BANI BACE

178 16 0
                                    

*BANI BACE

      INNOCENT MARA LAIFI





*ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION





Basira Sabo Nadabo





Wattpad @ Basira_Nadabo







Sis Sarah durlin my love for yhu is unlimited, i don't even know how to start telling yhu how much i love and care for yhu dear. Sha i love yhu wujiga wujiga ❤



Baban Hajia durlin (uncle Musa) Allahu ya kaiku lafiya ku dawo lafiya, muma muna nan zuwa watarana, kasa mai tsarki akwai daɗi, Allah kasa inna tafi ka ɗauki rayuwa ta a kasar da Manzo (SAW) yake kwance. Amin Ya Allah



Dedicated to my center fresh Ramalurv






4/08/2017



SHAFI NA SHA TARA




Yayi murmushi yana ganin ya hango nasara ɓaro ɓaro ya tattaka zuwa gaban tebirun su, yace ya mai girma mai shari'a Wahiedat Abdullah ta rigada ta amsa laifin ta saboda kowa ya gani ta kasa amsa cewa ba ita bace kuma daga ganin halama tayi saranda ta yarda ta amince ita ɗince ta aikata wannan babban laifi, amma zanso kotu ta bani dama na kirawo Mariya Waziri in tana kusa

Alkali yace kotu tana son ganin Mariya Waziri in tana kusa


Mariya ta fito cikin shiga ta alfarma tana tafiya cikin isa da gadara ta tsaya a gurin da masu laifi da bada shaida suke tsayawa

Barrister Abubakar yace malama Mariya ki ɗaga hannunki na dama ki maimaita abinda zan faɗa, kice ni Mariya Waziri

Ni Mariya Waziri

Na rantse da alkur'ani duk abinda zai fito a bakina gaskiya ce zan faɗa

Na rantse da alkur'ani duk abinda zai fito a bakina gaskiya ce zan faɗa

Sannan yace malama kotu zataso jin sunanki

Sunana Mariya Ahmad Waziri

Wani Wazirin?

Wazirin Sarkin garin nan maici yanzu

Malama Mariya menene alakarki da margayi Yariema

Alakata da Yariema, alaka ce mai karfi domin mahaifina shine babban aminin Sarki kuma har da batun aure a tsakanin mu

Madallah, shin ko zaki gane waccen baiwar Allah ɗin? Ya faɗa tare da nuna ni

Eh nagane ta Wahiedat Abdullah ce wacce aka bawa scholarship a makarantar mu

Toh menene tsakanin ki da ita don in kin tuna kalamanta na baya tace kun tabayin takun saka da ita

Ni kuma a'ah ni babu komai a tsakanin.mu da ita saboda ko.matsayin mai gyara min takalmi bata kai ba, kaga ko menene zaisa na tsaya kula 'yar talakawa irinta, inma zan kula talaka toh ba irin waccen abin ba


Toh tsakanin ki da Yariema Abbad fa

Yariema mijin da zan aura ne amma waccen 'yar natsiyatan talakawan ta kashe min shi, saita fashe da kukan k'arya

Yi hakuri Gimbiya Mariya Allah ya jikan shi yasa ya huta Amin, zaki iya komawa ki zauna mun gode hajia

Ya juya ya kalli mai shari'a yace da wannan nake so kotu ta yanke wa Wahiedat Abdullah wacce ta kashe ma Gimbiya Mariya mijin da zata aura wanda badan Wahiedat ta shiga tsakanin suba da yanzu suna zauna lafiya k'alau tare da mijinta amma saboda son rai da bakin cikin Yariema yace baya sonta Gimbiya yake so shine Wahiedat ta kashe shi, saboda haka ta wannan ne kawai za'ayi abi musu hakkinsu, ya mai girma mai shari'a da haka nake rokon kotu data yai gaggawan yanke wa Wahiedat Abdullah hukunci dai dai da laifinta, nagode ya koma ya zauna tare da murmushi a fuskar shi kila ya gama nasara kenan, ni kaina Basira da nake makale da 'yar wayata kirar baby nokia nake ɗauko muku rahoto dana kalla Wahiedat sai da naji danshi a fuskata dana shafa naji ashe hawaye ne ya saukar min saboda tausayin za'a kashe baiwar Allah da bata jiba bata gani ba koda a gaban ta aka kashe shi bai kamata ashe itace ta kashe shiba Allah Sarki amma ai gida biyu ne, kowa dai da abinda yake faɗa

Alkali ya bubbuga gumar sa kowa ya nutsu yace bayan dogon nazari da kotu tayi akan duba da shaidun da aka kawo gaban ta kotu ta yankewa Wahiedat Abdullah hukuncin.......

A dakata aka faɗa daga bakin kofa duk zuka juya zuka zubawa wacce tace a daka ido, tana takowa a hankali harta karaso gaban alkali tayi gaisuwa

Sai naji wani sanyi daɗi ya ziyarce ni ALHAMDULILLAHI nake ta nanatawa saboda nasan Allah ne ya kawo min wannan baiwar Allah ɗin domin ta kuɓutar dani akan laifin da ake shirin kashe ni kuma sun san BANI BACE




Kudai cigaba da hakuri na kusan kammalawa sauran kiris In Shaa Allahu. Basira tana kara godi




*Eloquence Writers Association



Karamar Su Babban Suce Ni Wato 'Yar Mutan Kd Ce


        Basira Sabo Nadabo



Follow Me And Vote My Story On Wattpad @ Basira_Nadabo

BANI BACE Where stories live. Discover now