BANI BACE

184 12 0
                                    

*BANI BACE

      INNOCENT MARA LAIFI





*ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION





Basira Sabo Nadabo




Follow Me And Vote My Story On Watpad @ Basira_Nadabo





Haliema (Momie) ina sonki sosai a rayuwata, ALLAH ya kara hadamu don wannan memory bazai taba mantuwa a brain dina ba, Haliema mai twins din suna, 'yar fara kyakkyawa mutan jala, ALLAH ya raya mana ke musha biki, amma lokacin Aunty Sister tana gidan Uncle Mujitaba In Shaa Allah, Muahhh 😘😘





*Dedicated To My Ramaluv durlin*



27/07/2017



SHAFI NA GOMA SHA DAYA



Wahiedat ki fada min gaskiya me kikayi aka kore ki a makaranta?


ALLAH Baba, banyi komai ba nima ina aji shugabar makarantar mu ta kirani office din ta shine ta bani wannan letter din amma wallahi banyi komai ba


Mallam kenan kamar baka san halin shuwagabannin nan bane, inhar suka kille ido suka hango yarinyar da bata da karfi a makaranta to fa nata ya kare, sai dai kawai ilimin ta ya fidda ta don ko irin taimakon dalibai da akeyi tofa ita baza'a bata ba, kuma karatun yanzu ai duk boge ne, kana ina ďan me kudi yana zaune baiyi karatun komai ba amma da anje jarabawa suka ga sunan uban yaron wani kusa ne a gwamnati sai a dauki makin yaranmu talakawa a bawa 'ya'yan masu kudi, kai dai mallam abin kawai sai addu'a amma ilimi ya tabarbare a kasan nan


Toh ALLAH ya Kyauta amma kam akwai gyara, toke kinji saiki dage da addu'a kuma ki kara kaimi a kan karatun ki, muma zamu cigaba da addu'a In Shaa Allah, ilimin ki shine zai fiddaki a wannan makarantar ko ďiyar Baba

In Shaa Allahu, Baba zan dage, muna zaune muna hira sai ga wayar shugabar makarantar mu, suna bukatar na dawo makaranta yau ba sai gobe ba, haka na shirya na tafi ina zuwa naga yariema a kofar makaranta, yana ganina ya washe baki sai wani farin ciki yakeyi na rasa na menene, tare muka shiga cikin makaranta, Gimbiya Mariya tana zaune da kawayen ta taga mun shigo tare da yariema kuma har gurin zama na tare muka zauna, muka cigaba da hira, ban tambaye shi ya akayi yasan bana school ba saboda nasan dole ya sani, zeenart abubuwa sunta faruwa a ciki harda kammalawar makarantar yariema, saida yajawa shugabar makarantar mu kunne akan karta yarda a cuceni ko kuma a taka daraja ta wannan abun shine ya kara tinzura Gimbiya Mariya ta sani a gaba har nima na samu na kammala karatuna, itah a tunanin ta muna soyayya da yariema ne wanda ni kuma ba hakan abin yake ba, ni maima zai kaini soyayya da abinda yafi karfi na, haba ai ba hadi ma domin duk wani dan sarauta yana kyamar dan talaka

_(Ni Basira Sabo Nadabo nace hiedat ba duk ba saboda ba duka aka taru aka zama daya ba kuma ya faru akaina na kara tabbatar da hakan, kawai kowa dai da halinsa shine magana)_

Toh wai hiedat wacece Mariyar nan ne data ke takura miki a school?

Yarinyar wazirin sarki ne

Au daman 'yar karere ce take miki haka shine bakici ubanta wazirin ba

Ke rufa min asiri, don Allah ki barni na mutu maza su kaini Don Allah

Toh, ina jinki cigaba

Tunda yariema yabar makarantar ban kara haduwa dashi ba ke har a TV bana ganin sa, nima har nayi graduation dina ban samu na cigaba da karatuna bay, da kyar na samu koyarwa a makarantar unguwar mu kuma suna biya na da tsoka, ranar laraba a hanyata ta dawowa daga makarantar da nake koyarwa na hadu da SULAIMAN, tun bana kula shi saboda tsabar nacin sa saida na kulashi, soyayya mu tayi karfi har iyaye suka shiga ciki, ana jiran ya karasa karatun sa na law a ABU yana shekararsa ta karshe kenan kullun soyayyar mu karfi yakeyi, sannan baki san wani abuba zeenart da Umman sa da Ummata sunyi karatu a ABU tare a fannin shari'a kuma kawaye ne sosai a wancen lokacin, bayan sun gama karatu ne basu kara haduwa ba sai a sanadiyyar mu ni da S.man sunji dadin sake haduwa a rayuwar su






*Eloquence Writers Association*



Karamar Su Babban Suce Ni Wato 'Yar Mutan Kd Ce

        Basira Sabo Nadabo


Follow Me And Vote My Story On Watpad @ Basira_Nadabo

BANI BACE Where stories live. Discover now