Page 24

974 55 21
                                    

Mirgina wa ya yi gefe jikinsa na rawa yana ƙoƙarin kurma ihu ya ce "Akan hakƙina za ki nakasa ni? Ki cuce ni ki cuci kan ki?"

Gabaɗaya muryar Zameer rawa take ganin yadda har yanzu take riƙe da fatanyar idanunta sun yi jajur jikinta na wani irin ɓari kamar mai shirin tayar da aljanu. Ya dake ya ce

"Ki bi a hankali, ni mijinki ne kuma zan ci gaba amsa sunan hakan har gaban abada, idan kina tunanin wani abu saɓanin nawa kin yi kuskure"

Ridayya da ƙyar take riƙe kanta, ji take kamar za a wurgar da ita ne, duk da gabanta dake faɗuwa da kuma girman igiyar auren dake kanta bai hana ta nutsa idanunta cikin nasa ba ta ce

"Giɗaɗo"

"Giɗaɗo kuma? Ina kika ji sunan nan? Mene haɗina da Giɗaɗo?" Har lokacin yana damƙe da jikinsa da Ridayya bata samu damar idda nufinta akan shi ba sai gefen ƙafarsa data makawa.

Jikinta duka rawa yake gani take tamkar babban zunufi zata aikata faɗawa miji magana, mijin da a yanzu komai da take ji game da shi yake yayewa. Da ƙyar tana riƙe jikinta ta ce

"Giɗaɗo ba shi ne sunanka ba? Giɗaɗon ƙauyen nahutun batsari ko?" Ta girgiza kai ta ce

"Daga Almajiranci ka dawo Zameer?" Ta zube a kan ƙafafuwanta zuriyarta na yi mata wani irin zafi da tafasa ta haɗe hannayenta biyu ta ce

"Yau ɗaya ka faɗa mini laifina a gareka don Allah, soyayyar dana nuna maka? Zaɓarka da na yi na watsar Abbieyna? Ko fara furta maka kalmar Ina son ka? Ko kuma budurcina daka amsa kafin aure shi ne laifina? Ko kayan ɗakina daka kwashe ka siyar shi ne nawa laifin? Ciyar da kai da nake yi kullum, ko kuma fifitaka a kan iyayena shi ne laifina? Ka faɗa mini laifina dana cancanci irin wannan cin mutumcin wulaƙanci da ƙasƙanci a gidanka, me na aikata har haka daya dace ka zame mini MUNAFIKIN MIJI? ka faɗa mini mana"

Miƙewa ya yi ta yi saurin miƙewa dukda rashin ƙarfin jikinta ga ciki. Zameer bai bari kalaman Ridayya sun yi tasiri a zuciyarsa ba ya yi murmushi ya ce

"Wane ya faɗa miki haka? Wanne munafukin ne har haka Ridha tsakanina dake za a shiga?" Kallonsa kawai take da juyayyun idanunta ba tare da ta ce komai ba.

"Ridayya kar ki bari zuciyarki ta yaudare ki, ba ki da wani waje da yafi wajena, ba ki da wanda ya fini a yanzu dole ki yi mini biyayya domin Batsari kike ba Kano ba"

Ya nufi inda take domin baya jin zai iya rabuwa da ita, abubuwan da yake ji game da ita ƙara fusgarsa suke, a gare ta ɗinne kawai yake jin haka dukda wani irin tsoro da yake shirin ruskar shi a yanzu. Ya gyara tsaiwa ya ce

"Ni tamkar ƙadangaren bakin tulo ne, a gare ni a ɓata ruwa, a bar ni a ɓata ruwa, ni ɗin dai ya zame miki dole. Na tuna miki da babban murya iyayenki sun rasu baki da kowa a duniyar nan sai ni, kuma ki hanani abinda nake so ki gane Allah ɗaya ne"

Kallonsa kawai take duk yadda hawaye ke ƙoƙarin fita daga cikin idanunta ta kasa saboda kada ya gane a yanzu iyayenta sune rauninta da rashin gatan da take da shi. Hannu ya saka ya fusgota kamar yadda ya zama yi mata wanda hakan ya zama tamkar Sexual violence a gare ta ko shi mijinta ne idan ba da ra'ayinta bane to tamkar zalinci ne, CUTARWA ne.

Kokawa suka shiga yi duk ya gigice da tsananin buƙatar ta ita kuma ta yi alƙawarin har gaba da abada idan akwai ba zai ƙara morar jikinta ba. Ta zage iya ƙarfinta ta gantsara masa cizon daya kusan kwashe masa fatar wuya ya saketa ta yi saurin fitowa daga ɗakin tana nufar  ɗaya ɗakin da yake da wata mata a ciki.

Wani baƙin ciki ya tukare a wuyan Zameer ganin yadda ya ga samu kuma ya ga rashi amma ko zata mutu sai ya fanshe duka sauran ranakun daya biyo ta bashi. Ya yi tsaki ya fita.

Kuka take tamkar ranta zai fita numfashinta na tsarƙewa saboda yadda zuciyarta ke mata zafi da raɗaɗi, idan ta tuna bata da kowa bata da wanda zata raɓa balle ya ƙwatar mata ƴanci sai ta ji komai ya sare mata ta ji tamkar ta yi giving up ko ta ji kamar ta kashe kanta. Rana zafi inuwa ƙona, ruwan daya dake ka shi ne ruwa ta yarda rayuwa da ƙaddarata a tare Ubangiji ya samar da su kuma sun zama jinin jikinta yadda ba zata taɓa iya guje musu ba.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now