BANI BACE

266 16 0
                                    

*BANI BACE

     INNOCENT MARA LAIFI





*ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION






Basira Sabo Nadabo




Wattpad @ Basira_Nadabo








Uwayen ɗakina kuna raina kuma ina godiya da kulawarku gare ni. Basira Sabo Nadabo tana godiya bisa kaunar ku a gare ni.

Uwar ɗaki na Aysha Sada Machika (MYSHA)

Uwar ɗaki na Mrs Hamisu (GOYON KAKA)





Dedicated To My Sweetat Ramalurv




6/08/2017




SHAFI NA ASHIRIN DA ĎAYA


Nagode ya mai shari'a ta cigaba da cewa malama Mariya zaki iya komawa ki zauna, zan nemeki wani lokacin in hakan ya taso, ya mai girma mai shari'a da haka nake neman alfarmar kotu data bani belin Wahiedat tunda har yanzu zarginta akeyi ba'a tabbatar da hakan ba kuma ina rokon wannan kotun mai adalci data kara bani lokaci akan kawo mata duk kanin hujjoji gamsashshu, nagode ta koma ta zauna barrister Abubakar sai harara na yakeyi ko kallo bai isheni ba muma mata muna da rawar takawa a kowani mukami aka ajiye mu ba komai bane bazamu iyaba ko wacce mace da irin baiwar da Allah ya bata, wata gurin iya magana wata kuma gurin iya kwalliya wata kuma gurin iya girki gadai sunan kowa da irin baiwar halittar da Allah yayi masa

Alkali yayi nazari mai zurfi yace kotu ta ɗaga wannan shari'ar zuwa goma ga watan da muke ciki sannan kuma wannan zama shine zama na karshe da kotun zata saurara, ya kara da cewa kotu ba zata baki belin wacce zargi ba za'a cigaba da rike ta har sai gaskiya tayi halinsa ya buga gudumarsa kowa ya mike alkali ya fita nima aka tisa keyata ziwa gidan jaru




JALINGO

Hajiya gaskiya da sake wallahi bazai yuwu ba ya za'ayi abar 'yar mutane a gidan yari kodan ke baki taɓa haihuwa ba shine yasa haka haba mana ina iliminki yaje ne kuma shi wannan abinda ake zarginta dashi ke kinsan abinda yasa tayi hakan ko kin nemi jin na bakin ta kafin ki yanke hukunci, ke kanki shaida ce yadda Zeenert take son Abban ta amma ace an wayi gari ta aikata abinda ke kike zarginta dashi donni har yanzu bana zargin 'yar talikar nan Allah

Haba yaya Aina'u ki saurare ni mana nice fa taki nice ya kamata ki saurare ni

Na saurare ki kice min me kice min kin kai 'yar da kika raina tun tana tsummar goyo sannan kice min bakisan abinda zata aika da wanda bazata aikata ba, ni kinga tafiyata kuma wallahi bazamu taɓa shiryawa dake ba idan dai zeenert bata dawo gidan nan ba

Haba yaya Aina'u don Allah karki tafi ki barni

Ah toh kidawo da Muzeenat gidan nan, na dai faɗa miki kenan, abinda wanda kikeyi don shi ɗinma bai barki ba nafasan komai duk wani kulle kullenku nasani kuma wallahi in bakiyi wasa ba saina kaiku kotu da gidajen radiyo tare da talebijin don bazan taɓa yarda da wannan cin kashin ba ehe

Don Allah ki tsaya kiji wallahi akwai abinda nake so mu tattauna dake yaya Aina'u, wallahi maganar tana da mahimmanci kila inna faɗa miki na samu saukin sa a cikin raina

Toh ina jinki, amma kisani bazan taɓa canjawa ba dole a cikin biyu kiyi ɗaya

Yaya Aina'u shekaran jiya ne wata mata tazo gidan nan wai tazo amsar 'yarta, ni ta kulle min kai saboda nasan bamu da wata 'ya a gidan nan sai zeenert kuma tazo harda min gargaɗin cewa inhar ban fito mata da yarinya ba kotu ce zata raba mu, toh kinji abinda yake damuna

Hmmm babban magana to ke baki tambaye ta wata 'yar ba ko kuma ta kawo miki wata 'yar ne bamu sani ba

Toh shine nima na kasa ganewa wallahi tun ranar kaina a kulle take na rasa yadda zanyi yaya Aina'u

Yanzu yaushe tace miki zata dawo?


Bata faɗamin ba, tadai ce inhar ban fito mata da 'yarta ba kotu ne zai rabamu

Toh shikenan ki bari tazo ɗin sai muji wayata 'yarta ne zamu bata ko


Hmmmm toh shikenan Allah ya kawo ta

Amin, ni zan koma saina sake dawowa ko, inhar tazo kiyi maza ki kirani

Uhmmm, sai anjima toh

GIDAN SU HIEDAT

Malam In Shaa Allahu mune da nasara gashi nan gaskiya ta fara futowa nifa ban yarda da wannan Mariyar ba, saboda ji daga barrister tayi bata tambayoyi harta wani rikice anya kuwa Alhaji


Ai In Shaa Allahu hajiya mune da nasara bakiga idon yarinyar nan ba harbwani zufa take gogewa na rashin gaskiya kai mutane basu da imani haba mana mutun ya kashe ɗan mutun kamar ya kashe kiyashi kai duniya ina zaki damu ne

Hmm badai gobe bane zaman mu na karshe zamuyi kallo ai, In Shaa Allahu, barin ɗan kwanta na huta malam

Toh hajiya ni inada aikin da zanyi ki tashi lafiya ko





*Eloquence Writer's Association


Karamar Su Babban Suce Ni Wato 'Yar Mutan Kd Ce

       Basira Sabo Nadabo



Follow Me And Vote My Story On Wattpad @ Basira_Nadabo

BANI BACE Where stories live. Discover now