BANI BACE

213 19 0
                                    

*BANI BACE

INNOCENT MARA LAIFI




ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION





Basira Sabo Nadabo




Wattpad
@
Basira_Nadabo






Sis Abeedah durlin u're more than a friend to me, u're ma blood, Allahu ya duba lamuran ki Allahu ya dad'a kare ki Amin Ya Allah




Aunty Cute sweetheart, Allahu yasa albarka a rayuwar ki, yasa ki gama da iyaye tare da dunyar lafiya Amin Ya Allah, ina jin dad'in novel d'inki _Zuma Sai Da Wuta_, Allahu ya baki ikon saukewa lafiya Amin Ya Allah




Ya Aina AKA Dimples, Ina tayaki murnar kammala littafin ki *'Yan Gidan Gwaiba*, Allah yasa kankare miki zunuban dake ciki alkhairan dake cikin sa Ubangiji yasa miki a ma'ajin aiyukan alkhairan ki, Amin Ya Allah


Sis Ayusha Iliasu Musa honey, ina sonki sosai bazan iya fayyace kaunata a gareki ba Allahu yabar mu tare Amin, Allah yasa albarka a jarabawarki Amin Ya Allah






Dedicated To Ramalurv





8/08/2017



SHAFI NA ASHIRIN DA UKU


A'ah nice Mariya Waziri kuma ni kaɗai ce babu wata bayana ko a gabana

Owk to sannu Mariya kinji tambayar da nayi miki ko na sake maimaitawa ne


Eh naji, wallahi babu hannuna a kisan Yariema nidai abinda na sani shine nasa bala yana lura da duk movement ɗinta saboda nan ne hanyar wucewar ta kuma nasan Yariema yana yawan bin hanyar amma wallahi ban kashe Yariema ba


Malama Mariya karki manta kinyi rantsuwa da Alkur'ani akan zaki faɗa gaskiya amma a farkon baki faɗi gaskiya ba to ya za'ayi na yarda cewa gaskiya kike faɗa mana? Mariya kinko san masifar dake cikin rantsuwa da mafificin littafi? Shin kinko san bala'in da zai afka miki sanadiyar rashin faɗan gaskiya? Mariya kinko san cewa rayuwarki zata wulakanta akan rashin faɗan gaskiya? Ina baki shawara da ni kaina da duk wanda yake nan ko yake saurare na aduk inda yake da muguji rantsuwa da Alkur'ani koda kuwa akan gaskiyar mu muke, Mariya a baya kincewa Wahiedat zakuyi biyu babu to me hakan yake nufi, ki tuna duk abinda zaki faɗa ki faɗi gaskiya ko dan tsira daga babban rantsuwar da kikayi, ke nake saurare

Wallahi ban faɗa mata wannan kalmar na zamuyi biyu babu da wani manufa ba ko kuma dan na kashe Yariema bane, abinda nake nufi anan shine zansa a ɗaura mata da masoyinta a wannan satin da abin yafaru don inhar na bari zuwa wani sati Yariema zai iya auren ta tunda nima auren zanyi bayan Yariema ya haɗu da Wahiedat ya fasa aure na shine na bawa ɗaya daga cikin mane mana daman fitowa muyi aure, wallahi abinda nake nufi kenan


Amma kin san da haka kike bawa shari'a wahala ko da yake kanki kika ba wahala tare da ayarinki, a dalilinki zakisa a kashe 'yar mutane wacce bataji ba kuma bata gani ba ki tuna kema fa watan watarana uwa ce, zaki iya ganin 'yarki ko 'ya'yanki a cikin wannan halin, kin bani mamaki hausawa sunce ciwon 'ya mace na 'ya maca ce amma ke kin nuna cewa wani ciwon ba naki bane, ki daina alfahari da arzikin mahaifinki domin gidan wani zaki, zaki iya komawa ki zauna


Ta fito da sanyin jiki halamun maganganun barrister Basira sun shigeta saboda yanayinta ya nuna hakan


Mai girma mai shari'a da wannan nake neman alfarmar kotu data wanke wacce bata jiba bata gani ba daga mugun kullun da magauta suka mata nagode, ta koma ta zauna


Shin ko lauyar mai kare wanda ake k'ara yana da magana


Eh ina dashi my lord, zan so ganin malam bala a gaban kotu



Malam bala kotu nason ganinka a gabanta



Malam bala yana jin an kirashi gaban shi yake faɗi domin yau kam yasan ya kaɗe har ganyen sa, saida alkali ya sake kiransa kafin ya fita


Barrister Abubakar yace malam bala kaji tsoron Allah da gaske ne Gimbiya Mariya tace ka kashe Yariema


Eh a'ah wallahi a'a babu ruwanta a maganar nan kuma amma ai har da ru.....


A'ah malam bala kar firgici yasa ka kasa faɗan gaskiya muna gaban alkali mai adalci ne


Wallahi Alhaji lauya nima ban sani ba


Amma dai babu Gimbiya Mariya a ciki koh


Objection my lord bai kamata barrister Abubakar yayi kokarin kuɓutar da mai laifi ba kuma yana kara ruɗa min evidence ɗina


Barrister ka kiyaye don karka maida mana da shari'a baya


Nagode ya mai shari'a, malam bala zaka iya komawa ka zauna


Alkali yayi rubuce rubucen sa na wani lokaci sannan yace barrister Basira ko kina da wani shaida ko wani abunda zaki gabatar kafin mu k'ark'are wannan zama?


Eh ina dashi my lord, ta taso cikin tafiyar isa da kasaita zuwa gaban alkali tace ya mai shari'a ina son kotu ta bani izini na kira barrister Sulaiman Shu'aib


Gabana yayi mummunar faɗuwa me Ummata take nufi da kiran S.Man? ina S.Man da karar nan Ya Ilahi Ya Allah karkasa zargina ya zama gaskiya, na share hawayen daya gangaro min domin ina cikin tsaka mai wuya




*Eloquence Writer's Association

Karamar Su Babban Suce Ni Wato 'Yar Mutan Kd Ce


Basira Sabo Nadabo



Wattpad
@
Basira_Nadabo

BANI BACE Where stories live. Discover now