BANI BACE

244 20 0
                                    

*BANI BACE

      INNOCENT MARA LAIFI




*ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION




Basira Sabo Nadabo


Follow Me On Wattpad @ Basira_Nadabo





Baby Tsamiya, yar gidan Tsamiya, my Tsamiya, I love you Tsamiya lurv😘



Dedicated To My Sweetheart Ramaluv




25/07/2017




SHAFI NA TARA

Ke!! Ba wa'azi nace kimin ba dole yau saina kashe kashin dake raina, shekara da shekaru banga wanda ya isa ya hanani abinda nayi niyya ba

Abba Allah ne zai hanaka kuma bazai taba baka daman cinma burinka akaina ba, kuma zai kare ni daga dukkan sharrin ka, na kara fashewa da wani irin kuka

Ya shigaba da zuwa gurina, inaja da baya har na manne da bango

Ki gudu mana, ki tsaga bango ki shige

Toh ke kuma kina tsaye zai lalata miki rayuwa baki gudu kin fita ba ko kiyi ta ihu har mai gadi ya jiki ko kuma kije wani gurin ki buya

Hmmm hiedat kenan duk wannan tunanin basuzo kaina ba, sai guda daya, nayi tunanin na kashe kaina, saina tuna wuta ce makoma ta sannan Annabi na zayyi fushi dani, saina juya akalal kisan kan wanda yake son rayuwata ta mutu ba tare da raina ya fita ba, nayi saurin raruman lamp dake bed side na kwada mishi akai, na kara buga mishi a kirji yayi ihu, ihun yayi dai dai da dawowar ummata da gudu ta shigo dakin Abbana, tana budewa taga Abbana kwance cikin jini, ni kuma ga lamp a hannuna da gudu ta karasa gurin Abbana baya numfashi, ta saka ihu tare da kururuwan na kashe mata mishi tace

Wayyo Allah ta kashe min miji daman tsintaccen mage bata taba zama mage, kin kashe min miji saboda ba ubanki bane to wallahi sai kin biya wannan kisan, bazaki kara kwana a gidan nan ba, daman sai da nace ma Alhaji karmu dauke ki ya kafe gashi abinda kika saka masa dashi kenan kin kashe min miji, saboda kici dukiya ko? To wallahi ko taro bazaki samu ba lokacin da muka tsinto ki abola muka miki sitira muka ilmantar dake shine kika ban kade mana zani a kasuwa

Tunda ta fara magana, hankalina ya fita ajiki na daman allurar da take faďa min zata tono garmar kenan? Toh waye iyaye na daman nima ba 'ya bace kamar kowa? Na shiga ukuna iyaye na sun cuceni sun gama dani kyawuna ya tashi a banza tunda ni na 'yar sunnah bace ni, kafin na ankara yan sanda na gani cike da ďakin, muryan ummata na tsinkaya tana cewa gata nan itace ta kashe min miji, kufitar da ita bana son ganin ta, kin cuceni zeenart Allah ya isa tsakani na dake shegiya 'yar tsintuwa ki rasa abinda zaki saka mana dashi sai sharri ku fitar da ita Don Allah, wata 'yar sanda tazo gabana ta samin ankwa sai jana takeyi bani da kuzari dan ban san inda nake jefa kafata ba har zuwa dana baki labarin rayuwata, kuma bana nadamar kashe Alhaji Abba da nayi, babban bakin cikina shine ban san waye iyayena ba sannan wani irin laifi nayi musu da suka zabi yin zina har suka haifeni, ummata bataji kunyar goyon cikina ba sai rainona ne takejin kunyar yi? Wazai bani amsar nan, hiedat bazan taba yafe ma iyayena ba kuma ko a gaban Allah sai anmin shari'a tare dasu don bazan yafe musu ba, ta fashe da kuka

Ban hanata ba saboda kukan shine zai rage mata damuwar dake cikin zuciyarta, har tayi shuru dan kanta nace, kiyi hakuri Muzeenat tabbas kina cikin tsaka mai wuya amma ke naki mai sauki ne akan nawa amma kuma duk mun tafka laifi iri daya, sai dai ni zargina akeyi danni ban aikata ba wallahi zeenart Allah, bari kiji labarina zaki tabbatar da cewa BANI BACE, sannan ban aikata ba, Inna lillahi Wa Inna Ilaihir rajiun, wallahi Allah ban aikata ba zeenart amma sunce nice

Toh hiedat ki fara bani labarin kafin na yarda cewa bake bace kika aikata da har aka kawo ki gidan yarin nan, don nasan duk wanda kika gani a nan to wani babban laifi yayi amma dai ina jinki

Hmmm zeenart daga ganin halama kema kina bayan su kenan ko shikenan

A'ah ni wallahi bana goyon bayan su, nidai ki bani labari

To shikenan, bari kiji labarina


*Eloquence Writers Association


Karamar Su Babban Suce Ni Wato 'Yar Mutan Kd Ce

     Basira Sabo Nadabo



Follow Me On Watpad @ Basira_Nadabo

BANI BACE Where stories live. Discover now