BANI BACE

357 28 0
                                    

*BANI BACE

      INNOCENT MARA LAIFI




*ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION




Basira Sabo Nadabo

Follow Me On Watpad @ Basira-Nadabo.

*Dedicate to Ramaluv Ina sonki sweetat


_18/07/2017


SHAFI NA BIYU

Mallam tsaya na dauko mayafi na mu tafi tare na gaji ina son ganin 'yata, Don Allah karka ce bazani ba mallam ka tausaya min yau wata daya kenan kaki bari na muje ka tausaya wa uwar da tarasa 'yarta mana, sai ga hawaye sharrrrr

Ya isa haka kukan don naga ke bakya gajiya da zubar da hawaye, to yi maza kuma Don Allah ki wanke fuskar nan don gashi duk ya jike da hawaye amma da sharadin baza kiyi kuka ba indan munje

Ohhh jimin mallam da wani zance to muje mana tukunnah ko ka gani ko zanyi kuka, ai innayi kuka itama kukan zan sata nikam muje karsu hanamu ganin ta

Tunda muka doso gurun zuciyata take har bawa saboda ban san a wani yanayi zan tsince ta ba, ina ganin yanayin gurin naji hawaye yana saukar min

Kin fara ko Allah zaki koma a hakan ne zaki iya jure ganin ta? Eh hajiya to kiyi maza ki goge hawayen nan Don Allah

Toh mallam na share bazanyi kukan ba In Shaa Allah, ta fada cikin muryan kuka

Cen na hangota tana aikin kuka tun daga nesa ta hango iyayenta, tana son zuwa gurun su amma babu hali ta face da wani irin kuka tana buga kanta a jikin bango,

Da gudu umma ta karasa gurinta ta rike ta tace haba mana 'yar baba so kike ki kashe kanki ne akan abinda baki aikata ba

Umma wallahi BANI BACE ban aikata ba wallahi Umma banyi ba amma sunce nice, Umma mutuwa zanyi ina son na mutu Umma, Umma kice mutuwa tazo Don Allah, na kirata taki zuwa Umma

Shhhhhh yi shuru kinji akwai Allah zayyi mana maganin su, kul karki kara kiran mutuwa kinji ba yanzu zaki mutu ba sai gaskiya ta bayyana, kinji yi shuru daina kuka nima zanyi kukan, share hawayenki Wahiedat, zamu shigar da kara kotu bazan iya jure ganin ki anan ba kuma In Shaa Allah zamuyi nasara kinji

A'ah Umma kubari su kashe ni da nau'ikan azabar su, ni bana son zaman duniya, duniyar tamin kunci, bana so Umma mutuwa ta kawai nake so yanzu tazo Umma nidai mutuwa Don Allah Umma, tana kuka me cin rai,
(ni kaina Basira saida kwalla ya saukar min)

Shhhhhh kar kiyi sa'bo hiedat akwai Allah kuma shine zai bayyana mana komai yi shuru, duk cikin kuka suke magana

Ammm ďiyar baba yi shuru bar kukan ya isa haka kar kisawa kanki zazzabi, nida Ummanki zamu dage da addu'a kuma In Shaa Allah zamu shigar da kara kotu sannan Allah yana tare damu bisa yardan sa zamuyi nasara akansu, in sunce takalmar su mulki mu kuma takalmar mu Allah kuma shine a gaban mu a koda yaushe muna tare dashi, kema ki dage da addu'a don wannan kukan da kiraye kirayen mutuwa da kikeyi bashi bane zai fishshe ki, don in akace miki ga mutuwar guduwa zakiyi, ina tauhidinki yake ne, kuma ina so ki zauna kiyi nazari akan dukkan abinda yafaru a ranar Allah zai warware mana komai, amma wannan kukan bana son shi kinji ko

Baba S.man ya yarda ban aikata ba wallahi baba banyi ba, S.man ma ya san BANI BACE, baba Don Allah kace masa banyi ba Allah

Haba 'yar baba kukan ya isa haka, shima Sulaimanu yazo gidan ya kai sau biyar shine ma yace akai maganar kotu kuma shine zai tsaya miki nidai ki zauna kiyi nazari akan abunda yafaru a ranar don kece zaki fitar da kanki bani ba ba kuma Ummanki ba sannan ba Sulaimanu ba, kinga lokaci ya kusa zamu dawo ko kuma Sulaimanu duk yadda kika tuna kiyi kokari ki rike karki manta kinji ko ďiyar baba, hajiya kukan ya isa ki tashi mu tafi kafin marasa mutuncin cen su fitar damu, yi hakuri nima dauriya ce irin na maza amma kasan zuciyata kuna take min

Kai tsoho ku fita ko baku ga lokaci yayi bane? Ku fita tun kafin na fitar daku, inji ma'aikacin gidan yarin



*ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION

Karamar su Babban suce ni wato yar mutan kd ce.

     Basira Sabo Nadabo

     Follow Me On Watpad @ Basira-Nadabo.

BANI BACE Where stories live. Discover now