tare da tarar naira dubu ďari biyar da horo mai tsanani saboda shine ya taimaka gurin kokarin kisa

Kopir dauda kotu ta bada umurnin daya shire hularsa tare da zaman gidan yari na shekara goma tare da horo mai tsanani sannan zai bada tarar naira dubu ďari uku

Mariya itama kotu tashi tarar ta naira miliyan ďaya saboda tasan Sulaiman saurayin Wahiedat ne kuma ta zaga suke soyayya inda Allah yasa anyi aure zasu iya kashe ta kenan

Alkali ya bubbuga gudumar sa kowa ya mike

Da gudu naje na rungume Ummata ina kuka itama tana kukan farin ciki yau ga 'yarta ta dawo gare ta, na sake Ummata a dai dai lokacin da za'a fitar da S.Man nace



Eloquence Writers Association

Karamar Su Babban Suce Ni Wato 'Yar Mutan Kd Ce

Basira Sabo Nadabo

Wattpad
@
Basira_Nadabo

BANI BACE Where stories live. Discover now