Chapter 38

2.2K 102 32
                                    

“Yau nake ganin ɓatan nono a ƙirjin budurwa? Wai da gaske babban mutum ya saki Ridayya? Ku karanta mana takardar a fili mana" caraf Ammi ta karɓe zancen da faɗin "Wallahi Hajiya kema kya faɗa, su kawo takardar na karanta a fili kowa ya ji, ai saki ba kan Ridayya farau ba, ba kuma za a ƙare a kanta ba. Allah ya ƙaddara ita ɗin matar Burhan ce"

"Burhan kuma?"

Junaid ya furta da mamaki kwance a fuskarsa ita nata allon sai ya haska mata Burhan matsayin mijin Ridayya? Ai kowa da ƙaddara sam ba ta yi wa Ridha adalci ba, duk lalacewarta ta fi ƙarfin mashayi.

Ammi ta zarewa Junaid Idanu ta ce "To uwar mece da Burhan ɗin har kake maimaita sunansa, ai daman ya jima yana son ta, kawai babu yadda zai yi ne ni ce nake tanƙwara shi"

Kowa kallon Ammi yake banda Baffa da Mami, wacce ta yi kamar ruwa ya cinye ta wani irin zafi zuciyarta ke yi mata yaushe ne Ridayya za ta yi farinciki? Yaushe ne damuwarta za ta zo ƙarshe? Mene laifinta? Wani abu ya tukare maƙoshinta nan da nan abinda ke kwance a mararta ya motsa tare da tabbatar da lafiyarsa ras.

Baffa ya sauke numfashi bayan kammala karanta abin da takardar ta ƙunsa ya yi shiru domin bashi da wani abin cewa tsananin kunyar abinda ke zane a takardar shi ya addabi ransa ya kuma jin daɗin kalaman Ustaz har ransa, tantama da mamaki suka mamaye zuciyarsa at the same time kuna ya hasko irin zuri'ar da Ridayya da Ustaz za su samawa Rano families. Ya ɗaga kansa yana kallon Hajiya ya ce "To daman ba wani abu bane face.....,'

Baba ƙarami ya yi saurin tarar numfashin Baffa yana me riƙe hannunsa ya ce

"Saki ne kamar yadda kowa ya ji sai fatan Allah ya daidai tsakani. Aure daman rai gare shi na wasu ya ɗore na wasu akasin hakan ƙaddara kuma yaɗo take idan an san farko babu wanda ya san ƙarshen ta, wata ƙarshen ya zo me kyau wata ba yadda muka yi tsammani ba, idan akwai rabo tsakanin Muhammmmd da Ridayya babu shakka wanda ke da tawaye da auren rabo zai yi ajalinsa kowa ya sassauta buri" saurin yin shiru ya yi jin Umma ta rangaɗa uwar buɗa da faɗin.

"Ayy yiri-yiriri. Na gode Allah na kuma ji daɗin wannan rana don murna kamar na zuba ruwa a ƙasa na sha haka nake ji, ina roƙan Allah ya ɗorawa muguwar ƴarku son ɗana wanda zai kwantar da ita har gadon asibiti ta ji irin abinda ya ji, kuma tsakaninta da shi sai kallo daga nesa Mardiyya ita ce matarsa ta nan gidan duniya da kuma lahira, na tsaneta bana ko ƙaunar buɗe idanu na ganta ina fata idan rabon ya tashi kisa ya kasheta ita" ta sake sakin dariya.

"Ahhayeee cas raina fari tas idan ma mata biyu yake so ni zan nema masa wata in sha Allah ko a cikin yaran ƴan'uwana ne na Zamfara, kuma Muhammmmd dole ya dawo gida ya kuma bi umarnin uwarsa"

"To bari mu gani umarni uwa zai bi ko na mata? Ko kuma soyayya" Abba ya faɗa a fili ta ce "Me ka ce?"

"Cewa na yi ki saurin nema masa matar auren nima zan fi son hakan, kuma ki dinga sara kina duban gatari ki buɗe kunne da idanun zuciyarki kuma ki tuna cewa ɗanki nakasashe ne banga lafiyayyiyar yarinyar da zata zauna da shi baya amfana mata da komai ba, musamman yaran zamani da idanunsu yake a buɗe. Babban dalili babu iyayen da za su amince su bawa Muhammmmd auren ƴarsu bayan sun san ba zai taɓa haihuwa ba. Itama Mardiyya zan nemi makusanta na labarta musu komai"

Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye tare da barin parlourn ransa babu daɗi, ana zaton wuta a maƙera sai gata a masaƙa bai yi zaton Hajiya Hadiza zata kawo masa tsaiko ba. Mami ma miƙewa ta yi ta nufi part ɗinta zuciyarta tuni ta raunata ainun.

Hajiya ta ce "Allah shi daidaita al'amarin nan duk auren da ake tsiya haka fa ya fi tsayin rai, mutane suyi ta ƙoƙarin kashe aure kamar sune suka halacce shi, Ubangiji ya kawo musu da sauƙi"

"Amin" Anty Zuhura ta ce Ammi ta watsa mata muguwar harara tana ƙwafa.

Baffa ya miƙe Ammi ta yi saurin cewa "Baffa idan ba damuwa ina son magana da kai" ya dube ta can ya ce "Ina ji"

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now