BANI BACE

231 21 2
                                    

*BANI BACE

      INNOCENT MARA LAIFI




*ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION




Basira Sabo Nadabo


Follow Me On Watpad @ Basira-Nadabo




Dedicate to Ramaluv



22/07/2017


SHAFI NA SHIDA


Toh Allahu ya shaa,

Baba ni zan koma gida in cigaba da bin cikin lamarin don bazai yuwu mu shiga court bamu da evidence a hannun mu ba saboda mune da kara

Sulaimanu zan bin cika mana amma dai yanzu kam bamu da komai a hannun mu, hmm ni har fargaba nakeyi wallahi, ALLAH ya taimakemu

Amin Ya Allah, amma kam mallam ni kaina a tsorace nake, yanzu shikenan in sunyi winning a kanmu kashe mana ita zasuyi, sai ta fashe da kuka

Haba hajiya, ya kike saurin karaya ne? Waye yace miki za'a kashe ta ko kuma zasuyi nasara a kanmu, haba mana ki dinga kyautata zatonki mana, tunani mai kyau ma lada ne fa haba Don Allah kullun ace mutun yana kan abu daya

Nayi shuru toh, ta tashi ta shige daki don ta samu tayi kukan ta yadda ranta yake so, ko ta samu damuwar daya cun kushe a zuciyarta ya ragu har barci ya dauke ta

GIDAN YARI

Don Allah ka taimaka min da ruwan sha k'ishi nakeji, tun safe banci komai ba

Ke! Ya daka mata tsawa, ance miki nan gidan ubanki da uwarki ne? toh bamu da ruwan da zaki sha ki gama gugar nan ga wanke wanke cen yana jiranki don ubanki, wacce bata da imani don mutun yace baya sonki saiki masa da tsiya matsiyaciya yar matsiyata

Karka kara saka iyayena a cikin al'amari na saboda nice mai laifi ba suba kuma ni na matsiyaciya bace daga taimako sai ya zame min shae

Ke to waye matsiyacin? Eh nace waye matsiyacin

Sun san kansu amma dai nikam ba matsiyata bane

Tun kafin ta karasa rufe baki ya hada mata mari ya zare belt ya dinga zuba mata har saida ta zube a kasa, yau zan nuna miki aikin matsiyaci, yar iska, yau zaki san kinzo gidan yari, mara imani, duk rashin imani na bazan aikata abinda kika aikata ba

Cikin sheshshekar kuka take magana tace ai rashin imani yana gurinka don na tabbata kasan akan gaskiyata kake azabar dani kasan cewa ban kashe yariema ba amma da yake duniyar cike take da azzalumai, dadin abin Allah baya goyon bayan azzalumai da zaluncin su, akwai ranar da zai wanke ni daga mugun kullun ku azzalumai kawai, In Shaa Allahu asirin ku ya kusan tonuwa ranar da nadamar ku bazai amfane ku da komai ba, azabar ku tafe take da nadamar ku azzalumai

Ke ni kike gayawa wannan maganar lallai yau zan gana miki ukubar da iyayenki ma zasu kasa ganeki don jarkan ubanki

In banda kuka babu abinda nakeyi, wai sai yaushe ne zan wanke daga mummunar kullin da mutanen nan ne? Oh kasani BANI BACE wallahi ban aikata ba wallahi BANI BACE

Ke ba bayaninki nake nema ba nidai kawai ki amsa cewa kin aikata kawai shikenan kinga tunda mutuwa kike so sai na kasheki ki huta batare da kowa ya sani ba, sai nace mutuwa kikayi amma in kinki amsawa azaba da gwale gwalen da zan baki Allah ne kadai zai ceceki, wahala kullun kina cikin sa a gidan nan

Bazan taba amsa abinda kake bukata ba, ni ba mai kisan mutane bane kuma bazan taba zama mai kisan mutane ba kagane mugu kawai

Ya kai mata mari a baki har saida bakin ya fashe, cikin kunan rai yace toh wallahi na dinga gana miki azaba kenan a gidan yarin nan har sai kin amsa cewa kece kika aikata abinda ake zarginki dashi b'ace min a gaba kafin na ballaki tara shegiya 'yar matsiyata, ina ganin arziki kina koransa a gare ni to baki isaba dole ki amsa, ko kinki ko kina so dole ma ki amsa



*Eloquence Writers Association

Karamar Su Babban Suce Ni Wato 'Yar Mutan Kd Ce

      Basira Sabo Nadabo

Follow Me On Watpad @ Basira-Nadabo

BANI BACE Where stories live. Discover now