Page 32

1.3K 85 26
                                    

Ustaz ya girgiza kai ya kama hannunta suka zauna bakin gado, har lokacin kuka take ta ɗora kanta a ƙafarsa tare da zamewa zuwa kasan carpet, sosai take kukan ta riƙe ƙafafuwansa gani take kamar zai gudu ya sake barinta rashin gatan ya tabbata a gare ta.

Sai da ta yi mai isarta ta fara sauke ajjiyar zuciya nan da nan kanta ya fara ciwo ta ɗaga kai ta kalli Ustaz shi ma ita yake kawai yake kallo.

"Kin gama?"

"E, ina jin kamar na yi ta kuka" ya miƙe tsaye ya nufi wajan fridge ruwa mai sanyi ya ɗakko ya ɓalle murfin gorar ya dawo ya miƙa mata yana mai sake zama inda ya tashi.

Ta tsare shi da idanu dukda gefen fuskarsa kawai take kallo. Ruwan ta sha sosai kana ta ajjiye tana sauke ajjiyar zuciya mai nauyi.

"Ki kwanta, bacci ko za ki ji daidai"

Ta girgiza kai tana ƙoƙarin sake ɗora kanta a ƙafarsa ya zame yana kame fuska ya san tuni ta saba, ko bacci wani lokacin a kan ƙafafuwansa take yi, ta ɗauke shi uba, aboki, uwa, amini bata shakkar faɗa masa komai da zama a duk yadda ta so idan yana wajan.

"Abbiey magana zan yi maka"

"Ki kwanta"

"Ko na kwanta ba zan iya bacci ba, ka bari na faɗa maka ka ji" ta ƙare maganar tana marairaice fuska ta ɗan tura bakinta gaba. Jinjina mata kai ya yi ta sauke kan ta a ƙasa

"Abbiey don Allah yau ɗaya ka faɗa mini me ya sa Baffa da Mami basa so na? Me ya sa Mami take son Zainura ni bata so na, me ya sa Baffa yake son kowa ni ban dani ba, me ya sa nake amfani da sunanka a makaranta maimakon na Baffa? Me ya sa kuma kowa na gidanmu fari ne ni kuma baƙa mummuna? Me ya sa ko a makaranta kowa ke guduna? Me ya sa mutane suke cewa ba zan taɓa samun mijin aure ba saboda ni mummuna ce ina da manyan idanu, da babban leɓe kuma ina da jiki da gashi me ya sa fatata take maiƙo kamar an shafa mai? Me ya sa kowa baya sona kowa yake guduna kai kuma kake so na Abbiey?"

Ustaz ya yi shiru ta ce "Ka faɗa mini mana kamar na so na gane"

"Ustaza ba za ki gane bane, ki na ta harbo tambayoyi"

Ya miƙe ya nufi gaban madubin ɗakin da hannu ya nuna mata ta zo, tana zuwa ta yi ƙoƙarin jingina da jikinsa ya yi saurin zamewa kan hakan ya faru ya yi baya ya nuna ta tsaya gaban madubin a hankali ya saka hannu ya yaye, gabaɗaya suka fito a cikin madubin tana gaba yana baya da ta zara

"Bani za ki kalla ba, dubi kan ki sosai"

Ta ƙura wa kanta Idanu da baƙi da gaske ita ɗin asalin baƙar fata ce, asalin Bahaushiya ƴar'hausawa cikakkiya kuma. Idanunta farare tas sai dugwayen gashin Idanu har kwanciya suke, girarta a haɗe suke shaida yalwar gashi gaban goshinta ma haka, lips ɗinta su ba jaa ba kuma ba pink ba sun yi wani colour yirrr da su ɗaya ƙarami ɗaya mai ɗan faɗi ya bada wani shap tana da Oval face kawai tsananin baƙi da duhun fatarta ya saka ake ganin muninta.

Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Na gani ni dai ban gane ba"

"Ki gode Allah ki gode Annabi irin ku, ku ne ya yi yin zamani. Farin mutum har abada ba zai iya komawa kalar fatarki ba, ke kuma kina iya komawa fara idan ba ki gode Allah da irin zubin halittar da ya yi miki ba...," Ya sauke numfashi yana ɗan hutawa.

"Idan kowa baya son ki ai ni ina son ki ko?" Ta yi shiru ya ce "Idan Allah da kansa daya halicce ki ya samar dake a duniya yana son ki kuma ya amince da ke to babu damuwa kowa ma yaƙi ki, mutanen ƙwarai Ubangiji yafi jarraba imaninsu Ustaza ki kasance mai haƙuri da gode Allah da ni'imar da ya yi miki. Mutane da yawa sun lalace da yi wa mutum ba'a na daga halittar da Ubangiji ya yi masa, amma tunda kike kin taɓa ganin mutum ya yi halitta?"

Ta girgiza kai ya kalleta ta madubin ta yi saurin cewa "A'a"

"To bai kamata ki yi fushi ba, yin hakan kamar kina nuna rainuwa ga Allah da nuna masa bai iya halitta ba, ki saka a ranki ke mutum ce kamar kowa mai tarin marudai wanda kike shirin cimma, ki yi ƙoƙarin bawa masu faɗar hakan kunya, ki zama mai kwantarwa kan ki ƴanci a ko'ina kar ki bari a wulaƙantaki kuma kar ki wulaƙanta kowa, Allah da kansa ya ce wáakaramna bânii adama"

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now