page 15

450 37 6
                                    

"Biba sake riƙe mini tsinanniya gayyar na ayya gayyar assha, wato ba a rabu da Bukar ba an haifi Habu ko? Yadda uwarki ke son kwace mini miji, haka kike so wargatsa mini plan na yi biyu babu,uku ba ko ɗaya? Ki zame mini ƙarfen ƙafa mai wuyar fidda wa?" Ammi ta faɗa tana sake ɗora wuƙar a saman wutar gas ɗin. Biba dake riƙe da Ridayya, kamar wacce ta riƙe sa'arta sai haki take saboda wahala ta ce
"Ina ganin ki rabu da ita haka, she's to young da wannan azabar taki Maryam, matsalarki da uwarta daban, matsalarki da yarinyar daban, look at her? Shekara shida amma kamar ƴar shekara huɗu duk ta tsamure kodan rangwamen hankalinta kya saurara mata please"

"Na saurara mata? Kin san me kike cewa Biba, kin san baƙin ciki da takaicin dana ɗanɗana dalilin uwar yarinyar? Kin san halin dana shiga sanadin Fatima? Ai wallahi ko zan ƙarar da komai nawa ba zan saurara ba sai na kai ga gaci, this is my promise" Biba ta girgiza kai domin haka kawai tausayin Ridayya ya kamata, ita kanta ta tsani kishiya ko a mafarki bata fatan ace yau gata da kishiya balle a zahiri? Kuma burinta ta rayu daga ita sai ranta banda ƴaƴan kishiya. Ta kalli Ridayya da wani irin yawu mai kauri ke dalala daga cikin bakin nata,bata zaro harshenta da ya yi jajur yana tsastsafo da jini, fatar wajan ta ciro, idanun yarinyar kamar zai faɗo ƙasa saboda masifar azabar dake ratsa mata jiki, tana kaiwa gurɓatacciyar kwakwalwarta ziyara tare da game dukkan wani sassa na jikinta da suke motsa ji da gani.

"Ba kyau azaba da wuta, Ubangiji kawai ke da ikon haka, kurman da ita kike son yi ne?". "Ta kurman ce mana Fatima ke da asara bani Maryam ƴar Alhji Shitu ba"

"Malam Shitu dai, don bani da labarin Malam ya je makka, ke fa matsalar dake damunki hadda talaucin daya yi miki katutu a gindi" Ammi bata kula Biba don taga alama tunan silili take ƙoƙarin yi mata. Ta cafko harshen Ridayya tana ƙoƙarin manna mata wuƙar suka ji an ce.

"Ammi, Ammi me kike ƙoƙarin yi haka" Ta yi saurin cillar da wuƙar tana haɗe rai kafin ta ɗauki Ridayya idanunta zube a kan Junaid ta ce "Daga ɗora girki fa na nemeta na rasa, sai ihun ta na ji a kitchen, kasan ta da kwaɗayin nama kamar jikar mafarauta shi ne ta kifo da tukunyar ta ƙona kan ta" Junaid ya kalli kitchen ɗin, kana ya kalli Ridayya dake miƙo masa hannu tana sauke ajjiyar zuciya idanunta ya ƙafe sun ƙara girma, harshen data zaro yake kallo da sauri ya matsa yana kallon wajan ya ce "Me kuma ya sameta a baki?". "Ƙonar da nake faɗa maka ce ai"
"Bai yi kama da wacce ta ƙone ba, sai dai ƙona ta a kai, kalli shatin wani abu fa?" Ammi ta kalli Junaid gabanta na faɗuwa sosai ta ce "Me kake nufi? Ni zan ƙona ta ko kuma Biba data taimaka mini na ɗauke ta? Yarinyar daba hankali gare ta shi ya sa na ce babu mai saka ta a makaranta yanzu, ni zaka ɗora wa alhakin hakan Junaid?"

Ya girgiza kai murya a ƙasa ya ce "Ki yi haƙuri Ammi, bana nufin haka" Yana faɗa ya fice, ta leƙa ganin ya fi ta ta dungurar da Ridayya a wajan tare da yin part ɗinta, Biba ta bi bayanta a ranta tana jinjina abubuwan da suke mata yawo a kan ta.

Suna fita Ridayya ta miƙe tana yarfe hannunta, tare da fito da harshen waje domin samun sauƙin abinda take ji, da zarar iska ta kaɗa sai ta ji kamar yanzu ne Ammi ke manna mata wuƙar, majina, yawu suka haɗe mata sai kuma a lokacin ne ta fara neman hanyar gudu inda bata taɓa yi ba a gidan ta nufa, rashin ƙwari da ƙarfin jikin da bata da shi suke neman yasar da tsamurarren jikin nata. A jikin bishir zugale ta raɓe hawaye na bin idanunta sai nishi take da haki tana son yin kuka a fili ta kasa.

Shigowar shi kenan cikin gidan, tunda ya shigo ya samu kansa da faɗuwar gaba mara dalili. Ya yi jim a daidai mararrabar data haɗa shashin biyun, na Baba ƙarami dana Baffa. Yana ƙoƙarin nufar part ɗinsu ya ji saukar siririn muryarta a cikin kunensa.

"A...aaa.. Abbiey, Abbiey"
Furucin ya yi fitar gurbi daga cikin bakinta, ba tare data san waye a wajan ba, azaba ta saka babu sunan wanda ya zo bakinta da tunaninta sai na Abbiey.
Ustaz ya juyo da sauri har hiramin kansa na faɗuwa, idanunsa da suke kodayaushe a rufe ya sauka a kan Ridayya, ya zuba mata ido ganin sai murza harshe take.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now