Page 14

431 23 5
                                    

Fitowarsa kenan daga shashinsu domin yin shur na azumin Alhamis, tunda ya fito yake jin zuciyarsa babu daɗi, ya yi shiru yana jin yadda iskar gari ke kaɗawa tana bada wata amintacciyar ni'ima mai saukar da nutsuwa a zuciya. Saukar kukan jaririyar ya yi daidai da lokacin da ya ji kansa ya sara, ya yi jim yana son tabbatarwa da kansa  abinda kunensa ke jiyo masa. Da sauri ya miƙe tsaye carbin hannunsa na ƙoƙarin faɗuwa zuwa ƙasa, gashi farar jallabiyya ce tas a jikinsa.

Direction na inda kukan ke fitowa yake bi, a haka har ya isa daidai inda bolar gidan take ya waiwaya a hankali, amma bai ga kowa ba zatonsa ya bashi yau ko rashin sa'a ya yi mutanen ɓoye ke son buɗe masa ido? Ya ci-gaba da tasbihi a zuciyarsa. A bin mamaki kuma lokacin jaririyar ta daina kuka, yana ƙoƙarin juyawa ya sake jin saukar kukan nata wanda yake shirin rusa nutsuwar daya gino a kanta, cikin sauri ya fiddo wayarsa ya kunna torchlight tare da haskawa. Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!

A gigice ya saki wayarsa dukda ƙasan zuciyarsa bai gama tabbatar masa daba gamo ya yi ba, ya saka hannu a fili kuma cikin kamilalliyar muryarsa ya ke azakar na neman tsari da kariyar Ubangiji. Da duka hannu biyun ya ɗauki jaririyar yana matsawa wajan haske, ya runtse idanunsa da sauri lokacin da ya yi tozali da Ridayya, fatar jikinta ta kumbura jini sai zuba yake tako'ina a jikinta, da sassarfa ya nufi ɓangarensa ya shiga bedroom ya rasa abinda zai yi duka wannan abubuwan bai san su ba, sai jaririyar ya gama sha'aninsa a gidan bai kalle shi ba, balle ya san yadda ake kula da su.

Ruwan shower ya kunna yana ƙoƙarin zuba mata sai kuma ya girgiza kansa ya koma ya kunna hiter kafin ruwan ya yi zafi ya nufi saman gado, ya ɗora Ridayya a ciyarsa. a hankali yake bin fatar jikinta da kallo, dukda kasancewarta jaririya amma sam bata da hasken fata gashi da cinnakun da fatar suna neman zama ɗaya ga jinin dake fita duk ya dagule fatarta.
Audiga ya ɗakko ya dinga share jinin yana marmasar da cinnakun amma tamkar na asiri sun kafe gashi sai tsala ihun azaba Ridayya ke yi. Ustaz ya inda zai saka kansa idan ya tsora mata idanu sai kawai ya sauke ajjiyar zuciya, da ace shi ma'abocin kuka ne da karaya da lamarin rayuwa da tuni ya raunata. Ya ci-gaba da gogewa har jinin ya fita a hankali ya dinga kaɗe cinnakun wasu su fita wasu kuma suna nan. Ya ajjiyeta sai kuma ya dawo ya ɗauketa gani yake tamkar wani abu ne zai sameta idan ya bar ta. Ruwan zafin ya haɗa daidai wa daida, ya saka detol a ciki.

Zabura Ridayya ta yi sanda ruwan ya ratsa ta, ga sabuwar fata ga ciwo ga zafin ruwan wanda Ustaz ya kasa fahimta ya ɗauka duk ciwonne ya sata kuka, ya dinga wanke mata jiki a hankali kamar ƙwai ya gama ya sake haɗa wani ruwan ya mayar da ita har fatar ta ɗan washe cinnakun suka fita a towel ɗinsa ya naɗe ta, tare da fitowa.

Farar jallabiyyar Ustaz ta ɓaci da jini ya ajjiye Ridayya saman gado zai juya ta canyara ihu ya yi saurin dawowa ya ɗauketa ya sata a kafaɗa. Fatar wuyansa ta fara tsotsa kamar ta samu nono.
Murmushi ya saki mai taushi jin yadda take ƙoƙarin neman abinci ido biyu, sakkota ya yi  sai ta fara motsi da nishin kuka ya saka mata yatsarsa a hannu da sauri ta fara tsotsa tana sauke ajjiyar zuciya.  Ustaz ya lumshe idanunsa wani irin tausayi ya kama shi, bai taɓa ganin wannan rashin imanin ba ko a fina-finai Hausa da littafan Hausa ta marubuta suke yi. Ruwan zam-zam ɗin daya jiƙa tare dabinon ajwa ya ɗakko ya yi kauri sosai ya bata ta dinga sha, sai ta sha sosai kana ya cire. Jin ta yi shiru ya miƙe ya watsa ruwa a jikinsa ya sauya kaya daga jallabiyya zuwa three qauter Ustaz baya son kaya masu nauyi shi ya sa ba kowa ke shigowa bedroom ɗinsa ba, idan har shi kaɗai ne za ka iya samun shi daga shi sai trouser.

Sai a lokacin ya samu damar ƙare wa yarinyar kallo, idanunta rufe har yanzu babu wanda zai ce ya taɓa ganin su. Idan ka ce real definition of blac skin kai tsaye Ridayya ce, baƙin mai duhu sai da yana haske za kaga har ɗaukan idanu yake, yanayin shi bama mai irin maiƙo ɗin nan bane ya fi kama da baƙi irin na ƴan Ethiopia. Laɓɓanta jajur suke duk da suna da girma da kauri amma kamar a tsaga jini ya fita, gashin gira a cunkushe suna neman haɗe wa waje guda, ga gashin ido zara-zara sumarta har ta shige goshi ko'ina na jikin Ridayya suma ne.

MUNAFUKIN MIJIWhere stories live. Discover now