chapter 42

2K 93 30
                                    

"Innalillahi baka sake ta ba ka ce fa ɗan nan?" Zameer ya girgiza kai idanunsa cike da hawaye ya ce "Da gaske nake Baffa ni ban saki matata ba, guduwa kawai ta yi ta bar ni babu inda ban nemeta ba har gidan rediyo" ba iya Baffa ba hatta Junaid da yake zaune maganar Zameer ta jijjiga shi.

"Kenan Ridayya aure ta yi akan aure?" Baffa ya miƙe tsaye ya shiga zirga-zirga a tsakiyar parlorn can ya juya ya ce

"Na kasa yin tunanin komai akan wannan al'amarin,abu kamar a wasan kwaikwayo da labaran hausa na tatsuniya?"

"Alhaji Mansur zo ka zauna" Baba ƙarami ya kira sunan Baffa yana nuna masa wajan zama domin ya lura gabaɗaya hankalinsa a tashe yake tsoro da firgici sun shige shi sosai ainun da gaske.

Junaid ya kalli Zameer yadda yake ta share hawaye tunda yake ko ada can baya bai taɓa ganin ladabi da tsantsar tsoro a fuskar Zameer ɗin ba sai yau bai kuma taɓa ganin hawaye akan fuskarsa ba, rashin yadda ya gitta a zuciyar Junaid ya ce

"Idan baka saki Ridayya ba, to akwai wani abu a ƙasa tunda da can bata taɓa yunƙurin fitowa daga gidanta ba, ta dawo gida a saboda ka saɓa mata ba, balle a yanzu da take tunanin bata da kowa tunda Ridayya ta dawo ne kafin ta san cewa muna raye. Me ka yi mata? Me kaiwa Ridayya da har ta baro inda kake ta gudu? Me ya sa baka biyo bayanta ba sai yanzu?"
Da wani kalar shock Zameer ke kallon Junaid da kuma sauraren shi, ganin yadda zai rutsa shi ya saka ƙaryar shi ƙarewa Zameer ya ce
"Yaa Junaid ai kasan ba zan yi ƙarya ba, go and ask her ta san komai she knows everything wallahi tallahi"

"Da mamaki wannan lamarin, ba a rabu da Bukar ba an haifi Babu, wacce irin ƙaddarar ke bibiyar rayuwar Ridayya" Cikin fusata Junaid ya ce "Karku yadda da shi, domin tun farko shi ɗin ba abin yadda bane ina da tabbacin Ridayya bata taɓa cutar da kai ba, balle ta aikata wannan babban lamarin"

"Ya isa Junaid please"

Zameer ya sake sauke kansa ƙasa cike da ladabi kamar zai yi sujjada muryarsa a raunace ya ce "Ita ta ce na taɓa cutar da ita? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Lallai a bar mace da kaidinta amma ni ba zan ce komai ba, idan kana ganin ta dinga yawo da aurena a kanta shi ne daidai to babu damuwa I'll let her be tunda kana ɗaurewa ƙanwar gindi"

Junaid ya kalli Zameer cike da ɓacin rai yana tuna abubuwan da suka shiga tsakaninsa da Yaa Bilal musamman a cikin asibiti a kan Zameer Ridayya ta yi wa Ustaz Allah ya isa kuma ta kira shi da sunan da ko a family shakkar kiransa ake da shi. Idan Junaid ya tuna ranar sai ya ƙara jinjinawa Ustaz na irin so da ƙaunar da ya kewa Ridayya.

Baba ƙarami ya yi murmushi irin na manya mutum mai tunani da girmama zumuncin Allah da bawa kowa haƙƙinsa ya ce "Ɗana Zameer kana ina Ridayya ta gudu garin yaya hakan ta kasance ka yi wannan sakacin?"

"Abba muna nan Garin Kano ba sakaci na yi ba cikin dare ta gudu wai ta gaji da zama dani saboda kuskuren dana tafka a rayuwa, na mata laifi ni ɗin mai kaifi ne Abba amma girman laifin bai ka ga Ridayya ta gudun daga cikin gidanta na sunna ba kuma tare ɗana. Abba kai mai fahimta nasan zaka fahimce ni"

Zameer sam bai kula da Tajj daya shigo ya zauna ba, yana sanye da black suit irin ta manyan ƴan sanda sai baza ƙamshi yake idanun Tajjudeen Baita zube akan Zameer shi ma yana sauraren shi. Tajj zai magana da hannu Baffa ya yi masa alama da ya yi shiru.

"Karka wani damu ɗana ka ɗauka ni ɗin tamkar uba mahaifine a gare ka zan saurareka kamar yadda zan saurari ɗan dana haifa kuma na maka alƙawarin wallahi wallahi wallahi uku kenan idan har kai ne da gaskiya to zan dawo maka da Ridayya cikin gidanka da yaronka matsayin matarka"

Da sauri Baffa da Junaid da Tajj suka kalli Baba ƙarami da yake ta murmushi, firit Umma t fito daga laɓewar da ta yi ta ce "Kai Allahamdulillahi idan hakan ta faru zan fi kowa murna da samun nutsuwa a zuciya, Babban mutum ya rabu da kwallon mangoro ya huta da ƙuda har abada. Na daɗe ban ji tsanar da na yi wa mutum irin ta matsiyaciyar ƴar nan Ridayya ba, ba zan taɓa ganin farinta ba wallahi mummunan mai baƙar zuciya mai kama da Alade kawai"

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now