BANI BACE

194 22 0
                                    

*BANI BACE

     INNOCENT MARA LAIFI





*ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION





Basira Sabo Nadabo







Follow Me And Vote My Story On Watpad @ Basira_Nadabo







Muzeenat (zeenart), Bilkisu (Hajia), Ummu-Khairi (Baby), Halimat Sa'adiyya (Ni'iema), Moh.d Sani (Marwan), da sauran members Family ďin Hajia Sa'adiyya (Aunty Kaka) ALLAH Ya Kara Miki Tsawon Rai Tare da Kwanciyar hankali, Amin Ya Allah Grandma 👳🏾‍♀👳🏾‍♀



_Labiba Baba Ahmad my childhood friend ina sonki sosai bebe

*Dedicated To My Center Fresh Ramaluv Dear






30/07/2017






SHAFI NA GOMA SHA HUDU



Kee Muzeenat rabani Don Allah, nikam bana zargin kowa saboda nasan bazata taba aikatawa ba kawai baki ne tare da barazana take min, kema kibar zargin ta

Ke kin san Allah itace, ai tace zakuyi biyu babu to me take nufi da hakan da zakice nabar zargin ta, ke da za'a bani izini a kotu ko da nace itace

Hmm zeenart kenan toh ai kotu basa amsar zargi babu shaida, ke kuma zargin ta kikeyi tunda baki da shaida, kawai wannan lamarin Allah ne kawai zai fitar damu amma ba karfin mu ba


Ke, kinji dadi ma S.Man zai tsaya miki, gaskiya S.Man ya cika babban masoyi ni sai naga ma kunfi dacewa dashi, don mutumin da zaka shiga matsala ya zauna tare da kai ai shine masoyi sannan shine zai kareki a gaban alkali, ya kareki ya kare darajarki da mutuncinki, gaskiya hiedat kinyi dacen masoyi wanda burin ko wata 'ya mace kenan

Zeenart S.Man yafi gaban yadda kike tunani, ni kaina na tabbatar da kalan soyayyar da S.Man yake min, zeenart S.Man mutum ne mai tunani mai kyau, ga gaskiya da rikon amana amma bu daya yayi masa karanci, wanda duk tun kahon ka inhar karasa wannan abin da kai da dabba marabar kadan ne


Me kenan hiedat


Uhmmm zeenart S.Man yana da karancin ilimin addini, bai san komai daya shafi addini ba, wani abinfa nice nake tunatar dashi, abinda nake gujewa S.Man nan gaba shine 'ya'yan da zamu haifa a basu assignment a islamiyya su kawo masa yace a bani, kullun in suka lura da haka zasu san cewa mahaifinsu jahili ne bai san komai ba, nayi nayi dashi ya shiga makarantar da akeyi tsakanin sallar magriba da isha'i saboda shima yana jawo mazaje daga afkawa babban halaka, domin jahilci babban halaka ne wanda mutun yana rayuwa ne tamkar matacce saboda baima san abinda ya kawo shi duniyar ba sannan ko sallah zakayi sai kasan yadda zakayi kafin kayi, toh zeenart ya mutun zai tsallake azabar Allah ranar al'kiyama

Gaskiya babu, babu yadda zaka tsallake azabar Allah saboda ya baka lafiya, tare da rai da kwanciyar hankali kawai tashi zakayi ka nemi ilimin nan, don in kana takama da ilimin nasara, su kansu nasarar kansu ya waye sai sun bincika abinda Al'kur'ani yace sannan suke samun cigaba, abinda mu kuma muka kasa ganewa kenan hiedat

Bama wannan ba zeenart, sai kiga wani zai dauki dubu hamsin ya biya kudin makaranta duk bayan wata uku ko hudu amma naira ďari biyar dinda zai bayar duk wata shine yake gagarar mu, wallahi zeenart abin nan yana cimin tuwo a kwarya sai dai muyi fatan Allah ya gyara mana


Ke fito lokacin aikinki yayi, shegiya sai wahalar dani kikeyi ki amsa kawai daga ni harke mu huta mu daina ba mawa kanmu wahala amma da yake ke baki gaje arziki ba kinki bani hadin kai, fito wahala bakiga komai ba tukunna


Haka suka cigaba da bani gwale gwale da nau'ikan azaba har ranar ziyarar mu ta zagayo, kamar yadda Baba yace ile kuwa S.Man ne yazo min ziyara naji dadin ganin sa, bayan mun gaisa ya fara min tambayoyin su na lauyoyi, duk abinda na sani game da kisan Yariema Abbas Musa Sarki, yace


Wahiedat abinda nake so dake, shine ki kara hakuri In Shaa Allahu komai yazo karshe, ba'a son raina kike nan gurin a zaune ba baby, ki kara hakuri Wahiedat ranar litinin zamu fara zama a kotu kuma In Shaa Allah mune da nasara

Amma kaima ka yarda nice na kashe Yariema?

Ai Wahiedat wanda bai sanki bane zai yarda da abinda bake kika aikata ba, Wahiedat ban yarda ba kuma bazan taba yarda ba, ina tare dake hiedat babu mai cutar dake kinji matata kuma a koda yaushe ki dinga tunawa cewa Ni SULAIMAN masoyinki ne na gaskiya, ni zan koma saboda ina son komawa wannan gurin da abin yafaru domin in samo evidence, saboda in bamu da shaida tsab za'a iya kada mu a wannan shari'ar

Toh shikenan sai mun hadu a kotun amma akwai wani wanda ya takurawa rayuwata da lokacin aiki da lokacin hutu, ni duk lokacin azabana ne, nice wankin uniform, share field, wanke wanke, goge masa kaya yawancin aikin gidan yarin nan nice nakeyi bayan wanda ake bamu

Wahiedat komai yazo karshe ki kara hakuri, In Shaa Allah mune da nasara ko, sai mun hadu a kotu ranar litinin kenan, ya fada tare da mikewa

S.Man duk rintsi karka rabu dani, ina sonka kagane ban aikata laifin da ake zargina dashi ba, ALLAH ban aikata ba







*Eloquence Writers Association


Karamar Su Babban Suce Ni Wato -Yar Mutan Kd Ce

     
Basira Sabo Nadabo



Follow Me And Vote My Story On Watpad @ Basira_Nadabo

BANI BACE Where stories live. Discover now