BANI BACE

818 53 3
                                    

BANI BACE
         (INNOCENT MARA LAIFI)

NA

Basira Sabo Nadabo

Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim

SHEKARAR RUBUTU

2017

Tsara Rubutu
Na  Adamu Yusuf Indabo, ALLAH yabar zumuncin mu Amin.

GODIYA

Ga ALLAH madaukakin Sarki, wanda raina da rayuwa ta suke hannunsa. Ina gode maka, ina neman taimakon ka. Ya Allah ina rokonka, ka kare ni da dukkan abin ki. Ya Allah ka tsare ni ga magauta, Allah kada kabar makiya suyi nasara a kaina da kungiya ta, ALLAH bani da niyyar cutar kowa, ALLAH kada kabar makiyi yayi nasara a kaina da kungiya ta domin abarkar Annabi Muhammad (S.A.W).

DOMIN KU

Iyaye na abin alfaharina, wanda na dauki so da kauna na dora muku. Margayi Alhaji Sabo Nadabo da Alhaji Nuhu Abdullahi, tare da Hajiya Fatima Sabo Nadabo da Zulaihat Sabo Nadabo, tare da Zainab Nuhu Abdullahi da Aisha Nuhu Abdullahi da sauran al'umman Annabi Muhammad (S.A.W), ina rokon Allah da ya yalwata haske tare da rahamarsa a kabarbarunku, Ya Allah ka kara gafara a gare su damu baki daya Amin. Mahaifiyata farin cikin rayuwata nagode da kulawarki a gare ni nagode da shawarwarinki akan wannan labarin nawa Allah Ya kara tsare min ke Ubangiji yaja kwana. Amin Ya Allah.


JINJINA GARE KU

Yayye na muradina nagode da kulawarku a kaina ALLAH ya kara hada kanmu ya kauda shaidan a tsakanin mu. Amin Ya Allah

AUTA SHALELE

Fa'ieza Sabo Nadabo, ina sonki sosai a raina dake da takwara na Bashier Sabo Nadabo, tare da Muzeenat Rajeev kune ni, idan nace ni ina nufin ku, idan nace ku ina nufin ni, Allahu ya raya mana ku musha biki. Amin Ya Allah

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan littafin ga Family na gaba daya.


KAWAYE NA

Ramaluv yar kasar Niger republic ina sonki a cikin raina.

Aisha Habeeb Tall Gaskiya keta daban ce domin kalmar ana tare yana aiki a tsakanin mu kano zuwa kd ba abu bane mai sauki amma nagode da kauna sweetat.

Baby Nurse Mom Anielurv, ina sonki dake da yarinya ta ALLAH ya kauda fituna a cikin gidanki. Amin Ya Allah

JINIE NAH

Hajiya Abeedah Tautah wallahi ke daban ce duniya ma sun shaida hakan. Allahu ya jibanci lamuranki duniya da kiyama ina sonki sosai.

Rukaiya Nuhu Abdullahi, Rukiee baby mai dadin murya in tana magana kamar ana busa algaita, Ina sonki sosai tun daga qalbie zuwa baki na. Lallai Ana Mugun Taren Tare.


'''Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim'''

Ya Allah. Ina farawa da sunan ka kuma In Shaa Allah zan gama da Hamdan, wannan labarin *BANI BACE* labari ne da rabin shi da gaske ne amma sauran duk labarin ya tafi yadda kuke so ne, Allahu kasa na gama lafiya alfarmar Manzo, Habibullah, Shafi'ullah, Ya Mahabubullah Ya Sayyadi Ya Muhammadur-Rasulullahi Sallahu Aalihi Wa Sallam.

17/07/2017

Shafi Na Daya

Tafe take cikin gidan yarin ga kaca hannu da kafa in ta daga kafa da kyar take sake daga dayan, abin duniya duk ya dameta ta rasa inda za ta saka rai ta ji dadin duniyar nan kamar kowa, da galabataccen murya ta ce.

"Ya Allah ka taimake ni ka bayyana wannan murdedden al'amarin nan ya Allah!"

Karasa maganar ta yi cikin sheshshekar kuka ta daura da cewa.

"To ni da nake nan bani da gata waye zai fidda ni a cikin rikitattacen aal'amarin nan? Nasan ida Allah wuya babu, na dogara ga Allah shine zai bayyana komai!"
Kuka ne yazo mata mai karfi zuciyarta ta cigaba da ce mata.

'Yaushe kuma wani lokaci ne hakan zai faru? Ke da kullum kina cikin wannan daurin waye zai fuskance ki? Waye zai yarda da cewa bake ba ce? Waye zai aminta da kalaman bakinki har ya ji a ransa bake din ba ce? Yanzu da wani ido zaki kalli mahaifinki? Da wani idanun zaki kalli mahaifiyarki da ta yarda kuma ta dauki amanar kanki ta damkashi a hannunki? Me za ki cewa S.man mutumin da ya yarda dake kuma ya amince da aurenki?'
Hawaye na zuba daga idanunta masu zafi cikin daga muryar da ta disashe da kuka ta ce.

"Wa zai ceceni? Waye zai yarda da ban yi abinda suke zargina ba? Ya Allah kasan BANI BACE ban aikata ba wallahi ni ba mai laifi bace, Ya Allah ka wanke ni a idon duniya wallahi ban aikata abinda ake zagina ba. Wallahi ban yi ba suma sun san BANI BACE amma suka rintse ido suka ce ni ce! Ya Allah yaushe zaka wanke ni ne? Yaushe gaskiyar al'amarin zai bayyana kansa? Yaushe? Yaushe ne Ya Allah!?
Duk cikin kuka take magana. Daya daga cikin masu aikin gidan yari ne ya daka mata tsawa hade da cewa.

"Ke ki yi mana shuru tun kafin na ballaki takwas, wani ya ce ki aikata ko wani ne ya tura ki? Kin yi abu dan kudi yanzu kuma kina cika mana kunne da ihu. To wallahi bara ki ji badan badan ba da tuni na karasa dake har lahira."
Jan hannunta ya yi zuwa gurin da aka kebance don ita kawai ya jefar tare da barin gurin.

GIDA!

Iyayenta ne zaune abin duniya duk ta yi musu yawa babu inda suke dafawa su ji sanyi, mahaifiyarta ta dubi Abbanta ta ce.

"Malam anzu haka zamu zuba ido ana cutar damu itama fa ďiya ce kamar kowa kuma ni shaida ce yarinyar nan bazata aikata ba wallahi, zan iya rantsewa da Al'Qur'Ani ba za ta aikata ba.
Malam ya yi shuru bai ce komai, ganin yaki amsa mata ne ta fusata ta ce.

"Haba Malam ya ina magana ka yi shuru ko dai kaima zuciyarka ta yarda kan cewa 'yarmu zata iya kashe mutum ne.?"
Sauke gwauror numfashi ya yi kana ya ce.

"Hajiya ba za ki gane yadda nake jin zafi da kuna cikin zuciyata ba, ina jin zafin wannan abin daya faru wallahi duk wani hanya dana san zai bille mana duk sun toshe babu yadda zan yi ne shi yasa kika ganni haka."
Da raunanniyar murya ya karashe maganar.

"To shi kenan haka zamu zuba musu ido suna mana cin kashin da suke don kawai suna takama da mulki? Bamu da komai amma muna da Allah kuma shine zai fidda mana da ita daga cikin wannan sarkakiyar. Dole na koma bakin aiki domin kubutar da 'yata, ko ni kadai tare da karfin Allah zan fito da ita kuma karka manta ni yar malamai ce na dau alwashin ni ce zan fiddata daga mummunar dauri. Sannan daga ukubar da take ciki da taimakon Allah, mu ma mata muna da rawar takawa ni zan zame mata katanga abin jinginar ta ni kadai kawai ka tayani da addu'a domin Allah baya goyon bayan zalunci da azzalumai In Shaa Allah zamuyi nasara amma kafin mukai ga nasarar ne zamusha wuya ni dai goyon bayanka nake nema."
Zuba idanu kawai ya yi yana kallonta har ta kai aya sa'annan ya ce.

"Allah ya shige mana gaba kuma ya bamu sa'a akansu Allah yayi gaggawan bayyana mana bakin zaren amma bamu da karfin faďa da mutanen nan ki tuna da wannan."

"To Malam so kake mu zuba musu ido suna azabtar mana da yarinya ita kadai gare mu, bamu da waninta don haka ba zan yarda ba dole na kwatota ko da karfin ko kuma da karfin addu'a tare da karfin bakina don ba zan yarda da zalinci ba."
Cikin kuka take magana. Janyota ya yi jikinsa hade da rarrashinta ya ce.

"Hajiya ki yi hakuri mun rike Allah kuma ALLAH shine zai mana maganin su, don haka ki daina tashin hankalinki akan abinda muke ganin za mu iya maganinta kinji.?"
Agogon hannunsa ya kalla sannan ya ce.

"Bari na tashi na je gurinta saboda akwai wani mara imani bashi da tausayi wallahi kullum sai ta min kuka da shi har ban san abin yi ba."
Dago kanta ta yi da sauri tana kallonsa hawaye na cigaba da surnanowa daga idanunta amma ba ta ce komai.....

Yanzu aka fara tafiyar ina fatan zaku ji dad'in editing da kuma kari da sauyin labarin. Domin samun cikakken labarin ku biyoni a Wattpad handle dina @Basira_Nadabo. Na gode

Follow Me On Watpad @Basira_Nadabo.

BANI BACE Where stories live. Discover now